HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Lokacin bacci nayi Haneef y koma jikin dadyn shi yamai bacci ,itama Noor a jikin Indo tayi bacci …

Ganin lokaci y Fara ja ga tashin asuba gashi t gaji ta mik’e don zuwa kwantar d su Noor…

Ta shiga kenan Ta kwantar d Noor ,Tana Shirin tafiya karbo Haneef kawai sukayi Karo d safwan Aiko Saida goshin su y hadu Dana juna ,shikam kusan sake Haneef yayi don y taro Aishatun …

Sannu y dinga Mata Tana taba goshi Tana wash! Wash! Can ganin t barshi d yaro a hannu tayi yunkurin karban yaron y Miko Mata shi yadda seda akasamu gamsashen sako atsakanin su na jiki d jiki ,Tana ajiye Haneef t juyo …

Safwan y talamo ta Yana murza Mata goshin Yana cewa sannu Kar y tashi bakiji ciwo ba ko?

Itama ta gama sandarewa sai yadda yayi d ita ,yanata mulmulamata gun wasu sakonni masu wuyar fade na shigar su , Aishatu CE Fara gano hakan tabajin moon d’inta y canja t Fara kwacewa daya gareshi ,shiko dama yaji wanan reaction din baida zabin d y wuce cigaba d Abin d yakeyi Dan besan yanayi ba ma…

Ganin t raba kanta dashi ne yasa shi ,dawowa yanayin shi n da ,yace sannu tare d wata irin kunya d y rasa Dame ze kirata ?

Shin meya Kai hannun shi jikin Aishatu?
Meyasa y ke murza Mata harseda ita t janye d kanta bashi ba?
Kai wlh banji dadin faruwar hakan ba …

Fita yayi Yana Mata seda safe …

Itako duk t kasa amsawa ma ,zafin buguwar goshin ma y wuce anbarta d tunani …

Tanason komawa falo ,haka t hakura t sa musu key ta kwanta Tana tunanin bak’on lamari tsakanin t d dadyn su Noor!

Shima har y koma falo yaga kalon baze samu ba Dan haka yayi daki Dan bacci …

Wanan bak’on lamarin aketa Mai yawo dashi cikin sasan jikin shi d kwanyar shi Yana nishadantu Kuma ,Amman a zahiri Yana jin shi be ji wani Abu daga jikin ta ba Yana karyata zuciyar shi ,nace dadin Abun zuciyar ka ka karyata bamu masu sauraro ba ….

 

Haka suka kwana kwance nanauyan sako ….

Kwanci tashi b wuya rayuwa ta cigaba a haka tsakanin safwan d Aishatu Amarya yau har sunkai sati biyu cur suna zaman na ma’aurata …

Inda tuni Aishatu ta Fara zuwa makarantar ta ,murna wajenta d su Noor Abun bakama hanun yaro ,safwan y kaisu driver y dauko su ….

Yau nawara zata kawoma Aishatu ziyara ita d angon ta hydar ….

 

Safwan y sa amusu tarba ta mussaman , Aishatu t Tama shirya komai n karban kawarta aminiyarta ta ,aranar safwan y Sami damar bama Aishatu faleliyar waya ,yasa Mata number shi d ta su Ammy d hassana d ussaina …

Ita Kuma tasa ta Inna ,Akan zata karbi ta su nawara d hidaya d mama d aunty zainab!

Bayan magriba safwan y dawo gida cike d nishad’i ,ita kanta Aishatu tasan Yana cikin nishad’i batasan me nishadin nasa yake nufi ba shiyafi kowa sani !

Noor d haneef sunata wasan su d wayar dadyn su …

Sai ga nawara d choice d’inta sun danno cikin murna suka tarbe su ,Noor Haneef d gudu suka musu oyoyo!

Bayan sun gaisa cikin begen juna ,suna tmby juna y amarci ? Oho Indo tasan ma meye amarcin ? Tunda Tana tare d su Noor ita ai amarci y kare ,tace lpy lau y naku?

Nawara Bata iya amsawa ba hydar ne y amsa d Alhmd!

Itako nawara cewa tayi shegiya kawata anzana ‘yan gari har d bada amsa haka? Anzama ‘yan hannu …

Bayan Aishatu t cika Baki dasu cincin gyreba d abinci ,suka zuba Ana Hira Ana ci ….

Daga baya hydar d safwan d haneef suka tafi masalaci don gabatar d isha’i prayer,Suma matan sukayi ciki don Alwala su gabatar d tasu sallah …

Nan nawara take tsokanar Aishatu ,kunga kawata Amaryar sati biyu kinyi bulbul abinki kin wani murje g angon ki ga yaranki kusa dake!

Nawara ta sake cewa ,mama n gaishe ki d Inna jiya mukaje da n dinga sakarma my choice salon shagwaba Dole y kaini ba shiri !

