HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Kai NAWAL ma Akwai banza shakatafi ,sokuwa Tana Raye? Tazuba Ido ko d bala’i d tsiya batabi wata hanyaba ganin Hana yiwuwar Abin amman yanzu aikin Gama y gama Kai , sahoramar ce NAWAL wlh …

Cikin dabara ta ,seta kanta ,da taga kowa ita yake kalo kawai sai t yi dabara ,tace sannu Indo duk kin kode Haneef y tafi y barmu yaro me shiga Rai!

Aishatu dai ko kalonta batayi ba ,tace uhummm!

Ussaina tace ,Haneef Kam saidai mubi shi d Addu’a,nawara ma tace ,tabas Aishatu ALLAH y Kara muku hakurin jure rashin Haneef keda safwan d duk wani masoyinku ,makiyinku kuwa ALLAH ya nisanta ku dashi a duk inda yake a fad’in duniya kusa ko nesa …

“Zuciyar huzna sai d tabada daram!! Yarinyar Nan bade Dani takeyi ba Dan ubanta ? Wacece ma ita? Karde t fahimce Ni !

Ussaina tace Amin nawara , huzna sai tayi saurin d’aukan waya Alamar ankirata ,tabar d’akin Kar bakin ciki y hakakata ,…

Bayan sun idar d sallah ,maman nawara ta sa Aishatu a gaba akan tasa wani Abu a bakinta ,Sam Taki tace wlh batajin yunwa ta k’oshi ,lalami ban Baki Amman ko ruwa Taki karba d suka matsa Mata ma sai kuka ta rushe musu dashi …

Safwan ne y shigo d wasu mahaifiyar abokin shi don yima Aishatu d Ammy Gaisuwa ,ya shigo y samu Ana turka turka d ita Taki cin komai !

Ko d y shigo ,matan suka zauna sunama su mama Gaisuwa d Aishatu ,su namane kawai suka amsa , Aishatu sai kuka ,safwan y matsa kusa d ita Aishatu wai bazaki sama zuciyar ki salama ba ? Kukan ki ko kin cin komai baze dawo da Haneef ba ,jarabawace ALLAH y aiko Mana dashi Dan y jaraba imanin mu yaga y zamu yi, bazaki bada himma wajen Jin jarabawar ubangijin mu ba?

Ta dako zata Mai magana , bakin y kasa furta komai sai rawa muryar duk yadda taso tayi Amfani d ita wajen yimai magana Abun ya gagara sai hakuri tayi ,duk sun tausaya Mata ,ta kode ta jeme idon ta yayi lufu lufu yayi jajur d kyar yake buduwa inba kasani ba zakace ciwon Ido take Mai tsanani ..

Shima SAFWAN kwalace ta cika Mai ido ,sai maman abokin nashi ce ta dinga Basu hakuri d nasiha ,Tana shafa Bayan Aishatu ,duk yadda taso tsayar d kukan ta Abun yaci tura sai girgiza Kai kawai d takeyi …

Ana haka sai ga hassana d Noor wai Taki cin komai tanata kuka ,Tana a dawo Mata d haneef dinsu , hassana t Miko ma SAFWAN ita y karbe ta y Fara Bata hak’uri ,Noor kiyi hakuri kinji ? Haneef baze dawo ba Amman Ni Ina Nan Auntyn ki Tana Nan su Ammy suna Nan kinji ?

Cikin kuka tace ,ita tafison Haneef d’inta ,ya dawo ko akai ta inda yake itana zata bishi yanzu Bata d kani ? Ita wlh suje asibiti Adawo Mata d k’anin ta ita d Auntyn su …

Safwan y bude Baki ze cigaba d Bata hak’uri kawai kuka y kubce Mai sai hakuri yayi d maganar y dafe Kai kawai hawaye n shatata …

Noor kwacewa tayi daga wajen shi t koma wajen Aishatu Tana zuwa ta fad’a jikin ta ,Tana aunty kema Haneef ko? Kizo muje asibiti mu d’auko shi Dan ALLAH ,Haneef ka dawo wlh be mutu ba ,mallam yace in mutum ya mutu baya dawowa Amman Haneef be mutu ba !

Duk yadda Aishatu taso yi ma Noor magana ,Abu y gagara g bakin Tana sarafashi Tana magana Amman ba Abin d akeji ,tausayin su y Kara kama kowa n d’akin , mussaman safwan d yakejin kamar y tusasu cikin kirjin shi ko ze Samu sasauci a yadda yafi tausaya musu ….

