KUSKURE Complete Hausa Novel

Amarya Aishatu akayi gidan Inna d ita nawara ma haka akayi gidan mama d ita Dan su shirya a kaisu gidan mazajen su …
Bayan wasu daga gidan inna sun karama Aishatu fada aka mokaya gidan su nawara mama da Alhj su nawara y sake musu nashiha d nuna musu mahimmanci bin miji ,sunata kuka d kyar aka rabasu amaren biyu akasa kowace a mota Dan kaita gidan ta …
Da anso Aishatu t raka nawara gidan ta sakamakon lokaci d y kure ,yasa aka Kai kowace gidan ta kawai daga baya sa kaima juna ziyara….
Hassana , ussaina,aunty sufayya ,sune Yan d’aukan Amarya d wasu makotan gidan Ammy d se yanzu suka karaso Dan basuje dinner ba ,aunty zainab d su aunty Mai d’inki d maman nawara sunma Aishatu Kara har dasu aka tafi kaita gidan ta …..
Wasu yayun ,mama d ‘yan uwan Abban nawara ,da Inna d hidaya kawar nawara d Aishatu suka yima nawara Kara suka tafi Kai nawara gidan ta …..
Huzna fa zuciyar ta kamar ta fito Dan matsanaicin bacin Rai safwan yayi Aure Amman b lbr d kuturun wulakanci , gashi gari yaki wayewa Dan ta samu taje taga uwar d y aura ….
Ganin ba sauk’i Abun t on din datan ta dama tana following safwan true Instagram d wasu friends dinsa taga shi be hasko Amaryar tashi ba ,Amman taga hanzeee abokin SA y hasko safwan d Amaryar Sa ….
Ruwan huzna ne hau ,ganin Ango safwan d wata zukekiyar Amarya yarinya Mai bala’en kwarjini d kyau tadau make up na garari tayi badakama Dan koni Saida nayi tmby kafin na gane *indoo* ta canza ta koma Aishatu kawai ….
Ta Jima Tana ganin hoton tun hoton baya Bata Mata Rai Dan da kalon kurila takema hotunan Dan gano ko Wacece ko ta Santa ko ta taba ganin ta ,ganin Bata Gane taba kawai yasa hoton y Fara Bata haushi …
Can Kuma ta Lula duniyar ‘yan gulma ,tanaso tasan uban me ya raba safwan d NAWAL?
Tasan inta tmby hassana ko ussaina bazasu Gaya Mata yadda akayi ba NAWAL din ko in ta tmby ta watakila ta huce akanta Dan tasan yadda takeson safwan dinan yanzu cikin kowane d ita duk Wanda y takota sai ta haife shi…
Ina mafita? Indo banzar Mai Aikin su ita zan tmby kawai ,naji dalilin rabuwar safwan d NAWAL d Kuma sanin matar d y aura Yar uban waye d matakin karatun ta d matsayin ta ,Dan yadda Indo take tsorona d na zare Mata ido zata fede min biri har wutsiya ….
*Ankai nawara gidan ta ,d kyar hidaya suka rabu d nawara ,sunata missing juna ,suka barota suka dawo gida ,Dan hidayan a gidan Inna zata kwana Dan ta debema Inna kewar Aishatu ta ….
Aishatu ma gidan Ammy aka wuce da ita ,aka Mata nasiha aka wuce d ita gidan ta gidan NAWAL nada …
Bayan mutane sunsa Albarka sunata yaba tsarin gidan d su mama suka Kara Mata nasiha suka barota ,taga Alamar ita kad’ai za’a Bari Aiko ta biyo su da kuka Mai ratsa zuciya …
Da kyar mama ta rarashe ta takoma t zauna ,Amman ji take ita d batayi aunren Nan ba ayau ,Karo n farko d ta sani Auren y tsani kanta d ta Amince har ta dinga murmushi dazu ta manta da inda za’a kawo ta ,hassana d ussaina ne d aunty sufayya suka Dan jira kafin zuwan su safwan d abokanen sa d Yaya d ze d’auki suffaya…
Aishatu Amarya nata kuka hassana n Bata hak’uri har ango y karaso tare d taimakon su Hamza d Hafiz ,suka shishigo d ledoji suka ajiye yaya y tashi su suffaya d su ussaina Dan Ammy Bata Bari Anzo d su Noor ba …
Har zasu tafi ,safwan yacema hassana Ina so Noor?
Hassana Baki na rawa tace suna gidan Ammy ,yace danme bayace ataho dasu ba ?
Aishatu Tana sauraron su Addu’a takeyi ALLAH yasa yace aje a d’auko su Dan bazata kwana a gidan ba idan Babu su …..
