HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

Dan Haka taje gidan su ,suna cikin Hira tafa bijiro Mata d maganar d takeyi kwanaki Akan wani saurayi d tasamu Dan masu Abun duniya t kafeshi t dinga tatsarsa …

Aiko ,su haseenah ansaba d bokaye b boyeboye ta Fara ba huzna lbr malamin d irin kudin d ake biyan shi d irin amfanin aikin d irin iya aikin d yakeyi Dan shi kwarewar Akan iya jinsin su masa y tsaya yadda macce ko budurwa zasu kafe saurayi ko mijin su suta Shan shagalin su iya aikin shi kenan d kwarewar sa …

Jikin huzna ne yayi sanyi d taji irin iya aikin nashi , ita d takeso Indo t wulakanta ,Amman sai ace saidai tayi Abu Akan safwan Dan uwanta Mai taurin Kai ma kamar safwan!

Ganin tagana Jin lbr ta ita haseena sanan ita Kuma Taki fada mata tata damuwar d matsalar ,Dan Haka haseena tayi duk me yiwuwa don Jin dalilin son Jin aikin malamin ,huzna badan taso b ta fitar d sirrin ta g haseena d tsanar Indo d tayi ,ganin abokin kuka ba’a boyemai mutuwa ,Dan Haka haseena ta Bata gurguwar shawara Akan safwan din d irin Abun d y Kama amai ….

Huzna dai Bata d zabin d y wuce naaam ne ,d bazata amince b Dan Haka tace batada kudi a hanun ta sai t shirya Dan dad d’inta b wani sakar Mata kudi yakeyi ba !

Haseena tace ,to samarin ta fa meye amfanin su ,itama duk wani bushashar ta d tinkahon ta a wajen su take samu ,ita har gishiri t bayar aka Bata Manda ,lokacin d t fada cikin wani rashin kudi ga Aiki za’amata Bata d mai taimaka Mata Dan haka kawai tabada gishiri aka Bata Manda aka wuce wajen bukata ta biya …

Huzna zaro ido tayi ,tace ga wacce tafita sanin duniya gaba d gabanta ,tace aa adai jirani bantaba haka ba ba’ayi haka Dani ba ,tab to Dane zanyi tinkahon shiga gidan safwan din?

Haseena tace ,tab lokacin y zama bakiti b Gane komai zaiyi b lokacin sai yadda kikayi dashi ya zamar Miki stiyarin mota ba wani Abu d ze iya,in kinaso wlh Akwai gayu a kasa d zan iya hadaki dasu ki zaba ,kije kiyi shawara inajiran ki Dan kudin aikin ki d yawa bamusan bill din d ze caje muba Mai *KUSKURE* aikin shi n farko inya Fadi kudi ataya tundaga Nan ake samun matsala d aikin shi Dan Haka n fara Gaya Miki tunyanzu …

Huzna jikin ta y gama sanyi ,sukayi sallama d niyar zata dawo inta yanke shawara ……

 

Huzna ,taji babban Kai ,ta dinga jinjina maganganun haseena Tana sarama duniyancin ta ,Tana al’ajabi d mamaki ,uwa uba inda zata samu kudin yimata Aiki Akan safwan !

 

 

*Maman shaheed*????
[2/21, 12:56 PM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

*KUSKURE* ????????_‍????????
( _’Yar Aiki k matar Gida_)

 

_shafi na sittin_

 

“Huzna Bayan komawar ta gida tashiga Kai komo Tana neman inda zata samu uban kudin aikin d za’a Mata ,gashi Bata d halin su Bata d Wanda ta ajiye zai Bata Dan ko Abban t yanzu inba Abin d y shafi harkan karatun ta ba ,ba Abin da zai kaishi d’aukan kudi y Bata g kudi masu yawa bare ko karya tayi….

Can t tuno d shawarar haseena ,n inta shirya Akwai gayu har seta zaba! Huzna tace Kai! Ina tab yadda nakeson mutuncina d lpy ta hakama baze taba faruwa ba Dame zanyi tinkaho gidan safwan din ,tab Ina ,gashi tanata samari Amman t nutsu ta fitar d gwani Taki sai shirme d shashanci duk Wanda yazo yace Yana son ta sai tasan aibun d zata likamai ,ko na hali Kona surar jikin shi ko wani makusa Mara dalili har abokanen t na makaranta ,ga ranar su yanzu tazo ,can t tuno d wani Alhaji bishasha d y taba Mata tayi soyayya y Fara sakar Mata kudi Dan d Dollar y Fara yinkurin tsole Mata Ido ,ganin manufarsa akanta yasa sukayi kaca kaca suka rabu Dan shi b aurenta zeyi ba shi Dan tamore ne kawai aji Dadi a bale bishasha ,tun time din d yayi gigin Tana jikinta sukayi baranbaran ta tafi ta barshi Tana zagin shi ,shima ganin bazata wayeba Kuma b ‘yar hannu bace y rabu d ita yabi ‘yan hannun sa….

