HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Can t fito gashi ko turaren fesawa Bata dashi BAIWAR ALLAH ,haka t sid’ad’a ta d’auko nasu Noor t fesa abinta itama tayi kamshi kamar kowa …gashi Bata d jaka sai wani flat shoe d’in ta d aka taba Bata ,Tana ji dashi gashi y hau d kayan dama harda gyale su twins suka hado Mata Dan haka shi t yafo tazo ta Kama su Noor suka nufi inda d’an Bala driver dayaketa jin redeo a farfajiyar gdn …

Su Noor sunata ,murna , Indo t sanar ma d d’an Bala sun gama shiryawa ,sanan y kashe radio y shiga hannef a gaba su Indo d Noor abayan mota Indo nata gwalale ido Tana kalekale kamar bakuwar shiga mota”lol”

Koda suka Isa ,tuni an Fara shagali illahirin dubanin jama’a dangin Amarya d na ango sun hallaci wajen ,Dan haka Indo t dinga rabe rabe Dan ji tayi kamar jama’ar sunyi yawa awajen Dan haka d kyar t samu t zakulo inda su twins suke taje t gaishe su Aiko su Asmy d suhaima suka dinga yabonta wai tayi kyau kamar ba ita ba ,ita dai murmushi kawai tayi ….

Sanan sai g huzna t dano Tana ma hassana magana ,kawai tayi arba d Indo ,atake gabanta yayi wani mummunan fad’uwa takuma rasa dalilin haka ,can matsanaicin tsanar Indo t bijiro Mata haka kawai , ta gama kare Mata kallo t harateta t watsar t kamo hassana t rad’a Mata wata magana sanan t sake harar Indon sanan ta wuce ciki …..

Intako hassana karban Noor d Haneef tayi Tama Indo masauki t had’ata d kayan tand’e baki kala kala sanan tayi wajen momyn su Noor Dan damka su a hannun ta dan yau b ranar Reno bane d su zasu rikesu ahannun su ,to suna fama d jama’a Basu d damar rike yaran …

Momyn su Noor n ganin su t rungumesu Tana tambayansu karatu d sunci Abinci ,duk suka Bata amsa , Amman ‘yar matanan ko ta tambayi inda Indo take ,shin ko tare ma sukazo ? Ko ajikin ta Bata Samu tby su ba tunda ba ita ta haifo ta ba ,Allah y kyauta ,Ameen.

Indo intama hankalin t kwance sakamakon tarbar d ta samu gun hasana ,dama Dan ta momyn su Noor bajanta take ajiki ba in t ganta ma takura zatayi Dan haka , yanayin y Mata dad’i ,t cigaba d kale kalen ta ,Tana t ganin d’aurin Dan kwali d kwaliya kala kala harda t Al’janu ma , ga daururuka Suma ,dama tanaso taga Tana kashe d’aurin d’an kwali y bada ma’ana d’inan ….

can kayan motsa bakin t ganin gayun wajen ma Wanda sukafita had’uwa sun zage sunata kwasar gara Dan haka itama t d’an bude cikin ta fara aikawa cikin Nutsuwa d d’ari dari…

Can waje y rincabe anzo kamun Amarya , ga wani kid’a da ya gauraye wajen masu rawa nayi masu liki nayi masu feshe Amarya d turaren nayi aka dinga raba mayan kyaututuka , usaina ta ja Indo wajen Amarya SUFAYYA Dan su gaisa ,cikin fara’a ta karbeta suka gaisa usaina t karban Mata kyaututukanta t bata,Indo nata godia d yaba karamci irin nasu twins ,har take cewa ita dama a gdn su take Aiki tasan da taga gata , sanan ta ba hassana key d’in gdn momyn su Noor tace t Bata ita zataje t gaishe d Inna t kwana biyu bataje ba ,hassana tace toh har t Kara Mata su snacks tace t kaima Inna ,Aiko Indo tayi ta godiya sanan t fice daga wajen gaba d’aya t tari napep sai gdn innata itama t kwashi gara ..,..

Hassna taba mommyn su Noor makulin t karba tayi kawai b tare d t tambayi lpy Indo ko Ina take ba ta jefa shi jaka t zuge t ci gaba t sabgar t ta rabon Kaya tunda sune Akan bikin…..

 

Indo d gudu d farin ciki t shiga gdn Inna ,har innar n tsokanar t ke Kuma waya koroki kike haki ,ko kujerar makka aka baki fara’ar ki Taki boyuwa?

Indo zube Mata kayan tayi gaba d’aya ta d’au buta sai bandaki ….

Itako Inna zubama kayan indo tayi ,Tana tunani ko Ina Indo t samo su …?

