HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Zoben da yake manne a hannunta tafara murzawa nan wani haske yafito daga jikinshi daidai lokacin aka fara knocking d’in k’ofa wad’annan kuyangin da suke tsaye suka bud’e.

Wata hadima ce tashigo d’auke da wani k’aton tray tana zuwa d’an rissinawa tayi a gaban Gimbiya Najla sannan ta ajiye tray d’in tare da saurin duk’awa tafara k’wasar gaisuwa, kallonta kawai tayi batare da tayi magana ba nan baiwar tatashi tabud’e tray d’in da tashigo da shi, nama ne iri iri jibge a cikinshi, bin tray d’in tayi da kallo tace wannan naman duk na minene?

Baiwar cikin rawar murya tace ranki yadad’e sarauniya ce tabada umurni inkawo maki.
Jawo gashin kan baiwar tayi dak’arfi wanda dalilin hakan yasa saida baiwar tasaki k’ara, tura kanta tayi cikin tray d’in naman tace meyasa kika kawo min wannan bayan kinsan bana cin irinsu.
Cikin rawar murya tace kiyi min rai ranki yadad’e wallahi ba’ason raina nakawo maki su ba.

‘Dan guntun murmushi tayi tare da sakar mata kai tace na san ko aikin wanene wannan, yanzu ya zama dole kifita da wannan naman kije kikawo min irin wanda nake buk’ata.

Cikin sauri tad’auki tray d’in taficce, mik’ewa gimbiya najla tayi tashige fankacecen bedroom d’inta da yasha kayan alatu kamar ba a duniyar ba.

 

Washe gari haka ake ta shirye shirye gabad’aya garin Nairan hidima suke musamman ma idan akace dare ne dan daman indai dare ya yi mawuyacine kaga suna bacci lokacin ne mafi yawan mayun garin suke fita farauta cikin daji da safe zuwa lokacin da rana zata yi sanyi ne suke samu suyi bacci dan mafi yawansu basu cika fita in akwai rana ba musamman fararen mayu tana masu illa sosai.

A yau ko kamar sallar ko ma ace sallarsu ce kowa ya zage wajen shirya kanshi masu canza kamanni suna yi masu maida kansu siffa mekyau suna yi duk dan kowa yaga ya fi kyau.

Duk wannan hidimar da ake banda Gimbiya Najla dan ita daman chan wannan shagalin baya burgeta.

 

***** ****
Sarauniya Nuwairah tafe take kuyanginta suna take mata baya duk inda suka ratsa mayu ne suke zubewa suna kwasar gaisuwa saidai tabisu da murmushi ahaka suka isa ‘bangaren Sarki Nawar suna zuwa wajen k’ofa gabad’aya masu tsaron k’ofar da kimaninsu ya kai su talatin suka duk’a suka kwashi gaisuwa sannan aka bud’e mata k’ofa, kuyanginta a nan suka ja suka tsaya inda ita kuma tashiga ciki, tana shiga tasamu wata bak’ar kuyanga tsaye a bakin k’ofa hakan yasa tagane Sarauniya Wailah tana ciki, kuyangar saurin duk’awa tayi tagaisheta nan Sarauniya ta amsa sannan tawuce bisa d’aya daga cikin k’ayatattun kujerun Gold da suka k’ara k’awata parlon tazauna.

Tana zama bata dad’eba sai ga Sarauniya Wailah ta fito daga cikin bedroom d’inshi saurin mik’ewa Nuwairah tayi tare da sakar mata murmushi.
Ko inda take Sarauniya Wailah bata kalla ba tawuce tatafi da idanu Nuwairah tabita har lokacin fuskarnan tata tana shimfid’e da murmushinta me k’ara k’awatar da kyawun fuskarta sannan tajuya tanufi cikin bedroom d’in mijin nata.

Tana shiga tasameshi tsaye a gaban k’aton madubin da yaci ado da ruwan diamond ya cire rigarshi yana duba wasu abubuwa masu kama da k’ayoyi a bayanshi yana ganinta yayi saurin takowa ya iso wajen da take yana zuwa yarik’o hannunta yazaunar da ita saman gado sannan yatallabo fuskarta yana kallo yace ya ke kyakkyawar matata shin ko zani iya sanin dalilin shiga damuwarki?

K’ok’arin ‘boye damuwarta tayi sannan tace Ya kai mijina inason kasan cewa na shiga damuwa ne ba dan komai ba sai dan ina ji a raina kamar akwai abinda zai faru da rayuwata.

