KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

A chan ‘bangaren Najla bayan ta had’iye tufar da ke cikin bakinta har ta kai baki zata k’ara ‘ballar wata sai kuma tafasa tsayawa tayi tana kallon sauran tufar da take hannunta chan kuma tayi murmushi ta ajiye sannan tamik’e tashige bedroom d’inta
Wata irin k’ara Najma tasaki cikin ‘bacin rai tace idan kinsan wata baki san wata ba Najla ya zama dole inga bayanki ta kowace hanya sai na yi nasara akanki kirubuta ki ajiye wannan,,, wurgi tayi da kayan tsafinta tamik’e cikin fushi tafita daga cikin d’akin tsafin, tana fita wata bak’ar kuyanga ta iso wajen da take tace ranki yadad’e daman Sarauniya ce ta……bata ida fad’in abinda yake bakint ba Gimbiya Najma tashak’i wuyanta dak’arfi tabuga mata kai da bango nan take bak’in jini yafara kwarara nan tawuce tabarta a kwance tana ta shure-shure…
**** **** ****
Bayan kwana biyu Najla taji zaman duk ya isheta nan takira amintacciyar kuyangarta mayya Hasisa tasanar da ita tanaso tashirya mata kuyangi sufita yawon bud’e ido a cikin garinsu dan dama ita d’in ba mai yawan fita ba.
Duk’awa Hasisa tayi tace angama ranki yadad’e sannan tamik’e cikin sauri tafita..
Najla tashi tayi takoma bedroom d’inta tayi wanka tashirya cikin wata riga me zanen d’awisu wadda tabaje k’asa, gyara gashin kanta tayi yana ta k’yalli sannan tafito duk wanda yaganta sai ya duk’a ya sara mata tare da mik’a gaisuwa saboda tsananin kyaun da tayi bata damu da irin kallon da ake mata ba tawuce fada wajen mahaifinta tana shiga tatarar lokacin ana tsaka da fadanci fadawan da suka fara zubewa suna kwasar gaisuwa ne yasa sarki ya ankara da shigowarta fuskarta d’auke da murmushi tanufi wajen mahaifin nata shima a nashi ‘bangaren murmushin yake har ta iso wajenshi nan tad’an rissina alamun mik’a gaisuwa
Jinjina kai yayi sannan yace Dodo Gostan ya albarkaceki kyakkyawar ‘yata shin ko akwai abinda kike buk’ata ne daga mahaifin naki?.
Bakinta d’auke da murmushi tace ya kai Abbana na zo ne dan in sanar da kai a yau ina cikin yanayi na son fita yawon shak’atawa wannan dalilin ne yasa nayanke shawara zan fita inzagaya gari.
Wannan ba matsala bane ya ke kyakkyawar ‘yata zan had’aki da dakaru dubu wad’anda zasu kula da lafiyarki har kije kidawo.
Girgiza kai tayi tace a’a Abba bana buk’atar su zan je tare da kuyangi na.
Jimm yayi sai kuma chan yace Najla hankalina zai fi kwanciya idan kina a k’ark’ashin dakaruna majiya k’arfi
Shafa fuskarshi tayi tace Abbana kar kadamu ni zan kula da kaina na yi maka alk’awali zan je indawo lafiya lau batare da wani abu ya sameni ba kayarda da hakan ya kai Abbana.
Ajiyar zuciya Sarki Nawar yasafke sannan yace shikenan kyakkyawar ‘yata kije na amince dan farin cikinki shi nafi buk’ata
Duk’awa tayi tasumbaci goshin shi sannan tajuya tafita daga fadar, saman wani ingarman doki tahau wasu daga cikin kuyanginta suka tashi saman iska sukayi mata inuwa wasu kuma suka tsaya gefenta da gabanta dan kare lafiyarta ahaka suka fita gari duk inda tagifta idanu ne ke kallonta inda jama’a dayawa daga jinsinsu na mayu suka dinga sha’awar ina ma ace susameta, halittu iri iri duk inda tawuce sai sun yaba ma kyaunta ahaka har suka shiga cikin kasuwa tana kallon yadda mayu suke cinikayya daga ciki har da mutane da aka kamo ana siyarwa ga me buk’atar yin romo da su ko shan jininsu, ga kuma zuciya da kayan cikin mutane an fed’e ana siyarwa wasu daga cikin mayun suna siya suna ci, ja tayi tatsaya a daidai inda taga wasu mutane ad’aure ana cinikinsu, Hasisa da take gefenta tana ganin ta ja ta tsaya tace ya Shugabata shin ko kina buk’atar wasu daga ciki asiya maki?
