KUSKURE Complete Hausa Novel

Y kunna TV Yana kalo ..
Jin Alamun Yana falon har yanzu ,Kuma tunawa d anmata fada Akan bin umarnin mijinta Dan haka tayi shahada ta yi niyar fitowa kawai …
Wani zumbuleleb hijabi ta sako har kasa ta bude k’ofa t leko Dan ganin inda yake Dan tasan inda zatabi ..
Tana lekowa suka had’a ido Dan Yana setin fitowa daga d’akin tane ,d sauri t koma Tana ajiyar zuciya ,wani matsanaicin kunyar shi takeji haka kawai fiye da da …
Ganin y Mata shiru ,kuma Bata d tsari ,Dan haka kawai tayi shahada ta fito taje tamai sallama …
Ko kalon ta beyi ba ,idon shi a TV ,y amsa …
Can ta tuna ko gaishe shi batayi ba ,Dan haka tace, dadyn su Noor anwuni lpy?
Yana kalon TV dai yace ,lpy Lau..
Tace , Alhmd!
Tayi shiru ,shima yayi shiru ….
Bayan wasu mintuna har ta Fara gajiya d zaman jiran shi .,…
Can yayi gyaran murya ,ya Fara cewa, Ashe kinzo Jin mgn karatun kine ko?
Cikin zuciyar ta ,tace Kai Kama manta ne!
Ya sake cewa ,munyi magana d Alhaji d Ammy Kan ,Zaki Fara zuwa wata school ,Zaki dinga tafiya dasu Noor karfe 7:30 am sanan su Noor za’a tashe su around 1:30pm ke kuma Sai 1:45pm za a tashe ku ,ki ga Akwai Karin minti 15 a tsakanin ku ,Dan haka nace su Noor zasu dinga jiranki Dan nafiso ku dinga dawowa tare , school bus d’in su zata Dena kaisu Tana d’auko su ,tare zaku dinga tafiya Kuna dawowa kin fahimci bayani na?
Tace eh dadyn su Noor na fahimta,na gode ALLAH yasa kafi haka ,Allah y Kara karfin Arziki!
Yaji dadyn addu’a ,yace Amin nagode!
Har zata tashi y dawo d ita d cewa Baki tmby su Noor ba?
Tayi Dan murmushi Mai shiga ran masoyi ,tace wlh inason tmby Kuma?
Yace ,to jeki tunda Baki tmby ba!
Tace aa dadyn su Noor ,Dan ALLAH yaushe zasu dawo Tana wani murmushi Mai kayatarwa ..
Yayi murmushi shima ,yace Ammy tace bazasu dawo ba kwata kwata!
Cikin tuhuma d razana Aishatu ta dago Kai ta kale shi!
Suka hada Ido sosai , ita Bata d’auke ba shima be dauke ba ,Tana so d hango shin d gaske yake?
Shima so yake y hango ,yadda hankalinta y tashi d maganar …
Sai itace t iya d’auke idon ta sakamakon kwala d ta cika idon ,kadan y rage ta zubo …
Ganin zata iya mai kuka yace …
Nidai Ammy cemin tayi sai gobe zasu dawo ,su twins zasu kawo su ,me arahar hawaye !
Cikin murna d Jin kunya ta tashi t gudu daki Tana ALLAH y kaimu goben d Rai d lpy ….
Shima murmushi yayi ,y Lula duniyar tunani…
******
NAWAL nason Kara ganin hotunan Amarya ango ,Amman waya tace Bata Isa ba sakamakon makata d kasa d tayi har taci screen …
Dan haka ,wani iri ta zauna ,mama ko kulata batayi ba bare t tmby ta damuwar ta ,har ta shirya babu kwarin jiki ta tafi Aiki ,dake yanzu t koma aikinta morning ….
Kafin t wuce hospital seda t Kira lawy a waya ,suka hadu ta Bata hotunan ta sake gani ,zuciyar ta na tafasa ,Tana sake karema Amaryar kalo ,tunanin t d nutsuwar ta sun kasa gano Mata wace Amaryar tadai San ba Indo bace …..
Ganin ta shiga wani yanayi ,lawy ta Fara karfafa Mata gwuiwa d karatun ta na ta basar t fita hanyar shi ,waye safwan ?
Kin San yadda maza suketa rushing akanki ,Dan kin ki Basu fuskabe ma d yanzu ‘yar motar Nan d kin jima malakar ta,Amman kin tsaya wai kina Tara kudin siyan mota d sallary ki …
Haba hajiyata ,shi Yana can y manta dake ma ,kema ki nuna Mai Yar halak ce ke ,me magana daya …
NAWAL tajitane kawai ,tayi kokarin boye damuwar ta ,har suka rabu .,…
Huzna Ranar d kyar taje makaranta iyayenta sun Bata Mata bajat …
Ganin hankalinta yaki kwanciya ta on din datan ta ta Fara viewing status na su twins Aiko ta Fara tozali d pix din Amarya d Ango …
Direct Tama hassana maga ta waso Mata hotunan Amaryar d Ba’a gayatar mutane bikinta !
