KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Jikin Sarki Nawar rawa yafara yi nan da nan tsoro yad’arsu a ranshi dan ko kad’an bai ta’ba tunanin hakan zai faru a cikin iyalansa ba kallon Gmbiya Nuwairah yayi da itama take kallonshi hawaye sun wanke mata fuska, gabad’aya jama’ar wajen tsit sukayi dan abun ya basu mamaki sosai.
Sarki Nawar maida kallonshi yayi ga Dodo Farras cikin sauri yazube k’asa yayi sujja cike da girmamawa yace ya shugabana ina neman alfarma a wajen……wata irin gigitacciyar k’ara suka ji anyi cikin murya me ban tsoro akace babu neman alfarma a duk lokacin da muka buk’aci rayuwar mutum d’aya daga kowace zuri’a bayan kowane shekaru biyar wannan babban kuskure ne agareka ka san sharud’d’an mu ya zama dole abamu indai har anason cigaba da rayuwa inko ba haka ba zamu k’wata ta k’arfin tsiya yanzu za’bi ya rage gareka kabamu ‘yarka ko matarka.
Nan hankalin Sarki Nawar ya ida tashi cikin sauri yad’ago kanshi gabad’aya yama rasa ya zaiyi, muryar yaji a karo na biyu ance dak’ik’u kad’an suka rage maka inba haka ba mu zamu za’ba da kanmu.
Gimbiya Nuwairah tana jin haka tayi saurin rik’o mijin nata hawaye suna cigaba da wanke mata fuska tace ya kai mijina wannan itace ranar da nake ce maka na san bazan cigaba da rayuwa ba ni zan je dan Allah kakular min da d’iyata sosai dan Najla itace rayuwarmu daga ni har kai.
Saurin girgiza kai yayi yace a’a Nuwairah hakan ba zai yuwu ba kibarni ni na za’bi inmutu ku kuma kuje kucigaba da rayuwa ke da Najla dan bana son in rasaku ina k’aunarku sosai.
Murmushi tayi tace shin ka amince kasa’ba ma al’adar da aka gada tun kaka da kakanni dan kawai saboda mu? Baka tsoron abinda zai biyo ba? Kai fa sarkine kuma jama’a na buk’atar cigaba da zama da kai nidai dan Allah kakular min da ‘yata kar kamance itace rayuwarmu zamu iya sadaukar da komai saboda ita miyasa bazaka bari intafiba bayan ka san umurnine daga shugabanmu abun bautar mu.
Shuru sarki Nawar yayi yana sauraren matar tashi nan wata irin tsawa tafara tashi wani rami ne yabayyana a chan wajen da Dodo Farras ya’bace murya ce suka jiyo daga cikin ramin ana cewa lokaci yana k’ure maka ya kai sarki Nawar!!!…….
_*Part 1 Free pages ne*_
_Gareku masoya Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAWUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA…*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 5*
…Gimbiya Najma tana ganin ta fita tafasa wata irin razanannar k’ara tadafe kai tace na shiga ukku Didi kin gane min zoben da yake hannun Najla?
Rik’ota tayi tace Najma menene abun tashin hankali toh?
Cikin d’aga murya tace dole intashi hankalina Didi meyasa Abba zai mallaka mata shi? Me hakan yake nufi kenan ita Abba yamallaka ma zoben nan?
Rungumeta Sarauniya Wailah tayi tana jin zuciyarta tana tafarfasa cikin ranta tana bak’in cikin abinda mijinta ya aikata watau kenan ya fifita Najla akan Najma kamar yadda yafifita Nuwairah akanta yafake da sunan dole sai wadda tafito daga cikin jinsin su na fararen mayu bayan ta sa mahaifinta Boka Gobar ya mata bincike akan zoben ya tabbatar mata da ace Sarki Nawar zai mallaka mata zoben da Sarautar masarautar Nairan zata iya dawowa a hannunsu,,, ajiyar zuciya tasafke tace kinga Najma kidaina tada hankalinki ya zama dole kiyi amfani da k’arfin tsafinki wajen ganin kin mallaki zoben nan idan har bakiyi wannan k’ok’arin ba toh tabbas bazaki ta’ba mallakar masarautar Nairan ba.
