KUSKURE Complete Hausa Novel

Ganin daya ta gota ,yasa ta shiga kitchen tunda Akwai komai ta had’a musu shinkafa Fara d taliya d miyar Naman kaji d lemon cucumber d na’a na’a d dabino ta sirkashi d Sprite mineral….
Ta jere su kawai take jira …
******
Huzna dai ganin ta Fara hada Kaya tun asuba mamanta ta tmby ta inda zata?
Ta Bata amsa d bikin Yaya safwan!
Aiko ta dinga Mata fada ,tace to kini d nake uwar safwan bance zani ba sakamakon Abun d yazo musu a bazata ,sun bada hakuri duk d bamiji dadin hakan ba ,to koni banace zanje garin yanzu ba tunda angama biki Amarya Tana gidan ta uwarme zakije yi ke ,tsurku ko gulma?
Huzna tace ,haba mamy nifa ALLAH y Sanya Alkhairi zanje yi Mai d ganin aunty tamu ..
Mamy tace Anzo wajen ganin Auntyn ku shine dai gulmar d Zaki inkinyi hakuri kinsan kina Nan ze kawota ziyara ma kinsan safwan d zumunci ,sanan kema Zaki iya zuwa in kun Sami hutu Amman b yanzu d kuke tsaka d karatu ba …
Ke Waima so nake ki rage zuwa garinan kije kiki dawowa har a koma makaranta sai nayi d gaske sanan kike dawowa …
Huzna ta buga kafa a kasa ,tace mamy karki katsemin hanzari Dan ALLAH ,kwana 3 kawai zanyi na dawo !
Mamy tace ko kinfi kuda naci fa ba inda zakije ,Banga ma’anar zuwan naki ba ,sai kinyi hutu shima olny 1 week Zaki spending ki dawo …
Huzna t buga kafa Tana gunaguni irin na sangartatun yaranan …
Tayi d’akin dadyn ta ,takai Karan mamyn ta ..
Shima hakuri y Bata ,yace tayi hakuri mamyn ta nada gaskia ,mace ce itafa ba namiji ba seda kiwo ,kawai jiya kawai ki tsara tafiya d asuba ki tashi hankalin mu d hada Kaya ,irin wanan tafiyar ma hankali baya kwantawa d ita gaskia ,bamu amince ba munfi son ganin ki kusa damu …
Cikin shagwaba t Kali mamy d take tsaye gefen k’ofa ,Alamar duk bakinsu daya d dadyn nata tayi dakinta Tana kukan takaici ….
Basa hanata Abu ,Amman tunda sukace aa to kawai aa ne ,duk nacinta se ta hakura ta bi umarnin su ,haka ta dinga wargaza kayan tafiyar d kafa Tana birgima a gado Babu Mai rarashi , readers ko zaku taimako d rarashi?
*****
Safwan Yana Isa gidan Ammy ,Ammy tace to goga har anfito d sanyin safiyar Nan?
Sai a lokacin y duba agogo yaga Ashe 9 ne da ‘yan mintuna ,dai yaji kunya musamman d yaga Alhajin su y fito Karin safe …
Safwan yaji kamar y koma Dan kunya ko Kar aga rashin damuwa da aurenta yayi har y bar Amarya y taho Dan haka y shiga zabarin neman tacewa kafin tmby Ammy ko Alhajin su sudiran Mai a kunne!
Alhaji sune ya kaleshi yace ,ah ango Nan ka kwana ne?
Safwan y Sosa k’eya yace aa Alhajin mu ,..
Ammy tace nasan ko karyawa bakayi ba wanan irin samako kamar gwauro zoga break mu taimaka ma !
Y gano magana Ammy t keson gayamai a fakaice ,tab inko yaji Abincin Nan zesha Cari gun Ammy d Alhaji gashi Yana son cin Abincin Dan kazar Nan b wani nauyi ne da ita ba …
Kawai yace aa wlh , Alhmd ! Sai da nayi dam nafito ..
Ammy tace ,nasan Aishatu Bata d wasa wajen shiga kitchen Kam ..
Ammy tasake cewa saura Dame?
Y gano har yanzu Ammy baza saurara Mai ba ,sai y rabza kyarya gashi y rasa kyaryar d zeyi …
Can ya tuno d maganar karatun Aishatu ,yace Alhamdulillah!
Dama nazo ne kafin naje office mu tatauna Akan karatun Aishatu d irin tsarin d za’ayi saboda su Noor?
Dama nacema Abban nawara sai yadda muka tsara daku zan koma na sanar dashi !
Alhaji ,yace hakan yayi kyau ,Nima munyi maganar dashi ,so nakeyi n farajin ta bakinta ,Alhmd tunda kazo d mgn yanzu!
Ammy taji dadin maganar sa d yadda y damu d ‘yar mutane haka ..
