HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

_PART 1_

*PAGE 1 nd 2*

K’asar *Nairan* k’asa ce da takasance k’asa mai yalwatar arzik’i kuma k’asar ta shahara a duniya kasancewar k’asar mayu ne kad’ai suke rayuwarsu a cikinta babu bil’adam ko d’aya duk mutumin da yayi gigin zuwa garin saidai yazama gawa.

maitar tasu ta samo asaline tun kaka da kakanni, za’a iya cewa gadarta suke inda wasu kuma tasu maitar takasance ana samar masu da ita ne ta hanyar tsafi.

A tsarin garin duk jaririn da aka haifa a ranar za’a kaishi wani d’akin tsafinsu da suke kira d’akin *Dodo Gostan* inda yakasance ana ajiye jariri tsawon awa ukku a ciki indai har jariri baiyi kuka ba toh tabbas ya kasance acikin mayu wad’anda suka gaji maita.
Inko har jariri yayi kuka toh hakan yana nufin bai kasance daga cikin mayu ba dan haka shugaban matsafansu wanda yake mallakin d’akin dodonsu gostan shine zaiyi amfani da sihirinshi ta hanyar maida jaririn nan yazama maye.

Da haka ne duk wanda yataso tun kaka da kakanni yake kasancewa maye a garin hakan shine al’adarsu kuma addininsu.

Abinda zai baka mamaki halittun da ke cikin garin basu kasance mutane bane saidai sun kasance masu siffa biyu wani ‘bangaren jikinsu na mutane wani ‘bangaren kuma na wata halittar daban ammah duk da haka akwai wad’anda tawayar da ke tattare da su batada yawa saidai suna amfani da k’arfin tsafinsu wajen canza halittarsu irin yadda suke so takasance…

A garin suna da wani sarki da ake kira da Sarki Nawar, sarkin ya kasance daga cikin fararen mayu kuma sun gaji maita tun kaka da kakanni yana da dukiya me tarin yawa wadda takasance ya gada tun zamanin kakanninshi na goma sha ukku sannan masarautar garin abun kallo ce saboda anzuba dukiya wajen ginata ta k’ayatu yadda yakamata duk mulkin mutum idan da zai samu damar zuwa k’asar Nairan sai ya raina kanshi domin mulki, Sarauta, izza, k’arfin dantse duk sarkin ya had’a, duk da haka abinda zai fi baka mamaki shine sarkin yana shimfid’a mulkinshi cikin adalci wa jama’arsa.

Yana da mata biyu inda tafarkon takasance cikin bak’ak’en mayu d’iya ce ga babban bokan garin watau Boka Gobar ita kad’aice d’iyarshi tana da kyau na gani na fad’a sun had’u da sarki ne wata rana ya kawo ma boka gobar ziyara a gidanshi lokacin da yaje bai sameshi ba yana d’akin tsafinshi shine ita tafito dan tashaida ma sarki mahaifinta baya nan tun daga nan da sarki yak’yalla idanu yaganta yakamu da sonta dan haka yasanar da boka, shi kuma baiyi wata wata ba wajen amince ma shugabanshi aka sha shagalin bikki.
shekararsu goma da aure sannan suka samu haihuwar d’iya mace wadda taci suna Najma ta kasance daga cikin bak’ak’en mayu sannan ta gaji maita wajen iyayenta.

A lokacin da suke shekara ta sha d’aya da aure ne yak’ara aure inda ya auro wata kyakkyawar mata wadda a k’asar aka k’iyasta babu me kyaunta dan batada tawayar komai, saidai abinda jama’ar k’asar suka kasa ganewa inda Sarki yasamota har sukayi aure sunyi amfani da tsafi wajen ganowa ammah sun kasa gano komai kan dole suka hak’ura dan haka ne ba wanda yasan sirrin sai shi kanshi Sarki da wani malaminshi kuma abokinshi Abnar,

Abnar abokine ga Sarki Nawar tun yarintarsu sun kasance aminnan juna kamar yadda iyayensu ma haka suka kasance.

Bayan ya auro matar shi Nuwaira wadda takasance daga cikin fararen mayu tana zaune da mijinta lafiya ta kasance macece me tausayi da son jama’a, suna da shekara biyu da aure sannan tahaifi d’iyarta mace ranar da tahaifeka gabad’aya k’asar saida labarin haihuwar yakewayeta dan a tarihin k’asar Nairan ba’a ta’ba haifo yarinya me kyaun jaririyar Nuwaira ba saidai ita d’in ba fara bace sosai kamar sauran fararen mayu ba kuma zata shiga layin bak’ak’ensu ba dan tana da haskenta sosai saboda haka ne aka dangantata ga fararen mayu kamar iyayenta, koda aka kaita d’akin dodo gostan bila’adadin jama’a sukaje suka zagaye d’akin dan jin shin jaririyar zata yi kuka ko bazatayi ba.
Har tsawon awa biyu shuru batayi kuka ba ana saura dak’ik’a talatin afiddota jaririya tafara tsala kuka nan hankalin sarki yatashi sosai da d’iyarshi bata kasance daga cikin mayu wad’anda suka gaji maita ba, ammah da yayi wani tunanin sai yashare dan hakane boka gobar yai tsafi aka sa ma jaririyar maita, da haka ne akayi suna akai shagalin da ba’a ta’ba yi a garin ba inda yarinya taci suna Najla.

