HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

By
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????‍_????????
( _’Yar Aiki Ko Matar Gida_)

 

_Shafi n hamsin da biyar_

 

“Washe gari d wuri Safwan y tashi Bayan y dawo dg masalaci yayi wanka y shirya ,duk Aishatu n kalon shi sai can ussaina tazo t kirasu zuwa karyawa a parlour Ammy”

“Tare d Aishatu suka tafi ,Tana ta matsanaicin jin kunyar dadyn su Noor d su Ammy”

“Kanta a kasa t gaishe d Ammy lokacin Alhj su be fito ba ,su ussaina suka gaishe ta d hassana”

“Suka Fara cin Abinci suna Hira safwan nata Satan kalon Aishatu ,Wanda t rasa Gane kalon d yake Mata “..

“Bayan sun kamala ,Ammy tace sai su Fara shiri Dan Ayi komai d wuri , Aishatu tace Ammy tun yanzu d anbari irin zuwa anjima ko yamma …..

Safwan ne y Mata wani kalo ,Ammy ta kakeshi shine yaji nauyi y d’auke idon shi ,yace gwanda su koma d wuri ku gyara ko Ina ku huta abinki…

Aishatu tace toh Ammy ,Ammy tace yauwa yarinyar kirki jeki kiyi wanka kafin ‘yan uwanki su Gama shiryawa Suma ,kaidai Naga ka hatama ashirye kake !

Y ce eh Ammy tun d’azu n shirya ,kinsan inaso Inna ajiyesu n leka office duk d ba dadewa zanyi ba ,Amman zuwan nawa nada mahimmanci !

Ammy tace hakane , ALLAH y muku Albarka ALLAH yasa agama d duniya lpy,suka amsa d Amin ,Ammy..

Aishatu t tafi t fesa wanka tasa wata atamfarta Mai masifar kyau dinkin daidai jikinta d gyalenta d takalmin ta ,ba kwaliya tayi b Amman tayi tas ,rabonta d kyau tun kafin rasuwar Haneef …

Su hassana ma sun shirya ,sunsa wani material dinsu doguwar Riga d sukayi anko dake duk kayansu iri dayane ,suka rolling d gyale Mai match d material din …

Bayan safwan ya gama shigar d duk wasu tarkacen d y rage nasu y umarci su fito ,Bayan sun gaisa d Alh y dinga musu nasiha d fatan Alkhairi d zaman lpy Mai dorewa ,y tafi y barsu a gidan Yana ce musu su maida hankali su tafi d wuri …

Aishatu tanata kukan rabuwa d gidan Ammy d rasuwar Haneef kowa y gano kukan nata d biyu ne , Ammy t jata t rungumeta tanata rarashi d Bata hak’uri d Mata Addu’a, d shimata Albarka ,har iyama sa da ta Bata hak’uri d Mata fatan Alkhairi d Addu’a ALLAH ya jikan Haneef….

D kyar Aishatu tabar gidan Ammy ,tare d su Hassana suka shiga mota Tana gaba ,suna baya har gidan ta..

Suna shiga sukaga b wani Aiki zasuyi sosai ba ,tunda Dama su ussaina sun gyara ko Ina sun goge Dan haka se ,Kara gogewa d shara d sukayi ..

Bayan fitar safwan ,sun kamala komai har sun d’aura lafiyayen girki …

Sun ci sun kishi ,suna zaune sunata Hira hankalin su kwance sunata debema Aishatu kewa Dan sun Lura Tana yawan shiga tunani Dan haka suka dinga Mata hirar samarin su d Shirin maganar Aure d suka musu magana sunaso su Aiko Ayi magana ..

Aishatu tace Ashe sun kusa Shan biki, ALLAH y nuna muna ,yasa Ayi damu naji Dadi matuka …

Ganin tanata Hira d nishad’i suka Kara janta d hirar …

Suna haka safwan yayi salama ,suka amsa dukan su ,d ledoji biyu a hanun shi , Aishatu ji tayi kawai t Mike taje ta karbi ledojin ta yi hanyar dining d shi t ajiye …

Yadda yagan su ,yamai Dadi Dan b alamun kukan Nan a fuskar Aishatu sema nishad’i d y hango g tarba Mai kyau d hakan y matuk’ar burgeshi ,d murnar zabon zama ze ziyarci gidan Auren shi kenan …

Bayan y tby girki , ussaina tace ankamala Yaya , Aishatu je ta Fara zuba Mai har seda ya dakatar d ita,taje fridge t d’auko kunun Aya Mai matuk’ar gardi d sanyi ta zuba Mai Yana Sha Yana Santi har y Kamala y dauko Leda daya yace wanan ku tafi d ita gida aba Ammy na ..

Ussaina ta radama hassana a kune ke mu ware Yaya y Fara korar mu ,Jin basuji me yace b ,yace ko bakuji bane?

Hassana tace to Yaya Dana yanzu zamu wuce zuwa gida kafin anjima akawo Noor ..