Hassana t Bata hak’uri ,tace Abin ne yazo musu a haka ,suna bada hakuri. .
Can ta koma ,son Jin Abinda y raba safwan d NAWAL , hassana tace wata Yar matsalace ,har tasa Auren y jijiga …
Huzna dik yadda taso Jin gundarin zancen ,hassana Taki Mata bayani salasala yadda take so !
Sai tsaki kawai huzna tayi kamar Ana ganin ta , tacema to ita Amaryar ‘yar uwar Alhajin kuce?
Hassana tace aa! Da har zata Gaya Mata wacece sai ta tuna d huzna take chart fa ….
Aa wlh ,watace bakingabta a hoto ba ?
Eh naganta kamar naso na Santa ,mekama d Aljana ba!
Hassana tayi dariyar keta, tace Aljana Kuma tsabar kyanta ko Muni ?
Huzna taji wani iri Kar hassana t Fara Gane kishinta karara ,sai t wayance aa kawai dai tsokanar ta nakeyi ….
Hassana tace aiho …
Daga baya huzna t off din datan ta ,tanata kalon hitunan duk bala’en ta Bata Gane Aishatu Indo bace ,har ta hakura d gano Amaryar setaje t ganta…
Ranar ma Amaryar angon kwanan dari2 a gidan angon nata ,tun d ta gama musu girki ta kule d’aki Bata sake fitowa ba tasa key ,ganin ta takura kanta haka kawai y kyaleta bece Mata komai ba y barta yasan d su Noor sun Zo zata daina ya sani …..
Washe gari da wuri kafin shiga sallah y kwankwasa Mata k’ofa ,ta amsa d to zantashi ,nagode .
Sai yayi murmushi ,y wuce zuwa masalaci Abin shi .
Bayan y dawo y koma d’aki yayi karatun Al_Qur’ani d su Azkar din safe …
Itama , Aishatu haka t dinga Azkar tanama iyayenta d Inna Addu’a kamar yadda ta saba …
Shiko Bayan y gama kitchen y should gam y soya plan10 da ya dama cusdart y zuba fresh milk y d’auka zuwa dining bayan y gama break din shi….
Ya wuce zuwa wanka d shiryawa Dan y bar gidan y tafi school d’in d zesa Aishatu Dan jiya sun Fara mgn d pc din school d’in shine zeje su karasa yanzu kafin y wuce office…
Sanan Aishatu zatafi sakewa intaji baya gidan ….
Bayan y Kamala y fito cikin shigar ta birgewa ,y Zo y kwankwasa Mata k’ofa ,Ni natafi sai na dawo su twins zasuzo d su Noor …
Daga d’akin yaji tace, to dadyn su Noor ALLAH y kikyaye hanya ,su Kuma ALLAH y kawo min su lpy ….
Yace Amin y fice Yana sakin murmushi ..
Bayan y fita taji fitar motar sa ,sanan ta sadada ta fito ta karasa key a parlour duk d tasan dai Bata tsira ba ,a tunanin ta zata dinga kula da taji abtaba kofar …
Kitchen t nufa Dan neman ma cikin ta hakin shi ,ta samu ta data taliyar yara lndomie ta soyakwai Mai su Albasa d su tumatir aciki ta had’a tea ta koma d’akin ta yau batayi falo ba ,kamar Mara gaskia …
Bayan taci tayi Kat ,tad’an huta kafin t Fara gyara d’akin dadyn su Noor t wanke Mai bathroom dinshi t feshe d’akin ,sanan ta fito t gyara falo ta sake shiga d’akin d akace shine nata ta gyara shi sama2 sanan t sake karemai kalo Tana yaba d’akin tare d Alwashin cikin shi zasu kwana d su Noor yau insha ALLAH.
Bayan ta gyara ko Ina ,ta je ta dubo Babu Aya a gidan da ta had’a kunun Aya Dan haka kawai ta d’ebo wake ta gyara t wanke ta jika kafin ta markada shi ,ta yi priderice Mai kayan lambu yayi kyau ta juye ta Adana ,tasan ko zasuzo sai After 2 sbd school..
Bayan ta gama ta blanding wakenta y ta zuba a wasu mazubi masu kyau dama ta yayanka kwanta d zata zuba ,Bayan t Gama had’awa ta Dora a gas ta rufe …
Ta d’ebo filawar ta ta dama d lemun tsami kadan da Madara Bayan ta zuba ruwan tacaciyar markadadiyar gyadar ta a Kan gas ,Yana tatasa ta zuba kulin filawan Nan ,ta jijuya ta d’auke yayi kyau yayi fari ta zuba Madara ta ruwa d ta garin sugar y bada wani gardi Mai dandano ta juye a jug Mai rike zafi ,ta duba alalar itama ta dahu ta juye a mazubi ta jeresu Kan dining a falo ta d’auko juice ta ajiye na kwali manya guda 3 su kawai take jira …