HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Sunata kalo har bacci yayi gaba d Noor d haneef ,Bata sani ba Jin shiru yayi yawa ta duba taga sunyi bacci daga ita sai Mai tsaron ta ,d sauri ta Fara kici kicin janye Noor tarara Kai Haneef tukunna !

Ganin tanata kiciniyar gyarawa d kasa gasu duk a jikin ta ,sai safwan y taso garin y d’auke Mata Noor hannun su y gyara d na juna wasu sakonin gagawa suka Isa garesu …..

Y d’auke Noor din ,ta mik’e t d’auki Haneef ,ta zarce dakinta d safwan yace malakin ta Dan yau se kwnan can d su Noor …

Ta Zo ta karbi Noor suka sake sabanin taba juna , yayi gagawar karban ta t kaita dakin d takai Haneef ,safwan Yana kalon ta yace Amman tare zaku kwanta ko?

Tace eh ,yace to ..

Ruwa ta d’aukan ma su Noor sbd akwaisu d Shan ruwan dare ,ta Mai sai d safe ,yace ALLAH y bamu Alkhairi ……

Ta shiga t Danna key ,sai addu’o’en bacci d ta musu ta komo gefen su ta kwanta hankalinta kwance ….

Shiko yanacan ,Yana fama d sak’on d tabar Mai ,Dan har yanzu bedena yawo cikin jikin shi ba …..

 

 

*Maman shaheed*????
[1/28, 4:46 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE*????????‍♀_????????
( _’yar Aiki Ko Matar gida_)

 

_shafi n Arba’en d takwas_

 

“Ganin karatun wasikar jaki baze kaimai ba ya Samu y kashe kayan kallo y nufi d’akin shi don y kwanta Shima”

 

Bayan y kwanta kewan yaran shine y bijiro Mai ,kuji gulman safwan Kodacan dasu yake kwana ohon Mai ,Yana Kuma Kara yabana Aishatu d iya gyara” Dan da datake gyara Mai d’aki baya ganin d’akin Yana birgeshi kamar yanzu Dan dacan sata akeyi Kuma shi bada son ranshi ba yanzu kuwa ta d’auke shi a matsayin aikin ta ” Yana sake yaba Mata yadda Bata d’auki Aikin gida wani wahalalan Abu ba , sai daga baya bacci y d’auke shi ,baya.

Bayan y tashi d Asuba ze wuce masalaci ,y tsaya k’ofan d’akin Aishatu y nowk 2× yace sallah mode activated! Tace to dadyn su Noor daga cikin d’akin a yanayin magagin bacci, sanan y tafi zuwa masalaci …

Bayan t tashi a dakin tayi Alwala tayi raka’atanil fijir tayi subhi ta zauna zaman Addu’a kafin t fada kitchen…

Bayan t Gama t fada kitchen t Fara hada musu break soyayen dankalin turawa d kwai d cusdart sai farfesun Koda ,kafin t Kamala ta hadama su Noor ruwan wanka ta Fara tashin Noor ta Mata sanan t tashi Haneef yanata mitsika Ido wai baccin be ishe shi ba ….

Bayan t saka musu uniform ta ajiyesu zaman jiran break ta zubama kowa tace suci su k’oshi Wanda be k’oshi yamata mgn ta Kara Mai don karsuje school d yunwa…

Bayan fitowar dadyn su Noor ,hakan y birge shi matuka y sake yabama kokarin Aishatu ….

Bayan Aishatu t gaishe ,su Noor Suma suka gaishe shi y shafa kansu y samusu Albarka ..

Noor natacewa shima y zauna azuba Mai Breakfast inyayi brush …

Dan haka y gyara zama , Aishatu t zuba Mai har seda y dakatar d ita t hanyar y ishe shi haka sanan ta tsaya …

Bayan yaci y k’oshi y duba agogon wayar shi yaga 7:25 yace su Noor su tashi y mikasu wajen school bus d’in su ,kafin aunty su t Fara zuwa su dinga tafiya tare …

Aishatu ce t Miko Mai lounch box dinsu t goya musu school bag dinsu t musu Addu’a Adawo lpy suka amsa d Amin ,sanan suka Mata bye bye dadyn su y jasu sai wajen motar makaranta su …

Koda y dawo Aishatu t Fara gyara inda suka Bata ,Koda safwan y dawo y dinga mamakinta …

Can y kasa hakuri ,yace bakya gajiya d Aiki ne?

Har zata rabudashi tace ,Aiki ai abokina ne ,inda sabo na Saba..

Cikin zuciyar shi yace ALLAH yasa ba magn yarinyar Nan t gayamin ba ,inmgn cema ai ninaja …

Dan haka shiru yayi y koma d’akin shi Dan y shirya shima Don tafiya office…

Bayan y shiga Bata koma daki ba seda t Gama gyara falo d kitchen Dan so takeyi tayi aikin jaka d takalmin yau ….