Safwan yace ,gulmar d take Miki kenan ? Ku tafi kamar Ana korar ku? Ussaina uwar tsegumi …

D saura suka had’a baki ,laaa aa Yaya dama Ammy tace kana dawowa mu taho wlh ,yace ok nazata gulma take Miki, kundai ci Abinci sosai ko?

Sukace eh wlh Yaya harda Kari ma , Alhmd mungode …

Suka d’auko gyalen su suka ,saka takalma sai gidan Ammy Bayan y basu kudin napep d yaso kaisu yaga Ina baze iya ba ..

Aishatu bataji dadin tafiyar su ba ,Amman t hakura tanata musu mgn akawo Noor d wuri Dan ALLAH !

Zaman kuramai aka farayi tsakanin safwan d Aishatu ,ganin wani Abu nata fizgar shi ,yasa y dinga janta d Hira har t Fara sakin jikin ta suna Hira ,har y ce Kira nawara taji lpyn ta kuwa ?

Tace aa!

Yace y Kanata kiji jikin nata ,mace Mai ciki Tana bukatar kulawa gurin duk wani makusancin ta ,Dan sannu Bata d’auke ciwo amman dadine d ita ..

Aiko ,sai taji tausayinta y shigeta ,atake t dau wayar t kirata …

Hello ,kawata y jikin?

Nawara ,ban sani b sai yau ,yarinya wlh bashi Abu yau gareka gobe g Dan uwanka?

Aishatu tayi murmushi ,tace me din cikin ? Kede d Kika hadiya ALLAH y saukeki lpy , ALLAH y baku lpy Baki daya d babyn..

Safwan murmushi y sake y fahimci inda hirar t dosa…

Su suke hirar su Amman Yana nishadantuwa d hiran ,kamar Ana Sosa Mai inda yake Mai k’aik’ayi ..

Nawara tace ,ke wai bazaki Conceiving bane ,mu tafi tare asha shagali lokaci daya?

Aishatu tace ke dai ALLAH y raba lpy Ni karatu nasa gaba kimin fatan gamawa lpy b wani hiran ciki d shagalin bikin cikin ba ,ku bakwa tausayin mazaje d kashe kudi d sukeyi wajen hidimar suna ma wlh…

Nawara tace ,Kan uba au sune Abin tausayi ko mu? Mufa ranmu a hanun ALLAH yake mutuwa ko rayuwa sun jika Mana Aiki sun barmu dawainiya …

Aishatu tace to su ransu a hanun ki yake ,kowama ai tsakanin mutuwa d rayuwa yake…

Nawara tace wlh bazaki Gane b yarinyar , ALLAH inaronkon ka d sunayenka tsarkaka ALLAH k azurta safwan d samun zuriya a jikin Aishatu Nan kusa taji Abin d nake ji ….

Aishatu tasa dariya tace, ALLAH y shiryeki nidai agaishe d hydar d baby na kice inason shi ko inason ta Ina ta gaishe shi ,bye..

Safwan beso t kashe b hirar Tana kayatar dashi matuka kamar danshi akeyi yajeji duk d besan me nawara takecewa b Amman Yana hassashe a maganganun Aishatu…

Bayan t Gama ,sunata Hira ,sun Dan saki jiki ,har suna mamakin yadda suka saki jiki d juna haka ..

Baduyi aune b sai ji sukayi Ana Kiran sallah magriba ,sun shagala d Hira …

Sai a lokacin Aishatu t tuna d ba a kawo Noor ba!

Safwan yace ,hmmm Ammy kenan may be taga dare yayine tace sai gobe Akira yanzu aji dalili ta ba mutum amsa daidai d tmby d y Mata ,ko Zaki Kira kiji dalili?

Aishatu tace aa Kai dai k Kira ka tmby ,yace aa wlh ki sama min lpy d Ammy Akwai dalili tunda kikaga haka ,y tashi yace barinje sallah ..

Jikin Aishatu b kwari ta gabatar d tata sallar itama ,tanata tunani Bayan t idar Tana jira safwan y shigo t tambaye shi me zeci ta dafamai ,

Ganin tunani ze Mata yawa kawai t Fara tariyo hirar su d nawara Tana dariya ,Tana cewa shegiya kawata kunyarta duk t gudu Niko tawa Tana Nan …

Safwan bashi y shigo ba harseda y idar d sallar Isha ‘i ya shigo y samu Tana sallah y zauna bayanta yanata kare Mata kalo ..

Shikam yau yadda yadda Akan Aishatu Abun baze iya fasaruwa bana in ance y fada sonta ko kaunar ta ,cewa zeyi eh y fada harma d tausayinta Kuma dole ka so Mai son naka ,kodan sonda takema yaranshi Dole y sota shima ….

Ga wasu abubuwa d yaga Alamar sunata kusanto shi n Alkhairi a tatare d ita y zama dole y karbeta a matsayin Mata kobada son ranshi ba ,lodan wasu dalilai d yabarma kanshi sani …

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button