Girgiza kai tayi batare da ta janye idanunta akan mutanen ba tace Hasisa kin fi kowa sanin ba kowane irin nama nake ci ba, .
Hakane ranki yadad’e nasan hakan kigafarceni shafa’a nayi,
Maida kallonta tayi ga Hasisa tace ammah a ina ake samo wad’annan mutanen bayan tsakaninmu da inda mutane suke akwai tafiya me nisa?
Murmushi Hasisa tayi tace Ranki yadad’e kinsan anan kusa da mu akwai wata k’asa da ake kira *Shira* tafiyar wata biyu ce a tsakaninmu a chan mutane ne suke rayuwa a cikinta a satin da yagabata ne wasu majiya k’arfi daga cikin jama’armu na Mayu suka afka ma garin sun kamo wasu inda a chan kuma suka sha jinin wasu suka lashe wasunsu…
Cize le’be Najla tayi batare da ta ida saurare ba tawuce tayi gaba nan kuyanginta suka cigaba da binta…
Zagaya kasuwar tayi duk abinda taga ya burgeta tana sawa asiya mata ahaka har saida rana takusan fitowa sannan suka koma gida inda sauran mayun kowa yadinga k’ok’arin guduwa yakoma gidanshi gudun kar rana ta iskesu dan sun san muddin tatarar da su a nan toh saidai wasu ba dai su ba…..
___________
Sharmiza ce tsaye a bayan turakar Najla wajen wasu furani tana tsinka sai ga wata bak’ar tsohuwar mayya a dudduk’e ta tunkaro wajen tana zuwa tatsaya kusa da Sharmiza tace ya ke k’awata hak’ik’a ganinki ya min wuya kwanaki dayawa bamu samu mun had’uba
Juyowa tsohuwa Sharmiza tayi takalleta fuska d’auke da murmushi tace hakane Tsohuwa Umzab mun kwana biyu bamu had’uba kin fara min nisa bakison zuwa wajen da nake bayan tun muna k’anana muke tare a cikin gidan nan ammah a yanzu kina gudun kizo wajen da nake kuma nasan hakan yana da nasaba da halin da uwargijiyarki da ‘yarta suke nunawa na k’abilanci tsakaninsu da fararen mayu..
Cikin kod’ad’d’ar muryarta tace a’a Sharmiza kar kice haka ayyuka ne sukayi min yawa ammah da ba haka ba ai zaki dinga ganina…
Murmushi tsohuwa Sharmiza tayi tajuya tacigaba da tsinkar furen da take
Tsohuwa Umzab gyaran murya tayi tace yauwa ina ta so in tambayeki naga kamar angyara ‘bangaren Sarauniya Nuwairah alhali bata raye shin ko Sarki yana shirin yo amarya yasaka ne, kinsan a yanzu ba komai nake sani a cikin gidan sarautar nan ba
Murmushi Sharmiza tayi tace kod’aya ba haka bane Gimbiya Najla aka gyara ma shi itace a ciki yanzu, ya canza mata komai ya zuba mata sabo
Katseta Umzab tayi tace idan babu damuwa ko zaki iya min jagora inshiga ingane ma idanuna?.
Kar ki damu ya ke k’awata zan maki jagora kishiga dan ita Gimbiyarmu tana da sauk’in kai da dad’in mu’amala sannan bata banbanta mu da bak’ak’en mayu kamar yadda mahaifiyarta take..
Cikin jin dad’i tsohuwa Umbaz tace zanyi farin ciki da hakan..
Jinjina kai Tsohuwa Sharmiza tayi sannan tawuce gaba Umbaz tana biye da ita suka shiga Turakar Najla…
Tunda suka shiga take baza idanu tana kalle kalle ganin irin kayan alatun da ‘bangaren Najla yaji chan taja tatsaya tace Sharmiza zan koma ‘bangaren Gimbiya Najma ta aikeni ne kar taga na dad’e…
Haba Umzab kisaki ranki kizo mushiga na fad’a maki Gimbiya Najla batada matsala…
Girgiza kai tayi tace a’a kar uwargijiyata taga na dad’e tayi fushi
Toh shikenan Umzab nagode sosai sai mun sake had’uwa
Murmushi Umzab tayi tace ba damuwa Sharmiza sannan tajuya cikin sauri tatafi inda Sharmiza tawuce ciki da kwandon furen da ke hannunta tana zuwa tafara had’awa ta ajiye a ‘bangaren kujerar da Gimbiya Najla take zama sannan tawuce tatafi
Najla fitowa tayi daga cikin Bedroom d’inta taje tazauna saman kujerarta tana murmushi ganin furen da Sharmiza ta ajiye mata tad’auko tana dubawa dan ita ta kasance tana k’aunar fure sosai….