KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Bayan an gama koke koken ne aka sha bikkinsu tatare a gidan mijinta Sarki Abdullah lokacin yana magajin gari suna da shekaru ukku da aure Sarki Aliyu yarasu aka nad’a Sarki me jiran gado yazama sarkin gari a lokacin shi kanshi waziri zayyana ya tsufa sosai yana hali na bak’in cikin rasa abokinshi kuma amininshi daga k’arshe ya ajiye sarautarshi ta wazirci yace bazai iya cigaba da kasancewa Waziri ba saboda ya yi rashin aboki, dan haka ne aka nad’a wani aminin Sarki Abdullah yazama wazirinshi, Waziri zayyana baifi wata ukku da ajiye wazircinshi ba yakwanta ciwon ajali ya d’auki tsawon wata d’aya yana jinya kafin daga baya rai yayi halinshi….
Sarauniya Marwa har kusan zaucewa tayi saboda tashin hankalin da tashiga kafin daga baya tadangana…
Mahaifiyar Sarki Abdullah itace kad’ai tarage masu watau Sarauniya Amina suna kiranta da Yakumbo..
Shekarar Sarki Abdullah da Sarauniya Marwa Takwas cif da aure sannan Allah ya azurtasu da d’a namiji dan a lokacin har sun gama fitar da rai da samun haihuwa dan tun daga Sarki har Yakumbo kullum cikin samo ma Sarauniya Marwa maganin haihuwa suke duk wani me maganin da sukaji a fad’in k’asar sai sunje sun samo mata tun tana sha har tagaji abun yadinga bata tsoro tana ganin bazata haihu ba haka dai tacigaba da mik’a ma ubangiji kukanta
Lokacin da tafara laulayi babu wanda yagane cikin sai daga baya da likita yazo yadubata yake masu albishir da cikin da ke gareta kar kuso kuga farin ciki wajen Sarki Abdullah da Yakumbo gabad’aya mutanen da suke cikin k’asar saida suka san da Sarauniya Marwa tana da ciki dan labarin kaf yazagaya ko’ina duk wani masoyin sarki saida yayi tattaki yazo yataya sarki murna…
Kulawa ta musamman Marwa tadinga samu tun ba ga mijinta da surukarta ba hatta ma’aikata da kuyanginta duk wanda yake cikin gidan yana bata kulawa sosai dan suna sonta saboda ita d’in macece me hak’uri da kawaici batada abokin fad’a ta d’auki rayuwa da sauk’i.
Lokacin da cikinta yacika wata tara tahaifo shantalelen d’anta jajir da shi wanda bai rage komai ba a wajen kamanninta, farin ciki wajen su sarki da masoyansu ba’a magana nan aka dinga murna saboda jin dad’i a ranar da aka haifeshi sarki yaje gidan kaso yayafe ma masu laifi mutane d’ari sannan ya ‘yanta bayi d’ari maza da mata, ya bada umurni duk wani yaro da aka haifa a ranar a cikin k’asar miraj to azo wajenshi zai bada kaya da ragon suna sannan yafitar da kud’ad’e akayi shagali na musamman..
Kyautuka daga k’asashe dadama aka dinga aiko masu shi da d’anshi da matarta inda ‘yan cikin k’asar miraj ma ba’a barsu a baya ba wajen bada tasu kyautar hatta marassa k’arfi saida suka samu abinda suka kai ma sarki dan kawai su faranta mashi, tun daga babba har k’ananun kyautukan da su sarki suka samu sun sa su farin ciki dan Sarki Abdullah har kuka yayi saboda jin dad’i ganin soyayyar da ake nuna mashi..
Ranar suna yaro yaci Suna Aliyu ammah suna kiranshi da Ayran
Tunda Yarima Ayran yataso ya taso cikin gata da kulawa ta kowace ‘bangare soyayyar da akeyi ma mahaifinshi tashafeshi inda Sarki Abdullah yake k’aunar d’an nashi sosai baya son abinda zai ta’ba mashi shi, Ayran tun yana yaro miskili ne sosai bai cika son yawan magana ba duk wani jin dad’in rayuwa yana samu wajen iyayenshi da kakarshi an sa shi makaranta me kyau da tsada, yana da shekaru shidda Sarauniya Marwa tak’ara haihuwa a wannan karon tahaifi tagwaye duk mata nan ma aka yi murna sosai inda yara suka ci sunan Yakumbo da mahaifiyar Sarauniya Marwa watau Amina da Aisha ammah ana ce masu Afrah da Afreen.