Bayan Indo t fito ,tazube a cinyan Inna , Inna nadan dukan ta irin na wasa d’inan Tana cewa ,karki karyani ki barni d jinya ,tashi kiyim bayani Kan wanan tarkacen kud’in Dan kayan Nan dagani masu kud’i ne ….

Indo mik’ewa tayi t koro Mata jawabi sanan t waware Mata kayan robobin d aka Bata amun d kayan motsa bakin harda kayan gargajiya n Al’ada ..

Inna nata yaba karamci irin nasu twins tanata sa musu Albarka …

Indo nayin magriba ta tashi ,tabarma Inna tarkacen tace t dinga cin abinta har y kare ,ita zata koma Dan Aunty NAWAL Bata San t Zo ba ..

Inna tayi Mata Addu’ar d ta saba Yi Mata ,tace tayi maza Kar duhu y Kara shiga ,Nan Indo t tafi cike d kewan gdn su ….

 

Cikin hikima t koma wajen kamun Aiko Basu tashi ba har Bayan magriba anata bidi’a …..

Sai Bayan isha’i suka koma gdn Ammy ,

Wajejen goma n dare, Dan Bala driver yazo d’aukan su ,kafin t fito ita momyn su Noor ,ta bada su Noor d Haneef akaima Indo wai su shiga mota su jirata gatanan zuwa ,Aiko hassna t karbesu t kaima Indo ,Indo t kule can Bayan mota dasu ….

Su twins d huzna d su Asmy Suma driver suka samu Dan motar t musu kadan , sanan mommyn su Noor Tama kowa sallama harda Ammy sanan t shiga mota suka nufi gd …..

*Maman shaheed*
[12/28, 7:01 PM] First Lady????: ???? *WRITING*????

 

“`BY MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍♀_????????
( _’yar Aiki ko matar gida_)

_shafi na goma_

*Na sadaukar dashafin Nan gareku*
_zee baby jos_
_meelat tawa_
_zaibab din ummah_
_maman sultan_
_hajia wudil_
_ya kaku_
_maman shaheed_
(Takwara ta)
_muhievert india_
_first lady_
_maman Aslam_

 

“Cikin wasu mintuna suka Isa gida gaba d’ayan su, yayin d Haneef ya Jima d bacci a hannun Indo .

Momyn su Noor ,Noor ta ja kawai suka shiga gd ,su twins d su huzna ma sukayi ciki ,itama Indo t gama kici_kicin d’aukan Haneef tayi ciki gdn dashi …

A palour ta ajiyeshi Kan kujera tayi d’akin ta , ta cire kayanta ,ta canja wasu ..

Itama momyn su Noor nata d’akin t nufa , yayin d Noor take cemata bacci zatayi tace Mata taje Kan kujera t kwanda kafin a karkad’e musu gado bawai Dan yayi kura ko dati ba …

Su suhaima , Asmy, ussaina sunwuce dakin d suka kwanta jiya Dan sun gaji hutu d bacci kawai suke bukata…

Daga hassana sai huzna a palour suma suna shirin tafiya Dan su kwanta …

Can sukaji, karar mota ,sun tabata Yaya safwan ne dadyn su Noor ,Aiko mintuna uku suka shigo dashi palour ,Yana ganin su ya tmby su basuyi bacci ba , hassana ce tace wlh Yaya yanzu muke shiri , itako huzna sai wani irin kallo take binshi dashi Wanda t gama shagala acikin shi …

Can tace y s bamu ganka wajen kamu ba?

Yayi murmushi batare d y kaleta ba ,yace kamu sai Mata ai ,nakune, ta wani kebe baki Kai y s mazama ai suna zuwa kaga d munsha hotuna mun kwashi selfei …

Yace hhhh ko gobe ma ai zamu Sha Amman yau Kam ta wuce ,yayi gaba ma y barta Yana Kiran dear shi ….

Huzna kamar t bishi d duka Dan takaici ,besan cewa dadin Hira takeji dashi ba ,tayi tsaki siriri yadda hassana Bata ji ba t tashi ta nufi daki Dan kwanciya..

Yana shiga y Sami momyn su Noor n lalab’a Noor Kan tayi bacci …

Tamai sannu d zuwa , y fara ma Noor magana atunanin sa baccin be d’auketa b “Ina tariga tayi bacci ….

Yace aje akaisu d’akin su amusu Addu’a ,be gama rufe baki ba momyn su Noor t Fara kwalawa indo Kira around to eleven 10:45pm alokacin ……

Shine y dakatar da ita d cewa me zata Miki Kuma a tsohon Daren Nan?

Bud’an bakin sokuwar sai tace , zuwa zatayi t d’auki Noor t kaita daki har Haneef t kwantar dasu …

Y wani buga tsaki ya girgiza Kai ,yace haba wai sai yaushe Zaki bambance aikin Indo a gdn Nan d Wanda ba nata ba?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button