HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Wannan rashin had’in kan nasu ya samo asali tun a wajen iyayensu mata dan dama a garin akwai k’abilanci tsakanin fararen mayu da bak’ak’en mayu wannan dalilin ne yasa Sarauniya Wailah bata k’aunar Sarauniya Nuwaira sa’banin Nuwairah da koda takasance cikin fararen mayu bata da halayyarsu ta al’adar garin.

 

A duk lokacin da zaka fito wajen garin zakaga mayu iri iri kala kala suna rayuwarsu wasu suna jifar junansu da tsafi iri iri wasu zakaga sun sauya kamanni ta hanyar komawa wata mummunan halitta, ko kaga sun shiga daji sun kamo dabbobi suna yanka suna ci, yanayin rayuwarsu kawai zaka kalla kagane cewa ba irin ta mutane bace.

Najma da Najla sun taso da mabanbanta ra’ayi Najma tun tasowarta ta kasance me ra’ayin son gado kakanta a ‘bangaren tsafi saboda haka ne tun tana yarinya batada wajen zuwa inba wajen kakanta Boka Gobar ba haka zasu zauna yadinga koya mata tsafi.

Inda Najla tataso akasin hakan saidai ita babu abinda yafi burgeta sama da taganta tare da mahaifinta ko taje wajen da mayak’an Sarki Nawar suke training tazauna tana kallonsu dan ba k’aramin burgeta hakan yake ba saboda haka ne mahaifinta yahad’ata da wani babban mayak’in garin watau barde Usbat yana koya mata fad’a na hannu da na takobi duk da wannan mahaifinta bai tsaya iya nan ba ya had’ata da abokinshi Malam Abnar yana koya mata tsafi dan daman wannan al’adar garin ce kowa sai ya kasance matsafi indai har yanaso yakasance cikin jarumai.

Lokacin da Najma da Najla suka fara girma nan kyawunsu yak’ara bayyana, musamman ma Gimbiya Najla da taciri tuta a cikin garin wajen kyau dan kyaunta yana rud’ar jama’ar garin sosai indai har zata fito toh idanun kowa kanta yake dawowa haka za ayi ta santin kyaunta saboda hakane tadinga ‘boye kanta ba kasafai tacika fitowa cikin jama’a ba,

‘Yar uwarta Najma tana bak’in ciki da wannan kyaun da ‘yar uwarta tafita saboda haka ne tafara tunanin yadda zatayi ta’bata mata fuskar da take gani kamar da ita take tak’ama…

A al’adar garin duk bayan shekaru biyar akwai shagali da fararen mayu sukeyi, suna shiga a cikin wani k’urmin daji da yake da yawan namun daji, a ranar da za’ayi shagalin duka fararen mayu zasu ci gayu kowa yasa kaya masu kyau, wad’anda zasu canza halittarsu suna sauyawa zuwa wata halittar ko kuma suk’ara ma kansu kyau.

Hakan yakasance lokacin da shekarar shagalinsu tazagayo ana saura kwana ukku suka fara shirye shiryen shagalin cike da farin ciki.

 

Sarki Nawar ne zaune a cikin makekiyar fadarshi wadda girmanta ya wuce tunanin mutum ga fadawansa kusan d’ari biyar zaune sun zagaye shi, wata kuyanga ce tashigo d’auke da wani k’aton kwando tana zuwa tafad’i gaban sarki takwashi gaisuwa duk fadawan da suke wajen ne suka amsa mata sannan cikin girmamawa tace ranka yadad’e gunki gostan yataimakeka ga sak’on da kace akawo maka ya samu.

Kallon d’aya daga cikin fadawanshi yayi nan yayi saurin bud’e mashi abinda akasa aka rufe kwandon.
Kayan adone na yakutu, lu’u lu’u zinarai da dai sauransu jinjina kai sarki yayi sannan yace aje akai ma Sarauniya Nuwaira.

Amsawa tayi da toh angama ranka yadad’e nan tasake kwasar gaisuwa sannan tad’auki kwandon cikin sauri tamik’e tafita.

 

A chan cikin gidan sarauta wanda girmanshi zai kai girman gari guda cikin gidan ‘bangare ‘bangare ne, d’aya daga cikin ‘bangaren tanufa wanda yasha ado anzuba mashi kayan k’yale k’yale sosai komai na cikinshi abun kallo ne.
K’wank’wasa wata k’ofa tayi nan k’ofar tabud’e dakanta wata kyakkyawar macece fara shimfid’e saman kujerar zinari wasu fararen halittu zagaye da ita sai hidima suke mata.

