HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

_shafi N Arba’en d shida_

“Haka Amarya ta Kwana kuka ,Tana tunanin irin zaman d zatayi d dadyn su Noor kenan , gaskia in ba’a kawo su Noor ba bazata iya zaman gidan ba ,Kuma indai ta gaji d bakaken amsoshin d yake Bata ,zata yi kokari ankarar dashi d irin nata salon …

Rabi tunani rabi bacci haka tayi kwanan amarcin ta a gidan angonta tsohon mijin NAWAL”

“Shima dai Yana ganin ,be kyauta ba ta wata fuskar ,Amman wani ra’ayin nasa Yana ganin hakan shine daidai Dan shi ba Auren so yayi d Indo ba ,…..

Sai tausayinta y bijiro Mai sai yayi kokarin janye wa,kusan kwana yayi tunani shima …

“Da asuba a firgice ya farka ya makara ma ko masalaci baije ba y rasa jam’in yau ,Dan haka y gabatar d sallar y ….

Bashi d zabi ,zamanshi takeyi agidan Dole inbe kiyaye wani hakin nata ba y kiyaye wani ,Dan yaje kofar d’akin NAWAL nada inda yanzu y zama na Indo Mai Aiki amatsayin matar safwan kuma Amarya ,y kwankwasa Mata jin shiru yayi yawa y Fara zargin karde yarinyar Nan ba acikin t kwana ba?

Y murd’a handle din k’ofan ,yaga t budu hakan y tabatar Mai d Bata ciki y leka ba alamun ansha d’akin ma bare kwanciya y rufo y tafi d’akin d y barta Daren jiya …

Tun kafin y gama karasowa ledojin d y ajiye Mata ,suka Fara Mai barka d asuba ango ,muna Nan yadda ka barmu ,sai baiji Dadi ba …

Da kamar zekoma y rabu d ita ,Amman se Dan karasa y bubuga Mata yace ki tashi ko sallah kyayi ,y juya ze tafi yajiyo muryar ta Mai dadin saurare cikin tatausan lafuza ..

Ni ai tun liman na Jan Mamu nayi tawa Tama Jima d tafiya ……

Kai yarinyar Nan bade kwana tayi typing Ido biyu ba?

Inko hakane be kyauta Mata ba ,ya Kamata ace y dawo y duba halin d t kwana ,wata zuciyar tace Bata kyautama kanta bade ,a Ina zakaga halin d take ciki ,ta garkame k’ofa ,ita taso hakan ai Kai meye naka aciki ?

Yace hakane fa ,inji wani sashin zuciyar tasa…

Bashi d zabin d y wuce y tafi y barta karta Kara gayamai maganar d ze Bata amsa …

Har y koma y zauna yaga alamun garin y fara Haske ,ga alamun yunwa namai sallama ,Dan shima kwana yayi beci komai ba ..

Kawai sai y d’auki kazar Nan ta jiya (KWANTAI) ya je kitchen y danata oven yaran dumamata y fito d ita dama y tarasa ruwan zafin say had’a kakauran tea din shi y wuce dining d dumamamiyar kazar shi d tea din shi d yaji 3in1 Yana yaga Yana korawa d tea har y cika tumbin sa ,sai d uwar hanjin sa ta d’auka sanan y tuna d ‘yar mutane ,Dan Koda d ta zauna a great Dan shi matsayin Mai Aiki be taba horata d yunwa ba bare yanzu d take mai kula d su Noor ta gaske Dan haka y tashi yayi kofar d’akin d take d bega Alamar tanada niyar budewa ba …

Ya kwankwasa ,tayi shiru,sai d yayi n 3 tace inaji ?

Yace iyeee lalai yarinyar Nan ,hmmm yade basar …

Inkin tashi Karin kumalo ga ledar d kikaki kulawa Nan tun jiya nata jirai har yau ,Kya shiga kitchen din tunda b bak’on ki bane ki gyara ki ci Dan yunwa Bata d hankali Dan taci mutum Tara nagoma take jira inji wani waken Almajirai ,na fita hakin ki ….

Y wuce batare d t bashi amsa ba ,shima beyi jiran amsar ba Daman …

Bayan koma Dakin shi y Dan kwanta kafin yayi shiri zuwa gidan Ammy d’auko su Noor,yanzun ma yasan inyaje zesha tuhuma wajen ammy ne yanzu ze tafi …..

Itako , sai yanzu ma wakar Almajiran d yayi take Bata dariya ,hmmmm bazan fito din ba ,kasan hakin nawa akankane kake gayamin maga ,ohooo yunwar t kashe Ni ,Ina ruwanka d mutuwata ….

 

Around 8:30am y gama shiryawa y fito ,yayi hanyar fita y duba k’ofan d’akin d Aishatu take ciki har yanzu ledojin suna wajen yayi tsaki yace dama yarinyar na tanada taurin Kai haka?

Har yayi zuciya ze fita y dawo ,y tsaya bakin k’ofan ,ke bakiji menace Miki bane tun d’azu?

Ta yatsuna fuska daga ciki tace me kace?

