HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Ammy sunji dadin Addu’a ta ,sun tafi mama t Hana NAWAL cewa komai amman duk d haka seda ta rubuta wasika ta aikama Indo dashi ,sanan suka tafi …

Tabata hararar safwan ,ko kulata beyi ba ….

Gidan an watse har mama d nawara sun tafi Inna ma gobe zata tafi ,mama huzna ma gobe zasu tafi ,huzna ma t yadda zata bi maman in ba hakaba mutuwa zatayi d bakin ciki g sufayya t Gama tasota gaba ,Dan haka Dole t koma t sake sabon shiri .,..

 

 

*Maman shaheed*????
[2/3, 7:49 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_shafi N hamsin d uku_

 

“Washe gari da wuri su maman huzna suka shirya sukama kowa sallama ,huzna ma guntuwar takarda t faki idon Jama’a wulama Aishatu sukayi gagawan kalon juna ,huzna yes na isane nice Nan , Aishatu dai d’auke kanta tayi badan ta tsorata d huzna ba Dan Arziki Rasuwa kawai d Kuma muryar t taci yasa Bata biye Mata ba ,Amman t Gama d’aukan duk wani wulakanci d rashin mutunci daga NAWAL ko huzna ko wani me biyo musu baya ma Nan gaba ,tunda dai Bata d matsala d dangin mijinta sai wasu banzaye d zasu hanata rawar gaban hantsi!

To wlh ta shiryama duk wani iskancin su, ita b Akan safwan zatayi fada ko kinyadda d raini b ,Akan ‘yancin kanta ,kanta zata fitarma d kima d daraja…

Har su Hassana suka Raka maman huzna suka tafi ,wani Abu be Kara shiga tsakanin huzna d suffaya ba ,ita suffaya kiris take jira ,itako huzna taja linzamin rashin mutuncin t tayi gaba dashi …

Bayan sun tafi ,Inna ma tace zata tafi , Aishatu y dawo sabo sai taji batason tagiyar Inna ,su suffaya d Inna ne suka dinga Bata hak’uri ,Inna ma natacewa Banda shirmen ki badan mutuwa ba ma meze hadani dake? Hakuri ya zama Dole kicigaba d ma Haneef addu’a ,Noor Kuma ALLAH y Raya muku ita cikin Amincin ALLAH…

Ammy tace Amin ,suka dinga b Aishatu hakuri ,Inna n cewa su rabu d ita d iya shege goyata zatayi ko a jaka zata sata?

Safwan Ne d kanshi y mayar d Inna gida yaso Aishatu t bisu Inna Ce t Hana ,wai Kar Abin y zama wasan kwaikwayo Mana …

“Ganin yadda Aishatu ta rame daga jinyar Haneef zuwa Gama zaman makokin shi ga alamu d suka hango n fitinar NAWAL d ta Fara damun Aishatu yasa ,Ammy d wata yayar ta suka ce abar Aishatu a gidan Ammy kafin t Dan saki jiki sanan ta koma gidanta daga baya …

Bayan kowa y watse gida sai su kadai ,Ammy t gayama safwan shawarar d suka yanke ,hakan yamai Dadi Dan y Lura har yanzu Aishatu n cikin Alhinin mutuwar Haneef g kukan d Taki sasautama kanta seya Mata babban rarashi d nasiha akai tukunna …

Dan haka Ammy t gayama Aishatu ma ,itama taji Dadi Dan dama har tunanin komawar y Fara bijiro Mata b Haneef sai noor kawai gidan beze Mata Dadi ba ,sunji Dadi dukansu d hukuncin Ammy ..

Dan haka ,Ammy tace yaje y d’ebo musu Abun bukata su zauna a can part din gaba dayansu ,hakan yamai Dadi ,itako Aishatu tace d ma a wajen su Hassana ai akabarta d y fimata …

Bayan safwan y je y d’ebo musu har uniform din Noor y d’ebo Mata seda yayi kuka d yaga uniform din Haneef a tare d na Noor y ware y ajiye Mai nashi y Mai Addu’a yaci kukanshi y d’ebo ma Noor nata kayan sanan y deboma Aishatu nata kayan bana hatta pant seda y dauko Mata y hado a bag y taho y wuce dasu inda zasu zauna sanan y shiga wajen su Ammy …

Ammy d Alhj suka sasu a gaba sunata musu nasiha Mai ratsa zuciya suna nuna musu girman hakuri d karbar hukuncin ubangiji duk sunji sunyi naam zuciyarce take karyewa sai ahankali zasu Saba …

Wuni sukayi safwan ba inda yaje still wasu nata zuwa Mai Gaisuwa ,Mata ma wasu n shigowa gidan Gaisuwa…

Noor dai gobe za’a shiryata ta tafi school,safwan ko sai jibi zai leka office ..