Ammy tace makaranta za’a nemar mata ta kusa d tasu Noor sbd su dinga dawowa kusan lokaci daya kaga hakan zefi Dadi …
Safwan din yace dama wata school nagani gaban tasu Noor ,saidai ita 1:45 ake tashi tasu Noor Kuma kaga 1:30 ake tashin su shine nace jiran 15minits ai baze gagara ba sai su dinga jiranta insun tashi zai abiya a dauketa Suma a d’auko su su taho gida tare ,tunda islamiyan su 2:30pm ake shiga tsarin in yayi shikenan ….
Alhaji d Ammy sukace ,shike Nan ma komai ya tafi a daidai , ALLAH y badu ilimi Mai Amfani ..
Safwan y washe Baki Amin Amin yaji Dadi su Ammy sun fahimce shi karyar makarantar Aishatu ta kwace shi d y koma dvsakakiyar gwiwa yau ..
Gidan shiru su Noor sntafi school Dan haka be gansu ba ,Ammy tace yaushe Aishatu zata Fara zuwa ?
Yace d ya Kamala komai saidai tafara cikin satinan ..
Alhaji yace b matsala ?
Yace eh Babu matsala ..
Ammy tace mgn me d’auko su, sudai su Noor sunada school bus to yanzu ba a school bus zasu dinga tafiya suna dawowa ba ,waye ze dinga kaisu Yana dawo dasu gaba daya?
Safwan yace, Ni zan dinga kaisu ,wajen d’auko su Kuma zan nemi Mai d’auko su ..
Alhaji d Ammy ,sukace tsarin yayi ..
Sai wani satin akawo su noor ko?inji Ammy tasan mgn kenan!
Y Sosa Kai ,yace dadai ankawo su yau sbd su Fara shiri tare, tunjiya ma Auntyn su takecewa dama a kawo su yanzuma wai sai ta biyoni t gaishe ku mun tafi dasu nace tayi hakuri zasu dawo ne mutanen nata kunsan sun shaku ,harma tace na gaishe ku sosai ..
Alhj yace muna amsawa ,ai shakuwar tasu Kam sai dai muce ALLAH ya dawamar da ita haka..
Ammy da safwan sukace Amin y ALLAH ,intayi hakuri zasuzo ne dama Bari nayi t Dan huta tunda tace haka za a kawo su Amman sai gobe …
“Safwan yace ,toh badan yaso hakan ba ,yace ALLAH y kaimu ,su Hassana sa kawo su….
Ammy tace aa kazo k d’auke su dai !
Yaji kunya Kar goben inyazo aga kasa hakurin sa ,yace aa Ammy Aishatun ma neman su twins d’in take d Janna har sako tabani na basu ,Dan ALLAH ki barsu su kawo su ,har sayi zumunci !
Ammy tace ALLAH y kaimu ..
Safwan y tashi y tafi gida ,d karfin gwaiwa duk d ba haka yaso ba yau yaso ganin yaran shi …
Aishatu na falo tanata duba litafin d nawara ta Bata ,Tana wata kujera kusa d hanyar d’akin d ta kwana jiya dakinta na da tayi wanka t gyara jikinta t fito a Amaryar ta sak…
Kawai bataji karar mota ba ,bataji shigowar mutum ba ,dake yanata spire key dashi y tafi yasan zata rina kule kofar yadda ta rufe kanta jiya Dan haka be batama kanshi lokaci ba y rike wani makulin bude falon..
Koda y taba yaji d key be tsaya kwankwasawa ba ,yasa key dinsa y bude sai ganin mutum tayi y shigo falon …
Abunda yasa bataji ba ,tayi nisa cikin karatun littafin ,seda t ganshi a falon kawai ..
Aiko tana d’ago Ido suka had’a ido ,ta kwasa a guje sai d’akin d ta kwana jiya Tana haki tasa key can ma Tana ajiyar zuciya a gado……
Shiko Abin ma dariya y bashi y zauna y dinga dariya ,yaga kamar ta gama girkin ,dama Abincin su Ammy y gama tayar Mai d kwadayi …
Yace inzaki fito ma ki fito ,mudai base anmana tayi ba komai namune ,y zuba Abinci d lemu y Fara ci Yana Santi Yana murmushin gudun Aishatu ,ga abubuwa Suma sai rawa sukeyi shi gudun ma burge shi yayi da zata sake d ya tsaya kalon gudu ……
*Maman shaheed*????????????
[1/22, 4:12 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????
BY
“`MAMAN SHAHEED“`
*KUSKURE*????????♀_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)
_shafi N Arba’en d bakwai_
“Safwan Yaci girki yayi Kat ,sanan ya tashi y tafi d’akin shi ,kafin y wuce seda yaje kofar d’akin Aishatu yace ki fito n Gaya Miki yadda mukayi Kan mgn makarantar ki d Kuma dawowar su Noor!
Aishatu Tana ciki tanajin shi ,d kyar ta iya furta to !
Har y shiga d’akin shi y dawo falo Babu Aishatu Babu alamun ta …