Aiko safwan yace maza kuje keda Hamza ku taho min dasu ,Yaya dai kasa magana yayi bayason yima kanin SA fada gaban abokanen sa d Amaryar say kanen sa ,Dan haka yace a Bari zeje mayar d su sufayya sai y taho d su Noor din indai basuyi bacci ba …
Safwan yace Yaya ai ko sunyi bacci akawo su kawai ,Yaya bayason suyi ja’inja yace to ango kanina ,barin yi sauri ,y tasa su ussaina gaba Bayan sunma Aishatu salama…
Itama taji dadin kawo su Noor d ubansu y dage Ayi ,Dan haka t Fara tsara tare d su zata kwanta ma ….
Shima ango safwan Yana jiran kawo Mai yaran shi farin ciki shi …
Hamza d Hafiz sunyi addu’a sun musu fatan zaman lpy d samun zuriyya dayiba ,suka Mai sallama y rakasu har kofar gida wai ko zega Yaya y dauko su Noor…
Shiru Babu motar Yaya bare Alamar ta ,har su Hamza suka korashi gida y dawo yazo yayi zaman minti 5 y sake zuwa leka kofar gidan ko zega yayan Amman shiru y dawo parlour…
Tsakanin ango d Amarya Ana zaman kuramai ,shidai ango yaran shi yake jira ..
Amaryar ma ba Abin d tafi bukata kamar taga anshigo tasu sunzo sun rungumeta ba abinda zefi haka Dadi a wajen ta …
Ganin 12 saura minti 5 yasan d kyar in Ammy t Bari adauko su Noor ….
Dan haka y fara Kiran Yaya a waya a tsohon Daren to 12 wayar yaya akashe yasan hakance ta faru su Noor baza a kawo su ba ya buga siririn tsaki y jefar d wayar …
.ganin ransa y Dan baci tasan wata kila Akan kawo su Noor ne kamar yadda nata yake Shirin bacci ..
Ta dage tace, dadyn su Noor baza akawo su Noor din ba ko? Murya na rawa kuka nason kwace Mata fuskar ta lilibe d gyale Mai raga raga…
Abokin kuka ba a boyemai mutuwa ,yace eh tunda Naga 12 tayi nasan Alhj ko Ammy NE zasu Hana Amman gobe d kaina zanje n d’auko su ,kije ki kwanta g ledacan ki dauki abinda kikeso kici aciki ….
Kukane y kubce ma Aishatu ,shikenan daga ita sai Kato agida b yaran d zatayima wasa taji Dadi Yama zata iya kwanan gidan ?
Ganin kukanta y Fara taba Mai zuciya d har ze tafi y kyaleta ,ya dawo yace kukan fa na meye?
Sai d y maimaita tmby !
Tace ,innata nake tunawa ,cikin wani kuka Mai ban tausayi ….
Yace ,Amman kinsan ba inda za’a kaimiki ita ko yadda Kika barta haka zakije kiganta ko?
Taji haushin mgn sa ,tace nasani Amman anrabani da ita yau !
Yace waye y rabaki d ita?
Tayi shiru ,dan rainin hankalin dadyn su noor y Fara adabata !
Y sake tmby ,shiri b amsa Dan y Mai Raina Mata wayo ….
Yace ba a rabaku ba yanzu ma Zaki iya komawa d gudu inda take!
A sukwane ta d’ago d fuska ,Dan kalon shi !
Idanun su y gyauraya d na juna duk Saida wasu sakonni suka ziyarci jikin su ….
Yace yess ,g key din mota in kina ganin bazaki Sami Abin Hawa yanzu ba sai ki tuka kanki Dan ki Isa d wuri ,gobe nazo n karbi makulin motata ….
“Kai Aishatu ta furta a zuciyar ta Amman mutumin Nan y rainani ,yasan ban iya ko zura key din mota ba Amman yake fada min haka ,Dan shine sarkin bakar magana ,nagode ta tashi fuuuuu tayi d’akin ta nada tun lokacin Tana ‘yar Aiki a gidan ….
Yana Mata magana Yana cewa ba Nan ne d’akin ki ba ,Amman ko kulashi batayi ba ta shiga ta rufe tasa key daga ciki ta fad’a gado sai kuka …
D’aukan ledoji 2 yayi ya ajiye a kofar d’akin d ta shiga ,ya kwankwasa yace d’akin NAWAL Nan ne y zamo d’akin ki yanzu Auntyn su Noor g ladar Nan ki fito ki tafi can sai ki d’auka na barki lpy sai d safe …..
Tajishi Sarai ,Amman ta gwamace kwana haka ,sai kuka da taketa rusawa…..
*Maman shaheed*????
[1/21, 6:40 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE* ????????_????????
( _’yar Aiki Ko Matar Gida_)
*Shafin Nan nakune*
????????????????????????
*Jiddar samusa tawa* duk d kin denayi dani????
*Fatimah sokoto
*Fatimah zarah
*Yar baba
*Bilkisu
*Hauwa u
*Jiddar sokoto
*Jiddan Aliyu inata jigiyar ki kema*
*My Afreen Ina cigiyar kifa*????????