Ganin Aishatu rungume Noor sunata ambaliyar hawaye ,yaga baze iya jurewa ba y fita yabar d’akin y koma waje d hawayen shi d sukaki tsayuwa …

 

********
NAWAL d jama’ar ta wasu nata Hira wasu nata faman cin Abinci ,wasu nata karban gaisuwar d zuwa ..

Jama’a da dama sun kawo sadaka ,Dan ko girki ba Ayi ba a gidan Ammy…

Gida y dinke d ‘yan Gaisuwa na kusa d na nesa ,jama’a kamar tutudo su ake ,gaskia mutuwar Haneef t girgiza jama’a d dama kamar wani babba …

Har dare tayi Ana karban gaisuwa, Bayan magriba su NAWAL d mama suka tatara suka koma gida d niyar gobe zasu dawo d sasafe , NAWAL Tana Ammy sallama amman tsakanin ta d Aishatu ji take dama abata bindiga ta harbe ta ita d d’anta amman dake algungumace tafita damuwar d mutuwar sai kukan munafurci take kamar ranta ze fita sai wani rarashin ta ake Suma tsofafin munafukai ….

Bayan sun fita Alhj su y jasu zuwa gida cike d Alhinin rashin Haneef…

Suma nawara mijinta yazo Dama y d’auke ta suka tafi ,mama ma Abba dauketa suka tafi ,Inna ko Ammy d safwan sunce dayi zamanta anan …

Gidan y watse ba mutane sosai saura masu kwana …

Safwan ganin anata fama d Aishatu d Noor sunki cin komai yasa aka Kira Mai su zuwa side din d yake zama na gidan inda shi acan ze kwana ,shima yaki cin komai Amman sbd su Noor zeci yanzu Suma ze sasu suci ko kadan ne…

Safwan Yana matuk’ar tausayin Aishatu d Noor ,kimarta d darajarta y Kara karuwa cikin birnin zuciyar shi son d yakema Haneef y Kara Dora musu yanzu ,Dan haka d kyar take tafiya hannun rike d Noor har suka shigo ..

Ta shigo d’akin bakinta d’auke d sallama Amman ba me ji sakamakon muryar ta d ta dashe Dan kuka ..

Ya Mata umarnin zama kusa dashi a Kan kujera ta zauna t sunkuyar d kanta Tana taba yatsun hanun ta ,Noor Kuma na jikin shi!

Ya Miko Abinci a babban plate yace suci gaba dayansu shima beci komai ba har yanzu …

Aishatu t girgiza Kai Alamar t k’oshi!

Yace karmuyi haka ! Banason gardama kinsani Kuma ,munata Miki magana d banhak’uri kinki ji ko?

Ta girgiza Kai ,yace fushi kikeyi d yin ubangiji?

D sauri t d’ago tace aa d Kai ,kuka n Shirin kubce Mata y janyota jikin shi Yana share Mata n idon ta ,yace matuk’ar ba budulci ko fushi kike d Mai kowa Mai komai ba ki dangana muyi hakuri ba Haka mukaso ba Amman shi haka y tsara Mana hakuri Dole ne agaremu ko munaso ko bama so !

Ta daga Kai !

Yace yi magana ,kin hakura kinyarda inda Haneef yaje muma zamu?

Ta daga Kai Alamar eh ,yace aa d Baki zakimin magana Yana shafa kafadar ta Yana rarashin ta yanajin wani sanyi n ratsa zuciyar shi …

Duk yadda taso magana ,ba a ji daga Haka y Gane muryar ce ta dashe!

Yace muryar ce bata fita?
Ta d’aga Kai Alamar eh!

Yace Kinga aikin kukanki ko? Kinzama kurmar wucin gadi kinason magana Abu y gagara kiyi hakuri ki rage kinji?

Ta gyada Kai ,ta karbi wayar hannun shi ,ta shiga rubuta Mai wani Abu…

_dadyn su Noor wlh kukane baya shawara Dani bansan lokacin d yake tahowa ba duk yadda naso controlling din shi baya fasa zuwa wlh b lefina bane_

_haka duk yadda naso magana muryar Bata fita har na Fara tunanin ko bebiya na zama_

T Mika Mai Don karanta…

Yana Gama karantawa tausayinta y Kara kanashi y kaleta y sake rungumeta ..

Yace na fahimce ki ,sannu ,barin Kira abokina Dr sa’ed ko Akwai wani magani d ze bamu a Nemo Miki saboda washewar muryar Taki!

Y daga waya y Kira ringin daya biyu y daga..

Suka Gama magana yamai Gaisuwa ,y fada Mai sunan maganin d za’a Nemo Mata ,da na Sha d ruwa Dana tsotsa kanar sweet…har yace zata iya Shan su ice meant ,tomtom ma ..

Bayan y kashe wayar yace suci Abinci kafin yaje y Nemo Mata maganin a chemist…

Badan tanaso ko Yana so ba ko Noor ,haka y dinga Basu abaki kadan kadan Yana rarashin su Yana hada musu d kunun gyada Mai dumi sunaci har shi suka danci kadan ,yayi yayi su Kara suka nuna Mai sun k’oshi!

Yace sutafi shima zeje Nemo maganin ,har zasu fita y dawo d ita, banason kuka kiyi hakuri haka kinji ,ta d’aga Kai Alamar to!

Takana Noor suka tafi …..

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button