KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Tsohuwa Umzab tana barin ‘bangaren Najla cikin sauri tanufi ‘bangaren Gimbiya Najma tana shiga bata lura da Najma da ke zaune saman kujerarta ta Mulki ba sai jin muryarta tayi ta ce shin Umzab ko zaki iya sanar da ni abinda kika shiga yi a turakar matacciyar Sarauniya Nuwairah?
Duk’awa Umzab tayi nan jikinta yafara rawa saida Najma tadaka mata tsawa sannan tace ranki yadad’e kigafarceni daman zuwa nayi nafad’a maki abinda baki sanibam
Gyara Zama Gimbiya Najma tayi tace ina saurarenki menene kika sani wanda ni ban saniba?..
…Sarkine yasa aka gyara ‘bangaren Sarauniya Nuwairah aka yi mashi ado da kayan alatu wanda ke kanki ba’a zuba maki su ba shine yamallaka shi ga Gimbiya Najla a yanzu a chan take zama na nemi taimakon wata kuyangarta ne tashigar da ni dan ingano inzo infad’a maki kuma na shiga na ga tsarin komai na ciki ya yi dan ni da fari na ma d’auka Sarauniya aka gyara mawa zata koma ciki
Ran Gimbiya Najma ‘baci yayi lokaci guda tamik’e daga saman kujerar Mulkinta a fusace tace zan je ingano idan har kin min k’arya da abinda kika fad’a min sai naga bayanki ya ke Umzab…
Saurin ‘bacewa Umzab tayi ganin yadda Shugabar tasu tatafo a sukane tana fita kuyanginta suka fara ‘bullowa ta kowace ‘bangare zasu take mata baya tadaka masu tsawa tace kar wacce tasaki tabiyota…
Cikin sauri tanufi ‘bangaren Gimbiya Najla tana shiga cikin turakar wasu kuyangi da ke tsaye suna aiki ganin yadda tashigo a sukane yasa suka nufi wajen da take suna cewa ya ke Gimbiya Najma shin ko kina buk’atar ganin ‘yar uwartaki muyi maki iso….
Tun kan surufe baki tanuna su da hannu asukwane nan take wani jan abu me kama da wuta yafito daga cikin tafin hannunta yadaki fuskokinsu sai gasu k’asa zube fuska ta k’one wasu daga cikin kuyangi da sukaga haka sukayo wajen nan ma bata saurara masu ba tayi masu abinda takayi ma na farko…
Sharmiza da ke tsaye ganin ‘barnar da Najma take ma kuyangin Najla yasa cikin sauri tashiga parlorn Najla tasameta a zaune tana rik’e da furannin tana kallo ganin yadda tashigo a sukwane yasa Najla takalleta cike da mamaki batare da ta ce komai ba
Zubewa Sharmiza tayi a gabanta tace ya shugabata hak’ik’a ina bak’in cikin sanar da ke ‘yar uwarki Gimbiya Najma ta shigo cikin turakar nan taki tana ta kashe kuyanginki a yanzu haka ta dirfafo hanyar parlorn nan naki bansan da me tazoba ina jin tsoron kar ta cutar da ke
Jin abinda tace yasa Gimbiya Najla tamik’e cikin sauri tayi hanyar waje, Sharmiza tana ta kiranta ammah bata saurareta ba tana fita tasamu Najma a tsaye tana ta k’one mata fararen kuyanginta inda wasu suketa guduwa suna kururuwa suna neman suceci rayukansu ran Najla ‘baci yayi tadaka mata tsawa tace Najma menene haka kike aikatawa miye dalilinki na zuwa cikin turakata?
Juyowa tayi a fusace takalli inda Najla take tace sanin dalilin shigowata bai zama dole ba ina da ikon shiga ko’ina a cikin Masarautar nan dan haka kar kisaki kice zaki nuna min iko a wannan wajen.
‘Daure fuska Najla tayi tace idan har na fahimceki kinzo ne kici min mutunci ki’bata min rai wannan dalilin ne yasa kike kashe min kuyangi
Murmushi Najma tayi tace fiye da hakan nazo inyi maki, juyawa tayi takalli hanyar parlorn Najla tace oohooo watau Sarki ya gyara maki ‘bangaren nan ya zuba maki komai sabo me tsada kin dawo nan ko? Wai me kika d’auki kanki ko kina tunanin kin fi ni ne? Toh ina so kisani nice nan magajiyar Sarki ko bayan ranshi.