Wannan kuyangar saurin zubewa tayi k’asa tace Allah yataimake ki Sarauniya sak’o daga Sarki.
‘Daya daga cikin kuyangita ne tazo ta amshi kwandon taje gaban Sarauniya Nuwaira ta ajiye sannan tabud’e mata.

Murmushi Sarauniya Nuwaira tayi tace ashiga da su ciki.

Tun kan tarufe baki wannan bafadiyar tata tad’auka cikin sauri ta yi cikin wani d’aki da shi…..

 

Tunda tadoso kanta a cikin gidan sarautar jama’ar ciki suka fara zubewa suna k’wasar gaisuwa ammah babu wanda takalla daga cikinsu haka tawuce cikin takunta me jan hankali, da idanu suka bita suna yabon kyawunta da zubin halittarta dan komai nata na daban ne kamar mahaifiyarta.

Hanyar ‘bangarenta tanufa tana cikin tafiya sai ji tayi daga bayanta ankira sunanta.
Ja tayi tatsaya dan ko bata juya ba ta san me kiran nata, tana nan tsaye wasu bak’ak’en kuyangi suka fara isowa wajen sai a lokacin tad’aga kai takallesu su dukansu duk’ar da kai sukayi alamun girmamawa.
Wata kyakkyawar budurwace bak’a sanye cikin kaya na alfarma ta iso wajen tare da sauran kuyanginta, kallonta Najla tayi nan Najma tasakar mata murmushi tace me kika shirya ma gobe da takasance ranar farin ciki agaraku fararen mayu?
Tsayawa tayi kallonta dan yanayin yadda tayi magana yasa Najla tagane akwai wani abu acikin zuciyar Najma dan ko murmushinta kagani toh tabbas na mugunta ne.
‘Daga mata gira Najma tayi tace kinyi shuru ya kamata kice min wani abu ya ke kyakkyawar farar mayya.
Sai a lokacin itama Najla tayi murmushi sannan tabud’e baki cikin siririyar muryarta me dad’in saurare tace abinda nashirya ba lallai bane kowa yasanshi musamman ma bak’ak’en mayu da basu da hurumi a cikin shagalinmu

Bushewa da dariya Najma tayi tace dakyau Najla ina son irin wannan jarumtar taki da rashin tsoro hakan yana burgeni sosai.
Murmushi kawai Najla tayi batare da ta ce mata komai ba tawuce tayi tafiyarta.

Da idanu Najma tabita tana murmushin mugunta har saida Najla ta’bulle sannan tata’ba hannunta nan Najma ta’bace ‘bat
Kuyanginta suna ganin haka nan suma duk suka ‘bace…..

 

Gimbiya Najla Cikin tafiyarta me jan hankali ta isa wajen wata k’ofa me siffar d’awisu wadda aka k’awatata da zinarai tana zuwa wajen k’ofar nan gashin da ke jikin d’awisun yabud’e sai ga wani had’ed’d’en parlor ya baiyana.
Taka lumtsumemen kafet d’in da ke shimfid’e daga farkon parlorn tayi sai ga wasu mata su kusan ishirin sun bayyana a zaune k’asa suna sanye da kaya iri d’aya duk sun duk’ar da kai alamun girmamawa.

Cike da nuna isa take tako nan tawuce tatsakiyar parlorn tanufi wata babbar k’ofa da wasu fararen kuyangi biyu suke tsaye suna gadi ganinta yasa duk suka zube sukayi mata sujjada, batare da ta ce komai ba tawuce tashiga cikin had’ed’en bedroom d’inta da yaji kayan alatu komai na ciki an k’awatashi da lu’u lu’u da gold, kayan jikinta tacire tafad’a cikin wani toilet wanda shima tsarinshi abun kallo ne tana shiga tafad’a cikin wani bathtube me kama da swimming pool nan wasu halitta masu kama da agwagi sukazo suka fara wanke mata jiki, kwance tayi cikin ruwan tare da maida idanunta tarufe ahaka suka dinga cud’ata saida suka wanketa tas sannan tafito daga cikin ruwan.

Shiryawa tayi cikin wata had’ad’d’ar gown wadda tabaje tana sharar k’asa, wasu ‘yanmata ne guda biyu suka bayyana a gefenta suka ce ranki yadad’e ko kina buk’atar taimakonmu

Girgiza masu kai kawai tayi nan tahad’e dogon gashinta waje guda tad’aure sannan tafito parlor cike da tak’ama take tafiya bisa kujerarta ta zinari tazauna nan tabada umurni gabad’aya halittun da suke cikin parlorn suka ‘bace sai wasu kuyangi biyu da suke tsaye suna tsaron k’ofa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button