KUSKURE Complete Hausa Novel

Shima y tafi Nemo Mata maganin..
Bayan komawar ta ,huzna sai wani kalon tsana take Mata ,suffaya take cewa Ina Kika je inata nemanki muci Abinci ko kyafi Jin kwarin ci damu !
Kafin Aishatu tayi magana huzna ,tace ana makale d safwan Mana ,amutuwar ma Kya Bari kowa y watse ai kafin ….
Maganar ta kular d Aishatu ,Amman ba bakin ramawa ,Amman t Adana ta amatsatin bashi …
Sufayya ce tace ato Kinga lefinta ,mace d mijinta ! Nasan shi y kirata ma inba kiranta yayi b Aishatu b inda zata mace Mai kunya d sanin y Kanata ,kodai Ana jalous ne?
Huzna taji wani Abu y kare Mata kahon zuciya ,kardai sun gano ta ,meyasa t furta haka
Can tace ,yaba Yaya S ki dai San yadda muke d shi Dan uwa Rabin jiki , sufayya tace ai d aure tsakanin ki gware kukayi kuka fito ba …
Ganin suffaya t Gama gan,huzna tace ,ke malama Adana kalaman ki gida d zuciyar safwan b mazaunin
I dama Yaya Kika Kama ko nadan iya matsa Miki kizo ko a matsayin Mai Aiki na !
Kut huzna t Gama kuluwa ,Amman SUFAYYA t Gama d ita, …
Itako sufayya d Gaya take Gaya Mata magana Dan t Jima d karantar ta …
Itako Aishatu d ussaina d hassana d hidaya ransu fes ,hatta Aishatu Karo n farko d Alhinin Haneef ya Dan barta t ji farin ciki a ranta kenan tun rasuwar t ba wani farin cikin d y shiga kirjin t sai furucin suffaya …
Huzna ,cewa tayi malama ,Yaya Dan uwanane na Juni kin sani Amman inaso ki Kara sani mumukeda ikon sawa ko hanawa ,ki sani banice zan shigo gidanki ba Amman ki kwantar d hankalin ki me shigowar na Nan ,Dole ki samu abokiyar zama Naga bodarar ku fadada ……ta tashi t bar Mata daki ranta a bacce ,sun kula ita d suffaya dama tun auro t Bata Mata ba !
Su hassana d ussaina sukace t samu daidai ita,itama sufayya tace sun kula matuk’ar suna waje daya…
Bayan safwan y gama yawo chemist be Samo maganin b sai ice meant d y siyo d tomtom kawai ,Amman Yama abokin naki waya dama gobe ze Zo Mai Gaisuwa yace ze taho Mai dashi daga asibiti insha ALLAH!
Ko d y shigo y Miko ma Aishatu y Mata bayanin sai gobe za a kawo Mata maganin ta karba y koma d’akin shi shida Yaya Dan Yaya ma a Nan zasu kwana d sufayya!
Dare y raba sosai Dan kusan 12:30 ,wasu duk sunyi bacci hatta Noor Taki bacci ga baccin tanaji wai sai aunty ta t kwanta …
D kyar Inna d Ammy suka sa Aishatu ta kwanta ,Noor ma t kwanta a kusa d ita kamar zata shiga jikinta ….
Aishatu b bacci tayi ba seda t tabatar Noor tayi bacci t rufeta ta taso t d’aura Alwala ta Fara nafila tanama Haneef d mahaifiyar t d mahaifinta Addu’a in Yana Raye ALLAH y dawo dashi garesu ….
Kusan Asuba bacci barawo y Dan d’auke ta Akan Abin sallah!
******”
Washe gari a makare ta tashi ganin Bata Samu bacci b a salaya tayi baccin ma ammy tace su barta ta Dan samu bacci …
Aiko sai d taji motsin mutane Ana gaisawa Ana ta’aziya kamar a mafarki sanan t farka ,ta Kama salati tayi Alwala tayi sallah tanata addu’a d kuka sanan taje t gaishe d su Alhajin safwan tamai Gaisuwa shima y Mata yanata sa mata Albarka ,ta gaishe d Ammy d ‘yan uwanta har maman huzna duk wanan gaisuwar muryar a dashe kawai dai suna ganewa ne Ammy nata cemusu muryatace t dashe wasu nata cewa Tasha kaza wasu nacewa ta nemi shayi Mai su citta d kayan kamshi ,Ammy tasa aka dafa Mata da kyar Tasha kadan ….
Gari y waye anata kawo Abun sadaka ‘yan uwa d makota ,kunu d kosai ,waina d Miya,tea d bread ,harda su gurasa ba dashe ….
Su, NAWAL ma an Kara’so d kayan Abincin su Niki Niki ,Bayan sun gaisa , Aishatu taje har gaban maman NAWAL t gaishe ta tanata Gaisuwa itama t Mata ,tagane muryar tace t dashe tanata Mata sannu Tana ALLAH y Kara musu hakuri Baki dayansu ita Sam Bata tab’a ganin lefin Indo ba Dan b Abinda t taba Mata tsakanin t da ita girmamawa Abin Yana Kona ran NAWAL..
