HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Idanu Gimbiya Nuwairaj tazuba ma kyakkyawar ‘yar tata tana kallo daidai lokacin hawaye suka gangaro daga idanun sarauniya nan hankalin Najla yatashi sosai tayi saurin tashi zaune tare da rik’o hannun mahaifiyartata tace Ummana lafiya kike hawaye ina fata dai ba wani ne ya’bata maki a garin nan ba?
Girgiza kai tayi tare da goge hawayen ta tace ko d’aya ya ke ‘yata ina jine a jikina kamar akwai abinda zai faru da rayuwata a wannan ranar.

Wata k’ara Najla tasaki wadda tasa saida d’akin ya amsa cikin d’aga murya tace babu abinda ya isa yasameki ummana ni kariya ce a gareki duk fad’in garin nan duk wanda yanemi yata’ba min ke sai na shayar da karnuka na jininshi zan iya ja dakowa a kanki.

Murmushi Sarauniya tasaki tare da shafa kan d’iyar tata cikin jin dad’in kalamanta tace babu abinda zai sameni na sani d’iyata kawai dai a jikina ne nakejin haka.
Ajiyar zuciya gimbiya Najla tasafke tace hakane ummana kidaina zubar da hawayenki aduk lokacin da kikayi tunanin wani abu zai sameki kiyi tunanin ina nan ni kariya ce agareki.

Murmushi Sarauniya tayi tana kallon d’iyartata cike da jin tausayinta chan sai tamik’e tace bari inje in ida shiri kitabbatar kin shirya kafin lokacin tafiyar.
Murmushi Najla tayi tace toh Ummana kar kidamu zan shirya saidai muhad’e chan kar kujirani.

Sarauniya tace toh shikenan Gimbiyata duk yadda kikeso haka za’ayi zan sanar ma mahaifinki abinda kikace.

Murmushi Najla tayi a karo na biyu, sarauniya har ta juya zata fita sai kuma tasake juyowa takalli Najla sannan tajuya tafita.

 

Najla na ganin ta fita tad’auko kayan da mahaifiyartata takawo mata takalla tayi murmushi tabbas ta san mahaifiyarta ta yi namijin k’ok’ari wajen tanadar mata kayan,  murmushi tasaki ahankali tace ina k’aunarki sosai Ummana nan ta ajiye kayan takoma takwanta tacigaba da baccinta.

 

Wajen k’arfe sha biyun dare dajin Sanzar da suke kira bak’in daji cika yayi mak’il da fararen mayu kowa kagani ya ci ado cikin kaya mafi kyau da tsada a tsakiyar dajin suka kunna wuta wadda saboda cinta saida tahaske dajin su dukansu zagayeta sukayi wasu na bin bayan wasu nan babban malaminsu na fararen mayu Boka Ambar yasa aka yanke k’atuwar shanuwa aka tsiyaye jininta a cikin wani k’aton bokitin tsafi sannan aka cillata cikin wutar wata irin k’ara wutar tayi nan tak’ara tururuwa daidai lokacin Sarki Nawar da Saraujiya Nuwairah suka tunkaro wajen nan gabad’aya jama’ar fararen mayu suka duk’a sukayi sujjada banda Boka Ambar da yaruntse idanunshi yana karanta wasu d’alasimai takowa sukayi suka iso wajen da yake nan suka tsaya gefenshi tare da runtse idanunsu har lokacin sauran jama’a basu d’ago daga sujjadar da sukayi ba, ahankali Boka Ambar yabud’e idanunshi yad’auki wannan bokiti me cike da jinin shanuwa da yatsafe nan yamatsa wajen da sarki Nawar yake tsaye ya ajiye bokin bud’e idanu Sarki Nnwar yayi yasaka hannuwanshi cikin jinin ya yi kusan minti ukku sannan yafiddo hannuwan yashafa jinin a saman kanshi sannan yajuyo yashafa ma Sarauniya Nuwaira ita a gashinta, bud’e idanunta tayi ahankali tasakar mashi murmushi, maida mata martani yayi yace ina Najla ya akayi har wannan lokacin bata zo ba?
Saurin juyawa Gimbiya Nuwairah tayi takalli bayanta sannan tace bansan dalili ba bansan me yasa har yanzu bata zo ba munyi da ita zata zo ta ce kar mu jirata ita kad’ai zata zo.
Jinjina kai Sarki Nawar yayi yace ammah kuma har yanzu shuru meyasa Najla zatayi mana haka.

Boka Ambar ne yace ya shugabana Najla ta aikata zunubi ya kamata kufansheta da wani abun yanka mafi girma dan Gunki Gostan yagaugauta yafe mata.