Yaze kunnen rody ne dake tunjiya na dinga nanata Maki mgn ,Kan kici Abinci ko so kike kiyimin mushe a gida ,? D irin salon taurin Kan d Kika shigo gidan kenan?

Ganin Kar ya tafi Bata mayar Mai ba ,tace naji ai zan d’auka ko Nan da gobe ne ..

Kuma Ni bani d taurin Kai ,kawai dai nakanzoma mutum d salon d shi yazo min ne ,duk yadda ka ganni Kai Fara zuwan min ahaka ,Yi hakuri dadyn su Noor in maganata ta Sosa ranka ….

Y hasala d amsar d ta bashi ,Amman kalmar ta ta karshe t wanke wancan bacin ran d tamai ,babbancin Aishatu d NAWAL kenan inda itace bazatayi Abin d zata gyara *KUSKUREN* ta na farko ba…

Dan haka yace ,na tafi gidan Ammy taho d su Noor Kuma zamuyi mgn cigaba d karatun ki in hakan ze yiwu ….

Wani murmushi Mai sauti yaji ta sake gamida ajiyar zuciya Mai bayyana farin ciki ,tace Adal lpy amikamin gaisuwa ga Ammy d Alhajin mu …

Seda yayi kamar y dawo ,Abin d NAWAL Bata tab’a furtawa ba kenan ,tace Alhajin su? Aa be taba ji ba ,cikin zuciyar shi yace Kai yarinyar Nan tazo d nata salon fa ..

Y fice ba Bata amsa ba …

Itako murna duk ta gama cikata ,su Noor zasu dawo ga burinta d yake neman cika!

Bayan taji tashin motar sa ta tabatar y fita ta window ,sanan ta cire key ta fito falo tayi tuntube d ledojin d aka isheta dasu har t manta ma ,tayi kofar falon tasa key Dan Kar taji y dawo ,sanan tayi kitchen ta bud’e ledar farko …

Gamo tayi kyakyawa d wata dankwaleliyar kaza gashin injin Mai masifar kyau a Ido ,atake yunwar d ta dinga turawa lungu tun Daren jiya ta bayana t fito daga lungun batare d anbata izini ba ..

Itama tunanin gyarata tayi tamata want hadin kulikuli da su tumatir d Albasa ta dannata oven Dan gashi ….

Can Kuma ta had’a lafiyayen custard d’inta d tagansi sabone a kitchen din tasan nasu Noor ne Dan sune mayun custard ,ta zuba madarar gari aciki ta d’auko fresh milk ta zuba tasa sugar kadan ,ta gade abinta ta koma falo t baje a kafen tace wlh bazan mutu ba tunda ka raboni d gidan innata inda zanci kosai d kunu abina hankalina kwance ,Nan ko sai su wadanan Dan haka d su zan maye gurbin kunu d kosai na ….

Taci taci tayi Kat ,Abin yafi karfinta ,cusdart din ma kasa shanye shi tayi Dan haka t zubashi a Abun yin kankara t jefashi freezer anjima sa hadu ,(kara’i Dole Aisha Indo inji kawayen ki)…

Gidan ba wani gyara yake bukata ba ,tasan aikinta daga yau y Fara gashi dama ba malalaciya bace Dan haka seda t Fara shiga d’akin safwan shiga me huja Koda da take ba muharamarsa ba anbata izinin shiga bare yanzu ,gashi t tabata k’ofa a garkame take ,ta shiga ta gyara Mai komai ta wanke Mai toilet ta fesa air freshener masu dadin kamshi t rufo t fito falo t feshe shi d nashi room freshener shima sanan t leka d’akin d aketa kirari nata, Wanda ada can na uwar d’akin ta ne NAWAL janwuya ba ,inji Indo ba inji mmn shaheed ba..

Tana shiga taga ancanja komai na d’akin zama sabo ,ta sake yabawa d karamci irin nasu Ammy d Alhj ,ta godema ALLAH ta leka ko Ina ta bud’e ko Ina ga akwatunan ta a saman drower ga tsarin d’akin y birgeta ,baya bukatar gyara d’akin Dan haka ta feshe shi d room freshener ta dinga Jin Dadi d mamaki wai yanzu nanne dakinta na Aure?

D ta tuna d angon sai taji dama ba shine angon ba d tamore abinta , can t sake murna tace Aiko yau acikin shi zasu kwana d so Noor d’inta abinsu su more sabon Kaya….

Ta gama gyara ko Ina na gidan ,d’akin su Noor anan aka sa Mata kekenta d kayan d’inkin jakankunan ta d aka siyo Mata …

Ganin har Sha biyun Rana ,Babu su Noor Babu baban su kawai sai ta tashi ta Kama yanka karamar jaka d k’aramin takalmi na Mata ,kafin 1 harta gama hadasu farare masu ratsin Baki ,sunyi kyau dake kananane na yara wai Noor d’inta t hadama ,dama har na maza ta Fara koya ,shima Haneef t yanka Mai takalmi Mai kyau na maza t hada Mai yayi kyau shima Mai kalar fari d bakin Tana jira yaran nata suzo t basu …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button