Yau sai d ta tuna dashi tace Dana suna tare har yanzu!

Can Kuma tace Kai!! D muna tare ai d yanzu y karar min da tatalin Arzikin mutunci na d sai dai fankon huzna Amman ba huzna yanzu ba ,tab d y gama Dani a rayuwa kuwa ….

Rayuwa Tama huzna tsanani Akan tunanin neman mafita ,Wanda zabi y rage nata ko yi ko hakuri”

 

“Aishatu yau gidan nawara aka ziyarta Dan tanason suyi Hira d kawarta agame d yanayin d suka cinci kansu …

Safwan d kanshi y kaita ,Bayan y Kai Noor school y ma hassana mgn in antashe su taje t daukota t kaita gidan Ammy tunda yau Alhamis…

Bayan y ajiye Aishatu yanata Mata togaciyar kula d kanta d babyn ta Yana wani kasheta d salon shi ,Abin har kunya yaso Bata , Tana sake tmby wai kodai dadyn su Noor y manta itace Indo Mai Aikin gidan sa abaya? Kai gaskia y manta irin wanan sauyi na gagawa ga ruwan soyayya d yake fama yayafawa kulin salon d yake fito dashi daban! Nidai indai hasashena y zana gaskiya rasuwar Haneef ne y kawo sauyin yanayi d Rayuwar mu gaba daya ,tanan ALLAH y shigo d hikimar shi ,cikin lokaci kankani komai yazama tarihi ,rasuwar Haneef tazama sauyin lamari atsakani na dashi kenan ,Amman fa ba’ason ranmu y rasu b ,Dan dai haka ALLAH y tsara y hukunta ne ,gashi yanzu labari y mugun canjawa ,hmmm Nima ALLAH y bani ikon nuna maka ainahin kakata na tsantsar so d kulawar d na tanadar ma , ALLAH yasa kafin lokacin n daina shaku ko kokwanto game d Al’amarin mu n d’auka tsarin ALLAH nee ban Isa n aureka b ko a mafarki ma ,ta bishi d wani kalo Mai cike d shauki !

Sukayi sallama yanata kewar ta itama Tana kewar shi ,yace t Mai waya in sata tafi gida tace toh!

“Tana shiga nawara t taso t rungumeta d gudu ,har seda Aishatu tace tab ! Madam kin samu lpy wanan gudu ko tuna Abin d ke tare dake bakyayi?

“Nawara ta zaunar d ita tace dallah mu munfara samuwa kune on top yanzu …

Aishatu ta cire gyale tace ,nidai wanko Mana tufa dinan bana zama bakina b wani Abu Mai Dan tsami inba hakaba nacika gidanan d ruwan yawu wlh …

Nawara t karba tayi kitchen Tana cewa b komai gidan masu yawun ne ai ,Nima har yanzu ban baryi b ,kinganni nice gyada nice Aya nice duk wani Abu d tsayar min d zubar yawu harsu goro …

Ta wanko musu sunaci suna hirar su ta masu juna biyu ( _Hmmmm ciki kenan ALLAH y sauki duk wata Mai ciki musulma lpy ALLAH y Bata sasaukan labour Dan Alfarmar annabi d Al_qur’ani , Ameeen summa Ameen_) Addu’ar da Aishatu tayi kenan d sauri nawara tace Allahummah Ameen ,wasu d dama ma d nasani sunce Amin y Allah ????

“Sun Jima suna Hira Bayan sunci wainar filawar su d faten tsaki Mai su wake d alayahu yaji manja d kakide d yajin dadawa ,sukayi Kat ,sunci Aya sunci gyada har rake sunata ‘yan kwad’ayin masu ciki dai ,sunata Hira , Aishatu nata ba nawara lbr laulayin Nawara nata kwantar Mata d hankali Tana komai zai zama tarihi Nan d wasu wattani …

Sun Sha Hira har tuwo nawara tasa wata yayar mijinta ta musu miyar zogale taji gyada ta dibi nata d cikama Aishatu food flacks d nata d tsarabar yajin dadawan ta ,Bayan Tama safwan waya yazo ,yaga flacks din Abinci ya dinga tsokanar su ,tazo ta Miki kwadayi ko kawar mu?

Nawara tace aa b kwadayi tayi b ,Dan duk team din mu daya ,jirgi daya y kwaso mu ,Kar watarana nazo gidan ku a girka min Abin d baby yake so ,ace nayi kwadayi ,to b yin kanmu bane samu akeyi umarni ake bamu mukebi kawai …

Safwan yasa dariya y Kali , Aishatu wai hakane umarni kuke bi har kema? Yace eh Mana ,mu ‘yan birn umarnin babeis din mune ,yace hmmm Naga zaku hademin Kai gashi abokina baya Nan barin Kara wuta ….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button