Aishatu t gaishe d NAWAL , NAWAL Taki amsawa sai d wata kanwar ta tace aunty gaishe kifa akeyi?
Sanan NAWAL tace a ina? Ni banji komai ba in zata bude Baki tamin magana kamar yadda d takeyi to duk wani sababe d munafurci ba kaiki zeyi ba ,wai ke kinibabiya algunguma, uwar meye y rike Miki murya ,kuka ko uwar wani y saki kukan ,koni Naga nayi kukan Nan dake n tsakani d ALLAH nayi ai muryata Bata dashe ba sai ke uwar makirci kamar ke Kika haifar min Haneef din ,dallah jeki kibani waje nasha iska kije karaci kurumtar ki ALLAH yasa muryar Taki t dawama a haka har karshen ki be shafeni ba daga ke har munafukin mijin naki …
Me Hali baya fasa halin shi ,duk wanan Abun maman NAWAL batasan NAWAL n aikatama to indo ba ,seda lbr y Isa gareta shine tazo t samu karshen ..
Kafin Aishatu t Mike t tafi ,Mana t kamo kafad’ar ta tace yi hakuri yarinyar kirki , ALLAH y Kara muku hakurin jure rashin Haneef ,karki sa maganar maman su Noor cikin zuciyar ki komai zakiyi kiyi Dan ALLAH, ALLAH y Miki Albarka tafi abinki ….
Aishatu t tafi ranta fess Mata Mai kirki su NAWAL Albasa batayi halin ruwa ba ,Ayi asarar gadon halin kirki …
Itako NAWAL jitayi Mata duk ta gama bayar d ita a wajen indo ,mama t dawo kanta bakiji Abin d muka Gaya Miki ba ko ? Kinyi n farko d karshe inasakejin makamancin wanan n gama zuwa Nan bazaki zubarmin d mutunci ba ,ke Kuma kici gaba d barma kanki Abun fada wawiya shashawa Mara lisafi yarinya renon ki ta fiki tunani d sanin darajar yaranki ……NAWAL sai kuka mama t tozartata Akan Indo ,kishin safwan,d haushin Indo d mutuwar Haneef duk suka hade Mata sai kuka ..
Har safwan y karaso yazo gaishe d Mana d Mata Gaisuwa ,itama tamai sai yaga NAWAL anata kuka y zaci kukan mutuwar d’anta yakeyi yace sai hakuri , ALLAH y bamu y d’auki abinshi ,sadai mubishi d Addu’a ,ganin Yana Mata magana kalaman suka Mata Dadi kamar Kar y Dena yatayi Tana sauraron muryar sa ,gashi ita girman Kai y hanata gaishe shi bare tamai Gaisuwa ….
Y tashi y tafi y kaima Aishatu maganin ta ,duk NAWAL n ganin su ,wani kishi y turnukota badan Mana n wajen ba d taje taci mutuncin su sede komai y faru wlh shegu maciya ammana t sake balewa d kukan kishi d takaici zuciyar t zatayi bingiga..
Seda y Bata maganin y CE Sha Dan ALLAH ,sanan y tafi ,….
Ranar ma wuni akayi ana karbar gaisuwar hannef ,har see dare su NAWAL suka tafi Kan gobe uku d anyi sadakar 3 shikenan ..
Huzna d suffaya anata gabzawa ,har huzna t Fara kin zama kusa d sufayya , Aishatu Tasha maganin muryar t Dan bude kadan …
Ranar ma kwana tayi Kan sallaya tanama ,Haneef d maman t d babanta Addu’a har bacci y dauketa …
Washe gari d asuba akayi komai n sadakan 3 Haneef ,na soyesoye aka Mai Addu’a ,Bayan samun Dunkin Al’umma aka raraba Abin sadaka ,cikin gida ma anata karban gaisuwa …
Aishatu ,ko gaishe d NAWAL batayi b yau sai mamanta kawai ,Aiko NAWAL t dinga aikamata d sakon harara …
Ancika ankarbi Gaisuwa har zuwa yamma wasu na nesa ma duk sun tafi a ranar ,su NAWAL ma suna Shirin tafiya ..
Huzna aka zo wajen NAWAL Ana Mata iyayi d Bata hak’uri Kan rasuwar d’anta d cin amanar d Indo t Mata Dan t samu abokiyar munafurci d hadema Indo Kai ..
Aiko NAWAL t fetse ta tace gulmar banza meye bakisani ba ? Tsakani na d dangin miji kallo amman b Amana d yadda ..
Duk yadda huzna taso ganar d NAWAL yadda t tsani Indo Amman NAWAL Taki fahimtar ta ,daga karshe t rabu da ita ,sujarabu baran baran ….
Bayan sun gama komai ,mama Tama su Ammy d Inna sallama d Addu’ar ALLAH ya Raya Noor ….