Aishatu tace ayya Ina amsawa ,Nima kuwa dadyn su Noor y kamata y kaini n gansu wlh…

Nawara tace kinsan basason kaika gida da anyi Aure sekace wahayi iyayen ma baso suke ‘ya taje gida daga anyi bikinta ba sekace fadar Aya ko hadisi sekin lalabashi sanan ..

Aishatu tace haba lalabawa sekace wani jariri ko yaro ?

Nawara tace to yimai t karfi mugani ko zai barki !

Aishatu tace tab d yaranshi zan barshi d sunce kaza zece toh ai !

Nawara t bude Baki ,haba kawata banason rashin wayon ki fa ,yaran nashine ‘yancin ki se sunce Abu? Yaran d a hannun ki suka taso d tarbiyar ki suke tunkaho ,ki farka wlh daga baccin d kikeyi …

Banace karki so yaran Mijin ki ko karki jasu ajiki bane kawai dai kisan matsayin ki daban wajen mijinki matsayin yaran naki daban wajen dadyn su ,haba irin salo d dabaru Nan namu na Mata har yaushe Zaki tsaya kina sako yara acikine?

Nifa wallah only 2weeks dinan d mukayi d my choice nasan takan abina sanan Jan linzamin sa nakeyi ta sigogi masu kyau d tsari Babu boka Babu maLam ,wlh inkin bisu sekinga yadda komai ze tafi Miki !

Aishatu tace hmmm kedai ,dama kamar jira kike akaiki gidan Nan ankaiki kowa y huta sekita sheke ayarki keda choice din Baki kuta kwantalewa d malkwayewan …

Nawara ta Fara Shan jinin jikinta akan kawar tata ,Amman ganin t rasa samun gamsashiyar huja ko amsarta ba yasa t yi shiru …

Himmm nide ina shawartan ki Akan Aure wlh b Kara ko Alkunya zallar madarar fitsarar so d kaunar juna ake d’ebe kewar juna dashi ,ki kamashi y kamaki baran ke d kikeda ‘yan adawa ,wlh sai kisa kafar wando daya d fitsara Mai kyau akan mijin ki d duk wani d ze kawo Miki cikas cikin aurenku …

Kuma wlh duk ranar d kuka hadu d NAWAL take ki wa ? Uwar dakinki Ada ,ta Gaya Miki cuta Baki mayar Mata d mutuwa ba wlh kin rako Mata duniya a gidanan safwan b wani Wanda ze karban Miki ‘yancin ki seke d kanki wlh ,Kar ki Bata k’ofa ko kusa ko Alama bama ita kad’ai ba d duk Wanda y tunkaro ki zeci zarafin ki Akan Aure ki ,Dan b haramun kukayi ba besaba shari’a ba matar mutum kabarin sa inji hausawa ….

Nawara ta labartama Aishatu kalamai masu ratsa zuciya d Alamu sunyi tasiri akanta …

Bayan sun idar d sallah su safwan suka dawo …

Suka taba Hira akaci Abinci d kwadayi ,sanan suka tafi cike d rakiya d kewar su sukabar Aishatun d safwan din ,Bayan Aishatu t karbi number nawara d ta mama …..

 

*Maman shaheed*????

???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE*????????‍_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi n Arba’en d tara_

Bayan su nawara sun tafi gida …

Aishatu ta gyara wajen Tana mamakin zallah farinciki d t gani malale Kan fuskar safwan har yanzu ,Tana cikin gyara t tsinkayo muryar shi Yana cewa …

Wai ke bakya gajiya ne Aiki ? Y kamata kibarma gobe haka Kuma …

Tace d so nake n kaisu kitchen ai dama sai gobe zan wanke su …

Yace to da dai yafi abari sai gobe a wanke …

Yana kalon ta t gyara Nan t d’auke wancan har inda su Noor suka Dan zuzubar d Abin cake seda t share ,yanata tausaya Mata karon farko d y Fara tunanin ko Aiki ze Mata yawa g school t Fara zuwa g hidiman su Noor,y Fara tunanin d me ze birgeta y faranta Mata Dan y biya bashin farantama yaranshi d takeyi?

Can y tunano ,y Mata Alk’awarin kaita gidan Inna t gaishe t y tabbata hakan ze faranta ranta matuka sanan y kaita su gaisa d Ammy Dan y kula Ammy b k’aramin son ganin su tare takeyi b kulin cikin bibiyar lafiyar ta take!

Bayan kwana biyu ,ranar juma’a dadyn su Noor y biya t school y dauko su d ita d su Noor dake d wuri ake tashi ran juma’a 12 :20pm y dawo dasu gida …

Yace d Aishatu d su Noor su shirya y kaisu su gaisa d Ammy d aunty sufayya daga can dai y zarce dasu gidan Inna su gaisheta …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button