Gimbiya Najma wucewa tayi cikin sauri tanufi hanyar turakarta cikin ranta tana tunanin yadda zatayi taraba Najla da wannan zoben, directly d’akin tsafinta tawuce tazauna tana cewa ya zama dole inrabaki da shi Najla domin barinki da shi tamkar yana nufin kece zaki mallaki masarautar nan bayan mutuwar sarki, wurgi tafara yi da kayan tana cewa hakan ba zan ta’ba bari yafaru ba indai ina numfashi nice kad’ai yadace inmallaki k’asar nan..
Gimbiya Najla tana barin turakar Sarauniya Wailah tawuce sabuwar turakarta a chan ne tatarar da kuyanginta sun kai mata duk wasu kaya nata da suka san zata nema cikin sauri tashige bedroom tamaida tarufe, saman gadonta tafad’a nan tafara rusa kuka duk tausayin kanta yakamata ahankali tafara cewa yanzu shikenan su Najma bazasu ta’ba kusantar da kansu da ni ba? Mahaifina shine kad’ai zai cigaba da kasancewa tare da ni? Toh ammah ina dangin mahaifiyata tunda ya ce shi baida dangi shine kad’ai yarage a cikin zuri’arsu sai kuma mu da yahaifa, shuru tayi kamar me son tuno wani abu sai kuma takasa daidai lokacin aka fara yi mata knocking d’in k’ofa mik’ewa tayi tashige cikin toilet a gaban madubi tatsaya tana k’are ma fuskarta kallo sai kuma chan takunna ruwa tafara wanke fuskar…
Tana gamawa fitowa tayi tanufi k’ofa tabud’e nan tasamu masu yi mata hidima sun kawo mata nama da kayan marmari iri iri saman kujerar zinari tazauna tana bin manyan tiren da aka ajiye mata da kallo, d’aya daga cikin masu yi mata hidima ce tace ranki yadad’e Sarki ne yabada umurni akawo maki kowane kalar nau’in nama daga ciki har da na mutum da yasa aka gasa maki…
Tufa guda d’aya tad’auka tafara ci sannan tayi nuni da hannunta da afitar mata da sauran tire d’in, sharmiza ce taduk’ar da kanta tace ranki yadad’e idan wad’annan basuyi maki ba zaki iya bamu dama musamo maki irin naman da kikeso inkuma jinin mutum kike buk’atar sha wannan ba wani abu bane zamu iya zuwa musamo maki umurninki kawai muke jira.
Shuru Najla tayi tana cigaba da cin tufarta ganin yadda tanuna kamar batasan suna yi ba yasa duk suka ja bakinsu sukayi shuru.
Gimbiya Najma zaune take acikin d’akin tsafinta tana ta faman had’a abubuwan mugunta wanda zata jefi Najla da su ta hanyar sihiri da ta fara had’a wanchan ta tura sai taga kafin ya isa wajen Najla wani haske ya tare tsafin, mamakine yakamata tarasa ya akayi, haka ta jefi Najla da tsafi iri-iri sunyi kala goma ammah babu wanda ya isa a wajen Najla da ke zaune tana cin tufa dafe kai Najma tayi cikin fusata tace wanene yake k’ok’arin ‘bata min aiki haka alhalin na san Najla bata da k’arfin tsafi kamar nawa ya zama dole insan kowanene yake min wannan karambanin inko har nasanshi bazan ta’ba barinshi ba,,, wata dabara ce tafad’o mata nan tazuba ma tufar da ke hannun Najla idanu tana murmushi chan tajuya tad’akko wani d’an k’aramin tsinke me tsini rufeshi tayi a cikin tafin hannuwanta tare da runtse idanunta tana motsa baki alamun akwai abinda take karantowa chan kuma tabud’e idanun tasaki tsinken ya’bace, idanu tazuba ma madubin tsafinta bakinta d’auke da murmushin mugunta tana kallon Najla da har lokacin take zaune tana cin tufar….