Ta’be baki Najla tayi tace wannan ke yadama Najma ni baya gabana duk fitinar da kikazo da ita kisafketa dan ni bazan ta’ba biye maki ba….
Najma maimakon tabata amsa juyawa tayi takalli Sharmiza da ke tsaye bayan Najla tana ta mak’erk’eta saboda tsoro nan wani haske yafito daga idanun Najma yadirfani inda take tsaye Najla tana ganin haka cikin zafin nama takai hannunta tatare hasken wata irin k’ara tatashi sai ga hayak’i, bushewa da dariya Najma tayi tace watau ke har kina da Sihirin da zai iya karya wanda nayi toh a yau zanga iya gudun sihirinki dan haka sai ki kare kanki….
Najla tana bud’e baki zatayi magana wani hasken yafito daga cikin idanun Najma yatunkari inda take tsaye saurin sa hannu tayi tatare shi duk yadda taso takaryashi kasawa tayi ganin yana shirin zuwa inda fuskarta take dan haka tasa dukkan k’arfinta tatare, k’ara ma tsafin k’arfi Najma tayi tasake jefo mata wani hasken me zafi cikin sauri tasa gudan hannunta tatare bushewa da dariya Najma tayi nan tad’aga hannu tana tunkarar Najla gadan gadan ganin haka yasa Najla tadinga ja da baya a hankali har lokacin hannuwanta suna tare da wannan hasken me zafi da Najma tajefeta da shi sunyi kusan mintina talatin a haka har Najla tafara fita hayyacinta saboda siracin zafin da ke dakar mata hannu……
_*Part 1 Free pages ne*_
_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
_Sis Nerja’art_
09035938246[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 7*
*K’ASAR MIRAJ*
K’asa ce me yalwatattar arzik’i inda mutane ne suke rayuwa a cikinta akan tafarki na addinin musulunci, ta kasance gari me girma wadda tashahara akan dukiya har yakasance tana cikin manyan k’asashen da ake ji da su a cikin duniya, dan k’asar basu raina sana’a komai k’ank’anta.
Suna da wani sarki me aldaci ana kiranshi Sarki Abdullah, yana son jama’arshi sosai su ma suna son Sarkin nasu dan yana da adalci atsakanin jama’arshi sannan baida girman kai baya banbanta talakka da me kud’i duka d’aya yad’aukesu wannan dalilin ne yak’ara mashi farin jinin a wajen mutanenshi…
Fadar sarkin kusan gari guda ce aka gine an k’awata ta sosai, inda gidan sarautan ma yakasance abun kallo ga duk wanda yashiga, yanayin ginin kawai zaka gani kagane cewa kud’i sun zauna ma masarautar..
Sarki Abdullah yana da mata biyu da ‘ya’ya ukku
Matarshi ta farko Sarauniya Marwa d’iyace ga amini kuma wazirin mahaifishi sun kasance aminnan juna tsakanin Sarkin da yashud’e Sarki Aliyu da Waziri zayyana sun zauna da juna cikin aminci da yarda wannan dalilin ne yasa sukayi sha’awar had’a ‘ya’yansu aure dan a lokacin Sarki Abdullah shine kad’ai d’a ga Sarki Aliyu kamar yadda Sarauniya Marwa takasance d’iya tilo ga Waziri Zayyana, a lokacin da iyayen nasu suka bujuro masu da buk’atarsu nan take sukayi na’am musamman Sarki Abdullah da yanuna farin ciki sosai saboda Sarauniya Marwa batada makusa ko kad’an atare da ita dan mahaifiyarta Shuwa Arab ce Waziri Zayyana ya aura saisa tayi kyau sosai tad’akko mahaifiyarta, shima Sarki Abdullah dayake ba bayaba wajen kyau da kyakkyawar halayya, sun k’ulla soyayya me tsanani a tsakaninsu cikin lokaci kad’an aka yi aurensu, gab da shirye shiryen bikkinsu Allah ya amshi ran mahaifiyarta akan hanyarta ta zuwa ziyara k’asarsu tayi had’ari tarasu Marwa ta yi kuka sosai daga ita har mahaifinta sun shiga cikin hali na damuwa dayake su d’in musulmai ne wad’anda suka yadda da k’addara suka mik’a lamurransu ga ubaubangiji