Wata irin razanannar k’ara sarki yasaki tare da saurin latsa zoben da yake a babban yatsan hannunshi nan wani abu me kama da computer yabayyana a gabanshi, rufe idanunshi yayi yafara karanto wasu d’alasimai da ita kanta Gimbiya Nuwaira batasan abinda yake cewa ba saida yad’au lokaci me tsawo yana karantowa sannan yabud’e idanunshi yasafkesu akan ‘yar computer sihirinshi ajiyar zuciya yasafke tare da kallon Gimbiya Nuwairah yayi murmushi sannan yace kikwantar da hankalinki babu abinda zai faru da rayuwarki dan akwatin tsafina bai gwada min komai ba bazan ta’ba bari wani abu yafaru da ke ba ya ke matata.

Murmushi tayi ganin yadda hankalin mijin nata yatashi yasa tace hakane mijina nima kawai raina ne yaban haka ammah nasan babu abinda zai faru da ni, saidai ko da ma wani abun ya faru da rayuwata ina so kakular min da Najla sosai dan kaine kad’ai wanda zata cigaba da samun gata a wajen….
Katseta yayi yace haba Nuwaira kidaina cewa haka zamu cigaba da rayuwa tare sannan Najla zata samu kulawa daga dukkan ‘bangarorin namu guda biyu.

K’wallah ce tacika mata idanu tace nasan haka mune kad’ai farin cikinta ina bak’in ciki akan wannan rayuwar da mutanen garin nan suke ta k’abilancin da ke tsakanin Fararen mayu da bak’ak’en mayu wanda ta dalilin hakan Saraunya Wailah da Najma suke nisantar da kansu daga garemu shin idan rai ya yi halinshi ya Najla zatayi da kewa babu wanda zai tallafa mata.
Ajiyar zuciya yasafke yace Nuwairah kidaina irin wannan maganar dan tana d’aga min hankali sosai babu abinda zai faru da mu sannan ita Najla bana da matsala da ita na san cewa zata kula da kanta ko da ace bamu raye.

Murmushi Sarauniya Nuwairah tayi sannan taciro wani zoben gold me kyau sosai daga dogon yatsan hannunta rik’o hannunshi tayi tasaka mashi zoben a tafin hannu sannan tarufe hannun tana murmushi tace ga wannan ka ajiyeshi ina da burin ganin Najla ta mallakeshi kamar yadda nima namallaka bana so ya’bace a wajena saisa nabaka shi ka ajiye wajenka.

Jin abinda tace yasa hankalin Sarki Nawar yakwanta nan ya amshi zoben yace zan ajiyeshi kamar yadda kika buk’ata har zuwa ranar da zaki nemeshi daga wajena.

Murmushi tasakar mashi tare da cewa nagode Ranka yadad’e,,, tana fad’in haka tamik’e tsaye tare da d’an rissinawa k’asa alamun girmamawa.

Jinjina kai yayi nan tajuya tafita tabar d’akin da kallo yabita yana murmushi har saida tafita sannan yamaida idanunshi akan zoben yana kallonshi,,,,, tunowa yayi wani lokaci da mahaifinshi Sarki Zabban zai mutu shi yamallaka mashi shi yace ya adanashi kar yasaki yabari zoben yasalwanta daga wajenshi har sai lokacin da yayi aure ya auri d’aya daga cikin jinsu na fararen mayu sannan zai mallaka mata shi wannan dalilin ne yasa yamallaka shi ga Gimbiya Nuwairah matarshi ta biyu, ajiyar zuciya yasafke a fili yace minene dalilin Nuwairah na bani wannan zoben tace inba Najla bayan ita namallaka ma shi? Ko dai akwai abinda yake shirin faruwa da ita?
Saurin girgiza kai yayi yace a’a babu abinda zai faru da ita saidai idan itace take tunanin hakan…..

Mik’ewa yayi yaje yayi ma zoben kyakkyawan ajiya sannan yasaka kayanshi na sarauta yafita yanufi fada.

 

da dare ko da Sarauniya Nuwairah taje apartment d’in d’iyarta ganin duk ranar bataga giccinta ba duk hidimar da ake banda ita koda tasan Gimbiya Najla bata cika son shiga cikin taron jama’a ba ta fi so take’be kanta.

tana zuwa d’akinta tasameta kwance baccinta kawai take abun ya bata mamaki sosai nan ta ajiye kayan da takawo mata saman gadon sannan tashiga tadata ahankali tabud’e idanunta takalleta,  murmushi tasakar mata tace ‘yata ya kamata kitashi kishirya kinga lokacin tafiyar mu wajen shagalin bikkin ya kusa ga kaya nan na kawo maki wanda nasa aka k’era maki da lu’u lu’u dan ina so shigarki tafi ta kowa kamar yadda kika zarce kowa wajen kyau.
Murmushi Gimbiya Nalja tayi sannan tace toh ummah.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button