HAUSA NOVELKUSKURE Complete Hausa Novel

KUSKURE Complete Hausa Novel

 

NAWAL tanata budawa d motar ta ,ranar suna zaune a gida ita d mama take tmby mama wai yanzu kosu bazasuma safwan mgn y dinga kawo Noor b shikenan sun goyi Bayan rabata d Noor?

Mama t harareta tace kalon ki nakeyi kawai ai Naga gudun ruwanki ,Naga d kanki kike son kwatarma kanki yarki ….

Amman yanzu tunda kinzo d salama Ni da kaina zan gwada Masa mgn naji me zece!

NAWAL taji Dadi tasan uwa uwace ,t mikoma mama wayar tata tace mama g shi ki kirashi yanzu plsss…

Mama tasan tsakanin ‘ya d uwa Dan haka t karba t danna number safwan , ringing 1,2,3 ….y d’aga jikin mamaki d salama y gaisheta ,t amsa cikin kulawa ,t tmby lpy mutan gida .,……sai NAWAL t turo baki suwaye mutan gidan Indo shegiya? Kuji mama d rashin kishi!

Sai d taji anfara maganar Noor sanan ta saki Rai …

Mama tace y Kama ace Adinga kawota ,beci ace anrabamu d itaba ,tunda mun Rasa kanin t ita d take Raye y kamata mudinga ganinta ta Kar ayanke zumuncin d ta had’a !

Maganganun mama sun tabashi yasan gaskia y tada ,yace dama yanada Shirin kawo t matsalan NAWAL ce ita take bashi matsala shiyisa y kekin kawota ,…

Mama tace Ni zaka kawowa ita b NAWAL b Kuma Inka tashi zuwa daukanta a hanuna zaka dauketa …

Yace to mama nagode ,zanduba insha ALLAH ,bani d matsala dake mama ,tamai godia ,shima y Mata har y had’ata d Noor din suka gaisa y dinga rad’a Mata tacema mama zatazo ai ,mama tace sai nagangi kishiya ba haushi!..

NAWAL nataso a Bata Noor Amman mama Taki karta Bata Mata shiri …..

Daga bayama ta kashe wayar sukayi sallama !

NAWAL t turo baki ,Kai mama ki bani ita kikaki ,Kuma sai wani godia kike Mai komai y Baki oho!

Mama tace,uwaki y bani ,d ai y bani Ni b butulu bace meye bemin ba safwan yaron kirki Mai hankali namijin gaske ai wlh kinyi babban Rashi b Baki namiki ba Amman kin sake safwan y kubce Miki wlh…

NAWAL tace ai badan bamu dashi bane y dinga Miki Bayan ,shi kanshi yasan munfi karfin komai ,…..

Mama tace,ai yaba kyauta tukwici ,ko da naka kanason na wani halayar Dan Adam ne wanan ,butulu kawai …

NAWAL tace ,nidai ki Dena Mai godia sai yaga kamar Kari kikeso ai ko roko kikeyi ….

Mama tace,wawiya inda kuka Sha banban kenan ,airin tunanin ki ba shi ai yasan n wuce maula a gareshi girma na ne dai d tunda yake gani na dashi d kukaso barar min har yanzu begama barewa ba keda mahaifinki….

NAWAL t karaci mitar ta ,mama nata Mata fada ,har seda taji ba Dadi …..

Shiko safwan seda y nemi shawarar Ammy akan Kai Noor gidan su NAWAL ,Ammy t nuna Mai haka b matsala afara gwadawa agani ai sunada hakki akanta ,insun bada matsala gaba sai a kiyaye ,yace to …

Itace Aishatu koda y tmby ta cewa tayi duk Abinda Ammy tace hakan za’ayi ,yaji dadin girmama mahaifiyar sa d takeyi sosai ….

 

*Maman shaheed*????
[2/22, 10:31 AM] Maman Shaheed: ???? *WRITING*????

 

 

BY
“`MAMAN SHAHEED“`

 

 

*KUSKURE* ????????‍_????????
( _’Yar Aiki ko Matar Gida_)

 

 

_shafi n sittin d daya_

“Rayuwa Tana tafiya Cikin aminci d kulawa ga safwan d Aishatu ,d yarsu Noor”

 

Mlm mamman hafeez yanata gudanar d harkar shi d taimakon sadeeq ,Yana gudanar d binciken shi n gano mutanena d yaketa nema ,y samu y gano unguwar Amman sakamakon gine ginen zamani d canje canje d aka samu na tsawon shekaru Ashirin yasa y kasa Gane komai sai yawan zuwa erea d yakeyi Yana Dan gudanar d binciken shi batare d ya samu gamsashiyar tmby ko binciken d yake gudanar wa ba …..

Haka dai baiyi kasa a gwiwa ba yanata cigaba d neman Kuma Yana Kara ,sananta nema d Addu’a Dan y Fara matsuwa d gano wadanda yake neman …..

 

Ya Kai tsawon wata biyu Yana nema d Addu’a ,Amman har yanzu shiru, yanzu har takai ta kawo y Fara tmby suna ko ALLAH zesa adace ….