Tun daga kansu Sarauniya Marwa bata sake ko ‘batan wata ba haka suka d’auki son duniya suka d’aura akan ‘ya’yan nan nasu…
Yarima Ayran yana k’ara girma kyaun shi yana k’ara bayyana inda miskilancinshi da rashin son hayaniyarshi yak’aru, tun yana k’arami sai Sarki ya yi dagaske sannan yake amincewa suje fada dan kwatakwata baya da sha’awar sarauta, sarki yana kwatanta mashi akan yadinga zuwa fada dan sarauta tashi ce dole wata rana zai gajeta tunda a jinin gidansu take, dayake da k’uruciya atare da shi saisa bai fahimtar inda zancen sarki yadosa….
Sarauniya Zaiba ta kasance d’iya ce ga ‘yar uwar mahaifiyar Yakumbo wadda takasance mahaifiyarta k’anwa ce ga yakumbo, Zaiba ta yi aure a gidan wani attajiri a cikin garin miraj aurensu baifi shekaru sha biyar ba da ‘yar d’iyarsu d’aya mijin nata yarasu Yakumbo tad’akko takawota gidan sarauta tarik’eta wajenta tana zawarci, ai tunda Zaiba tad’aura idanunta akan Sarki Abdullah tace dawa Allah yahad’ata nan fa tafara tunanin yadda zata ‘bullo tasamu sarki ya aureta, a farkon zuwanta bata cika shiga sha’anin matarshi gimbiya marwa ba ammah daga baya sai tafara shishige mata tana jan yaranta su Afrah da Afreen a jiki su kuma ganin d’iyarta Farha kusan tsararsu ce koda ad’an kwai tserataryar shekaru biyu tsaninta da su ammah ahaka suka taso kamar abokai..
Shiga da fita Zaiba tadinga yi wajen Sarauniya Marwa da Yakumbo tana kyautata masu sosai har saida tashiga ran Yakumbo sannan ganin bata kula kowane bajawari yasa tayi ma d’anta sha’awar auren ‘yar uwar tashi da fari har ya nuna bai aminceba saida yaga ran mahaifiyartashi yana neman ‘baci sannan ya amince dan koda yaje ma matarshi da maganar itama goya ma yakumbo baya tayi akan ya auri Zaiba kan dole yahak’ura akayi aurenshi da Zaiba…
Tunda ta auri Sarki Abdullah sai da tashiga tafita komai na cikin gidan Sarauta yadawo hannunta dayake Sarauniya Marwa macece mai kauda kai kawai sai ta k’yale tacigaba da hidimarta, har suka d’auki tsawon shekaru da Sarki bata ta’ba ko ‘batan wata ba
Lokacin da Yarima Ayran yagama Secondry School d’inshi nunawa yayi yana da sha’awar fita waje yayi karatun Doctoring da fari har mahaifinshi ya k’i amince dan baiso yayi masu nisa ya fi so yazauna a cikin k’asarshi , saida yadinga rok’onshi sannan ya amince yafitar da shi a India…
Shekarun shi biyar a india ammah abokinshi guda Salim d’an Waziri dan shi d’in baya son tarkacen abokai, ‘yan matan ko da suka dinga kawo kansu wajenshi basu k’irguwa dan ma shi d’in ba mai ra’ayin mata bane saidai yadinga wulak’antasu ammah hakan baisa suyi zuciya sudaina ba, ganin haka yasa yake cewa duk mata halinsu d’aya basu da aji bazai ta’ba son wata mace ba
Ahaka dai yasamu yagama karatunshi yadawo gida, a ranar da zai dawo ko idan kashigo garin miraj sai kad’auka wani gaggarumin bikki ake dan Sarki shi kanshi baki har kunne shiri akayi na musamman na tarar d’an nashi
Bayan ya dawo ne Sarauniya Zaiba tanemi tafara cusa mashi d’iyarta Farha dan ta ci nuri akan aura ma Yarima Ayran ita, itama kanta Farha tana k’yalla idanu taganshi tace ma mahaifiyarta ita babu wanda zata iya aura in ba Yarima Ayran ba, saidai shi dayake bai bada fuska ba yana da k’warjini sosai su kansu mutanen gidan suna ganin k’warjininshi bare na waje in ko har ka ga yana hira to da iyayenshi yake ko ‘yan uwanshi Afrah da Afreen magana in ba wadda tazama dole ba bata cika had’ashi da sarauniya zaiba da ‘yarta Gimbiya Farha ba dan ya lura da Farha bata da kamun kai sosai saboda yadda take shige mashi dan ma yana taka mata burki, ammah ahaka take kauda kai tacigaba da nuna mashi tana sonshi yadda yake ma yana ba ‘yan uwanshi haushi dan aganinsu basuga makusa atare da Gimbiya Farha ba