Bayan y gama Shirin sa n fita y Fara Mata magana ,ze wuce office ba wani Abu d take bukata?

Tace Mai eh !
Batare d ta d’ago t kale shi ba ..

Yadai bar Mata 5k yace ko bukata zata taso Miki zansa a kawo sako anjima …

Tace d ma kabarshi Babu abinda zan bukata,

Yace musu nefa banaso ,

Tace shikenan ,

Ya fice Yana sai y dawo ..

Tace ALLAH ya tsare gabanka d bayanka gefen Daman ka d gefen hagun ka, samanka d kasan ka , ALLAH y hadaka d halaliyar ka fatan Alkhairi har dawowar ka …

Yaji dadin Addu’a ,Dan seda y Dan tsaya y gama saurara sanan yace Amin ngn sanan y fita ….

Bayan Aishatu tagama ,dinka jaka set 3 sanan tayi musu takalma ,sai ta huta har tadanyi bacin kailula …

Daga baya t tashi t blanding kayan miya Bayan safwan y Aiko d sakon kaji ta soyesu tayi peppe chkin ta dafa musu shinkafa d wake d hadin salad Mai kyau d su bama ta rapin dinshi yasha garnishing …..

Bayan su Noor sun dawo t zuba musu sukaci sukayi Kat ,ta musu wanka tasa sukayi Alwala sukayi sallah tasa musu uniform din islamiya d kanta ta rakasu makarantar Tama manta d wani sai an tmby in za’a fita …..

Bayan sun dawo daga makaranta tare d dadyn su ,tacan y biya ya dauko su tun amota suka Fara bashi lbr Aunty Aishatu ce ta rakasu islamiya ,yaji haushi sosai ,Amman yaki yadda kishi ne y yunkuro Mai wai akanme zeyi kishinta ? Sam bega dalili ba ….

Kuma aka bashi lbr Abinci me Dadi tun a waje yawunsa y tsinke ….

Koda y dawo gida, Aishatu tamai barka d zuwa ,ya bukaci Abinci “tace Yana dining , bayan y ajiye jakar shi y bude yaga taliya ,sai y ce ina Abincin d yara suka Fara bani lbr akai ?

Aishatu sai t koma kalon su shida yaran? Tana son Karin bayani!

Haneef ne yace eh aunty shinkafar Nan fara da Miya d su kwai Mai dadin Nan d kazar d Kika Bamu Medan yaji yaji tayi Dadi wlh .,.

Nan Aishatu ta gano inda zancen y dosa ,tace dadyn su Noor d harda Kai na girka ganin baka dawo d wuri bane yasa n ajiyeta n girkama taliya nasan kanason Abu Mai Dan dumi…

Yace hakane ,ngd Amman abani irin Abincin d kukaci d ranan ,sorry fa n yaba d kokarin ki …

Haka ta tashi t zubo mai ragowar ta kawo Mai badan taso ba Tana mitar iyayi irin nashi ,…

Yanaci Yana Santi su Noor nata Mai dariya su sukaci taliyar suka Kara d Naman kajin Mai dad’i …..

Bayan yaci yayi kat tazo tatare plates din d t Bata Dan takai kitchen ,sai a lokacin y ga kwaliyar ta wani tissue boyel Mai masifar kyau y amshi jikinta ,sai y sake yabawa d tsarin ta atake y tuno d zuwanta Kai su Noor makaranta ,sai y fara juye kishin shi ta wata siga zuwa tuhumar meyasa t kaisu d kanta Baga Mai gadi ba?

Cikin inda inda tace, Naga ba nisane Kuma na kwana biyu ban taka ba shine n Dan rakasu ,t hango kishi afuskar sa zalla
amman sai ta d’auki hakan a matsayin halinsa n tsauri Dan haka t Fara bashi hakuri …

Yace ,Kar asake ,nibanason fitanan kinji ko ,d dawaya ma ai d komai zai dinga tafiya yadda yakeso ,yace zan Baki waya Amman banason numbobi barkatai aciki dg tasu Ammy sai ta tsirarin ‘yan uwanki …

Ita fadan da y Mata duk y gama kular d ita Dan ba a kishinta ta d’auki fadan ba ,Dan haka ma Bata Samu amsa Mai ba ,ganin tayi shiru …

Yace ko d kurma nake mgn?

T d’auki plate tace to akufule irin taji dinan…

Sedaga baya yaga be kyauta ba Abin d y Mata ,Amman Jin y Isa bazesa y Bata hak’uri ba …..

Bayan ta gyara komai taja yaranta sunata kalo ,yanatajin wani Abu game da ita ta wani Satan kalon ta d yake yanajin anushiwa a tare dashi ,Amman San yaki yadda d cewar t Fara samun matsugunine cikin farfajiyar zuciyar shi ,shidai yasan yau kawai d yake kalon ta t faranta ranshi Bayan haka besan wani Abu ba Kuma ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button