Cikin Aishatu y tura y fito yayin da n suffaya y tura sosai ,ga bikin su twins y gabato ,an fitar d anko sun gama tsara event din d zasu gudanar ,Ammy na tare d Ahalinta Cikin girmamawa d d’aukan su daya a gurinta …..

Gab d bikin dake Noor sun Sami hutu ,Bayan maman NAWAL ta sake ma safwan magana Kan zuwan Noor t musu kwana biyu ,duk sai yaji kunya d girman maman Dan Haka yace ze kawota Cikin satin insha ALLAH….

Bayan yasa Aishatu t hada Mata Kaya a bag ba sai d y tmby yarinyar yaga tanason zuwa sanan y barta ,y kaita taiyima Ammy sallama yaba su twins suka kaita Dan bayaso yaje kaita su had’u d dadyn NAWAL ko NAWAL d ya tabbata mama ze tarar d y kaita d kanshi …..

Ranar Aishatu d Noor aka dinga mararin juna akayi bankwana cike d kewa ,a gidan Ammy suka wuni har sufayya suna jiran kawo lefen twins dake mazane zasu kawo b bidi’a Dan Haka suketa jira d wasu daga ‘yan uwan Ammy….

 

Ba jimawa kuwa abokanen Alhj su safwan d su Yaya suka karbi lefen akwatuna dandatsa2 nagani ayaba kowace d irin nata d irin kayan d ke ciki na wanan n wane na wanan ,Kaya komai yaji g buhunhunan shinkafar su bibiyu d da carpet d kayan lalle dasu kumbo cike d kayan gargajiya …..

 

Bayan sun tafi ,su Yaya d safwan suka Kali kayan tare d su Aishatu har su Ammy a tsanake suna yabawa d fatan ALLAH y nuna musu lokacin Nan d sati hudu za’a d’aura Auren wata daya kenan…..

Bayan su twins sunje gidan su NAWAL , a parlour suka Sami NAWAL sunata salama sai daga baya t ansa ta musu umarnin shigowa ,suka shigo t gansu ta Fara binsu d wani kako n mamaki Dan batasan d zuwan su ba Dan Sam mama Bata Gaya Mata ba ,shiyisa rashin mutuncin zai motsa Kuma bataga Noor ba Tana tana Bayan ussaina rikeda hannun hassana ….

Sai d kyar tace ku shigo Mana muji meke tafe daku?

Ganin b Arziki a lamarin n NAWAL , ussaina tuni t Gama kaiwa wuya Dan Haka tace cwt Noor jeki Mana magana d mama da mukazo wajenta d Alama nasan Tana ciki ….

Ganin Noor t fito tsilim a Bayan su ,sai NAWAL aka saki fara’a …..

D sauri t ware hannu ,”oh my Noor come to me” Tana murmushi ….

Ganin Noor n Shirin zuwa , ussaina tace maza Noor kimana magana d mama a hanya muke wucewa zamuyi ,Aiko Noor t fasa zuwa wajen momyn ta t wuce room din mama d gudu Tana Kiran sunan ta ….

NAWAL t kulu ,tace ke karki sake Ina magana d ‘yata kina Bata umarni Akan umarnin d na Bata ,kinfi sanin ko Wacece Ni agareta ….

Kafin hassana ta kashe zancen , ussaina tace haka dai gashi kin Bata umarni n Bata zabi ta bi nawa t aiwatar ,iko sai gidan maza wlh ,duk Wanda beji kunyar Hawa jaki b ,jaki bazeji kunyar tikashi d kasa ba ,nifa ganin laushi baya hanani tankade wlh …..

Hassana ce tace y Isa ussaina ki Bari muyi Abin d y kawo mu !

NAWAL tace batta n gurji bakin shegiya nayi maganin fitsara yarinya ,ke Naga d salama atare dake Baki manta girman mutane b sosai …..

Ussaina tace ,ahayeeee girma girma ne , ALLAH ne Mai girma …..

NAWAL tayi kanta zata mareta Dan ta Gama kaiwa wuya yarinyar d take girmamata ada yanzu itace take fada Tana mayar Mata ?

Takai hannu kenan , ussaina t rike hannu Kam! Sai ga mama t fito d fara’ar ta ,ganin hanu y kusa Mari g su ‘yan biyu a tsaye ko arzkin zama Basu samu ba ,tasan NAWAL ta Fara zubar d kimar tata gaban kannen ta …

D sauri ta k’araso tace y haka NAWAL?

Ussaina ganin mama tazo! t yarfar d tsitsiyar hannun NAWAL gefe Tana hura Mata hanci ,Tana cewa batakai Nan ba!

Mama tace NAWAL meye haka Ina tmby ki? Shirme ko shashanci har meyayi zafi d gemu zeci wuta haka kina babba a gareta?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76 77 78 79 80 81 82 83 84 85 86 87 88 89 90 91 92 93 94 95 96 97 98 99 100 101 102 103 104 105 106 107 108 109 110 111 112 113 114 115 116 117 118 119 120 121 122 123 124 125 126 127 128 129 130 131 132 133 134 135 136 137 138 139Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button