 

Najma da Najla sun taso basu jituwa a tsakaninsu shekaru biyu ne tsakaninsu, tun suna yara mahaifinsu yake k’ok’ari wajen ganin sun had’a kawunansu ammah hakan bai yuwu ba dan haka hankalinshi yatashi saboda yana son yaran nashi sosai duk lokacin da zaije fada tare da su yake zuwa kujerar Najma tana a gefen haggunshi inda ta Najla take a gefen dama,

Wannan rashin had’in kan nasu ya samo asali tun a wajen iyayensu mata dan dama a garin akwai k’abilanci tsakanin fararen mayu da bak’ak’en mayu wannan dalilin ne yasa Sarauniya Wailah bata k’aunar Sarauniya Nuwaira sa’banin Nuwairah da koda takasance cikin fararen mayu bata da halayyarsu ta al’adar garin.

 

A duk lokacin da zaka fito wajen garin zakaga mayu iri iri kala kala suna rayuwarsu wasu suna jifar junansu da tsafi iri iri wasu zakaga sun sauya kamanni ta hanyar komawa wata mummunan halitta, ko kaga sun shiga daji sun kamo dabbobi suna yanka suna ci, yanayin rayuwarsu kawai zaka kalla kagane cewa ba irin ta mutane bace.

Najma da Najla sun taso da mabanbanta ra’ayi Najma tun tasowarta ta kasance me ra’ayin son gado kakanta a ‘bangaren tsafi saboda haka ne tun tana yarinya batada wajen zuwa inba wajen kakanta Boka Gobar ba haka zasu zauna yadinga koya mata tsafi.

Inda Najla tataso akasin hakan saidai ita babu abinda yafi burgeta sama da taganta tare da mahaifinta ko taje wajen da mayak’an Sarki Nawar suke training tazauna tana kallonsu dan ba k’aramin burgeta hakan yake ba saboda haka ne mahaifinta yahad’ata da wani babban mayak’in garin watau barde Usbat yana koya mata fad’a na hannu da na takobi duk da wannan mahaifinta bai tsaya iya nan ba ya had’ata da abokinshi Malam Abnar yana koya mata tsafi dan daman wannan al’adar garin ce kowa sai ya kasance matsafi indai har yanaso yakasance cikin jarumai.

Lokacin da Najma da Najla suka fara girma nan kyawunsu yak’ara bayyana, musamman ma Gimbiya Najla da taciri tuta a cikin garin wajen kyau dan kyaunta yana rud’ar jama’ar garin sosai indai har zata fito toh idanun kowa kanta yake dawowa haka za ayi ta santin kyaunta saboda hakane tadinga ‘boye kanta ba kasafai tacika fitowa cikin jama’a ba,

‘Yar uwarta Najma tana bak’in ciki da wannan kyaun da ‘yar uwarta tafita saboda haka ne tafara tunanin yadda zatayi ta’bata mata fuskar da take gani kamar da ita take tak’ama…

A al’adar garin duk bayan shekaru biyar akwai shagali da fararen mayu sukeyi, suna shiga a cikin wani k’urmin daji da yake da yawan namun daji, a ranar da za’ayi shagalin duka fararen mayu zasu ci gayu kowa yasa kaya masu kyau, wad’anda zasu canza halittarsu suna sauyawa zuwa wata halittar ko kuma suk’ara ma kansu kyau.

Hakan yakasance lokacin da shekarar shagalinsu tazagayo ana saura kwana ukku suka fara shirye shiryen shagalin cike da farin ciki.

 

Sarki Nawar ne zaune a cikin makekiyar fadarshi wadda girmanta ya wuce tunanin mutum ga fadawansa kusan d’ari biyar zaune sun zagaye shi, wata kuyanga ce tashigo d’auke da wani k’aton kwando tana zuwa tafad’i gaban sarki takwashi gaisuwa duk fadawan da suke wajen ne suka amsa mata sannan cikin girmamawa tace ranka yadad’e gunki gostan yataimakeka ga sak’on da kace akawo maka ya samu.

1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button