Yama tayi lis gab d magriba wasu daga cikin ‘yan uwan maman NAWAL sukazo Gaisuwa ,wata nata hararar Aishatu ,itako ko ajikinta batasan tabayi bama ,sukayi gaisuwar suka tafi ….

Bayan anyi sallah magriba Aishatu nakan salaya d’akin daga ita sai Noor ,ta d’auko takardar NAWAL d t Aiko Mata t Fara dubawa!

_ke kaskantaciya ! Mai Aikina wacce taci gashina dna yarana! Wai har kin samu damar shiga gidan d na Yi sarauta n murza kambuna son Raina ,har kinajin kamar ke Kika haifar min yara anamimiya kin gama tugu kinyi Kane Kane d yarana har kin kashe min 1 to wlh kisani Ina Nan dawowa d rundunar yaki d manyamanyan Hadimai zan sake sarautata a gidan safwan Karo n biyu Wanda ko damar kasancewa daya daga cikin hadimaina Baki dashi_….

_Nasani wanan Rubutace ne Auren huce takaicina safwan yayi dake Dan y nuna min wai y haifu ! Abanza man kare nasan baze iya hada jiki dake ba ,ko a mafarki kazama kucaka Mai datin zani ,ki gagawan tarkata komatsanki ki koma gidan wanan kakar Taki Dan motar yakina a cike take d makamai_

*Daga dodon ki NAWAL*…….

 

“Hmmm wawiya Mara hankali d tunani babbar mota d k’aramin tanki ,shine abinda Aishatu t furta Akan NAWAL”

“Ta Kara d ,namiki nisa ,inkin Isa kizo mu gwabza Babu gudu Babu Jada baya ,da banason mijinki ma Amman yanzu son sa k’aunar sa nake kodan irin ku,sede ku mutu na afka kogin son shi inata nitso Babu Mai fiddani Kuma sai shi,zan gyara Miki *KUSKUREN* ki insha ALLAH!

“Aishatu aka sake bude t huzna ,Bari muji ita Kuma karyar haushin me take?

_Indoo kike ko indoodoo komade wa kike ,bar ganin tsautsayi d Rashin sani sun kaiki g Auren Yaya S,Ni ban yarda d Auren ba ki sanar ma malamin ki yaci karya y kwana d yunwa wlh ,asirin ki y kusan tonuwa Dan wanan Auren Ina tantama ace wai Yaya S y auteki me aikin sa?_

_lndo kazama ,kucaka ,duk da bansan sunan Auren ba ,Amman n iya Kiran shi n wucin gadi ,Dan ke ba type din shi bace bare y ji dadin Aure dake duk d nasan in Zaki mutu baze taba hada jiki dake ba ,Dan nagana ganin komai Dan Auren d ake more rayuwa y fita daban ,na gama ganin naku Babu shakuwa b morewa juna Babu komai sanyi qlou sai tarin nadama d Dana sani d Yaya S nasan yake yi Dan Dole yayi wlh_

_Wlh ki shiryama dawowa ta Dan gaba daya zan antayo kamar kogi Mai ambaliya duk wasu tarkace irin ki gaba zanyi dashi_

*Bye ‘Yar Aiki*…..

 

“Aishatu tayi murmushi ,tace bara a kufai ,karya Mai bin namiji ,kizo n shirya Miki keda ambaliyar ki duk wata musiba t duniya ai ALLAH y bamu maganin ta d Addu’a …..

Ya zama Dole n tashi Akan magauta na ,Akan wani safwan zaku yi kaina d mashi?

Yazama Dole d d’ebo makaman kare kaina dashi …

Tahada Takardun t yagasu Tana tnanin ,me huzna take nufi d Ana Gane Auren d ake morema juna?

Su basa morema junan su kenan?

Me take nufi d hakan?

“Kai ohon Mata ita tasani tayi kadan tasani dogon nazari ,aniyarta t bita ,d take min zancen malamina ALLAH y isan min ,niban San meye malami bama sai a novels ko gidan radio ko television ko films ,ita tasan wanan Kuma Amman b Ni ba wlh ,d ALLAH n dogara Kuma y isar min Akan komai da kowa …..

Can t Mike jin anfara Kiran isha’i tayi sallah ,ta Kara d shafa’e d utiri,tayi addu’a sisai sanan t salame ta tashi t koma parlour…

Tana fita sukayi kacibus d hassana yauwa kizo muci Abinci kiranki zanje dama …

Aishatu tace n koshi ,Ammy tace me kikaci?

Maza Zo ki d’auka ki kaima safwan nashi in acan zakuci to g Noor Nan ma ,kinsan in bakici ba itama b ci zatayi ba …

Taje t d’auki n dadyn su Noor ta tafi kaimai tare d rakiyar Noor d hassana t bita d jug n kunun gyada d Tasha Madara …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button