Sarki ne yayi saurin cewa na fansheta da manyan shanu guda ukku.

Jinjina kai Boka Ambar yayi sannan yad’auki bokitin jinin yawatsa shi a bayansu inda sauran jama’a sukayi sujjada ahankali suka d’ago kansu tare da shafa gashin kansu sannan suka mik’e tsaye, wasu halittu masu kama da doduna ne suka fiddo manyan ganguna suka fara kad’awa nan aka fara rera wak’a kowa yana kai hannunshi wajen wuta yana d’an ta’bawa sannan yajanye hannun cikin sauri suna cikin haka dajin ya amsa da wata irin k’ara me kama da kukan hadari nan take gabad’ayansu suka zube k’asa sukayi sujjada, k’asa ce tafara girgiza duk sai kowa yayi tsit, walkiya tafara haskawa lokaci guda wutar tamutu duk sai suka d’ago kansu ahankali hayak’ine yakauraye dajin a tsakiyar inda suka kunna wutar sukaga wani Dodo k’ato fari fat da shi da ka ganshi kamanninshi irin na tsohon biri ne abun tsoro zaune yake bisa wata kujera gashi duk ya baje mashi fuska, in ba ka saba ganinshi ba idan ka hangeshi daga nesa sai ka sume..
A karo na biyu suka sake duk’awa sukai sujjada sannan Boka Ambar yamik’e tsaye yafara kirari yana cewa muna mik’o gaisuwa ya shugaban fararen mayu, rayuwarmu fansace agareka ya kai shugaba Dodo Farras a yau ne shekaru biyar suka cika shekarun da muke sadaukar da rayuwar d’aya daga cikin fararen mayu gareka dan samun kusanci da kai shugaban Fararen mayu wanda muka gaji hakan tun kaka da kakanni.

Wannan dodon numfashi kawai yake safkewa yana bin jama’ar da sukayi sujjada da kallo yana bud’e hanci, Boka Ambar saurin zubewa yayi saman gwiwoyinshi tare da runtse idanunshi, wata irin murya sukaji wadda tasa gabad’ayansu saida suka firgita saboda k’arfi da k’ararta gabad’aya dajin saida ya amsa…..
Na ji dad’in zagayowar wannan ranar a yanzu zan gabatar da takobina agareku duk inda yatsaya ya zama dole abani d’aya daga cikin dangin wanda tatsaya wajenshi kunsan haka al’adar take idan har kuna son cigabanku da samun d’aukakarku da ta jikokinku fararen mayu a cikin garin Nairan.

Su dukansu amsawa sukayi da mun yarda da haka ya shugabanmu mu masu biyayya ne agareka.

Hannunshi yad’aga sama sai ga wata farar takobi tazinari ta bayyana a hannunshi runtse idanunshi yayi yafara karanto wasu d’alasimai nan gabad’aya jamar wajen suka mik’e tsaye kowa yayanki gefe guda yatsaya shi kad’ai tare da runtse idanunsu.

Sunyi kusan awa d’aya a haka sannan suka fara jin motsi kamar na tafitar ingarmar doki, ahankali yasaki takobin hannunshi nan tafara tafiya saman iska tatunkaro wajen da dubban jama’ar suke tsaye mata da maza yara da k’ananu bin tagabansu tadinga yi d’aya bayan d’aya saida tazagaye gabad’ayansu sannan a karo na biyu tatunkaro wajen da su sarki Nawar suke tsaye tana zuwa sai jin k’arar fad’uwarta sukayi k’asa dak’arfi nan gabad’aya kowa yabud’e idanunshi dan ganin inda wuk’ar tafad’a sai ganinta sukayi a gaban Sarauniya Nuwaira, duk wani mahaluk’i da yake wajen sai da yafirgita dan hakan bai ta’ba faruwa ga sarki ba sai wannan karon, shi kanshi Sarki Nawar zufa ce tafara kwarara a jikinshi yana kallon Sarauniya Nuwairah da tayi mutuwar tsaye, muryar Dodon sukaji yana cewa maraba gareki ya ke takobina a yau kin taki babbar sa’a dan kin fad’a a babban gida mafi girma da daraja a cikin garin Nairan, ya kai Sarki Nawar a yau gidanka nabak’unta dafatan zakayi farin ciki da wannan bak’uncin nawa albarkata tacigaba da yad’uwa a cikin gidanka dan haka ya zama dole kabada d’aya daga cikin iyalanka jinsin fararen mayu inyi romo da kansu insha jininsu dan samun albarkata.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button