HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Ba iya Gimbiya Farha kad’ai take rawar jiki ga yarima ba hatta ‘yan mata dadama suna nuna mashi so a cikin garin, Sarakunan da suka aiko mashi da gayyar yazo ya nemi auren ‘ya’yansu suna da yawa sosai ammah duk ce masu yayi subarsu ya gode, abun har mamaki yake ba Maimartaba yafara tunanin anya kuwa d’an nashi yana da lafiya?

Waziri yace lafiyarshi lau kawai bai ga macen da tayi mashi bane ka san irin su yarima dole sai sun darji mata
Saidai sarki yakad’a kai kawai, nan kuma yafara sa ana kawo mashi hotunan ‘ya’yan abokanshi ko yarima ya samu wadda tayi mashi ammah bai za’ba ba

Asibiti me girma da kyau Sarki yasa aka gina ma d’an nashi dayake Gynae Doctor ne nan asibitin shi tashahara a cikin k’asarsu da wajen k’asarsu duk wata mace me matsala tana k’ok’arin zuwa dan ya zuba liitoci k’wararru wad’anda suka san abinda sukeyi.

Su kansu wasu likitocin da Nurses mata saida suka fara tallar kansu a wajenshi saida yayi masu barazana akan rasa aikinsu sannan suka daina…

**** ****

PRINCE AYRAN GYNAE HOSPITAL

.Mata ne ba adadi a cikinta likitoci suna ta k’ok’ari wajen dubasu saboda yau monday ta cika sosai, Doctor Salim ne yafito daga office d’inshi daidai da wata nurse zata wuce kallonta yayi yace Sister Khairat wai har yanzu Dr Ayran bai shigo ba na ga patients d’in da aka kai mashi zaune har yanzu ba’a fara duba su ba, murmushi tayi tace Eh Dr Salim ammah ina tunanin yana hanya tunda ten ta yi..

Jinjina kai yayi yawuce yaje yayi abinda zaiyi yakoma akan aikinshi…

 

Office ne na musamman me zaman kanshi inda Dr Ayran yake zama, a wajen Office d’in mata ne sun kai ishirin abinda zai baka mamaki wasun su zaune suke suna kwalliya babu alamun ciwo atare da su sai masu jin jikin bazasu wuce mata goma ba…

Wani had’ed’d’en saurayi ne yatunkaro wajen sanye cikin k’ananun kaya fuskarshi d’auke da farin glass yana tafiya cikin k’asaita gabad’aya matan da suke zaune wajen suka maida kallonsu akanshi inda wasu suka shagala ga kallonshi ko inda suke bai kalla ba yashige cikin office d’inshi zama yayi yakalli Folders d’in da aka ajiye mashi sannan yad’auko wayarshi yakira cikin muryarshi me dad’i da nutsuwa yake wayan da ba sosai yake magana ba saisa bazaka iya jin abinda yake cewa a cikin wayar ba, yana gamawa ajiyewa yayi…

Wata Nurse ce tatunkaro office d’in nashi tana murmushi ita kanta fuskarta d’auke da kwalliya tana zuwa tayi knocking nan yabada izini tatura tashiga
Gyaran murya tayi tagaisheshi batare da ya d’ago ya kalletaba bare tasa ran zai amsa mata yace ga folders nan kifara kira min patients

Murmushi tayi tace toh ammah wane folder za’a fara da shi, shuru yayi yana cigaba da dannar waya wani irin haushi Sister Khairat taji dan ta so yad’ago kai yakalleta ko dan yayaba da kwaliyarta turo baki tayi tad’auki folder da ke sama tafita takira patient tafarko wata budurwa ce tataso ta ci gayu sosai Sister Khairat tana ganinta wani k’ululun bak’in ciki yatsaya mata cikin ranta tace kar dai Yarima yak’yasa idan yaga wannan dan tana da kyau sosai…muryar budurwar ce taji ta ce gani Sister

Batare da ta ce mata komai ba tawuce budurwar tabi bayanta zuwa cikin office d’in a gabanshi ta ajiye mashi folder sannan tanuna ma patient d’in inda zata zauna ita kuma tad’auki sauran folders d’in tafita

Sai a lokacin Dr Ayran ya ajiye wayarshi yajuyo yakalli wadda ke zaune tana ta aika mashi da kallo yace ina saurarenki menene yake damunki?

Tashin farko fari tayi mashi da idanu tace am abinda yake damuna? Shuru tayi kamar tana son tuno wani abu
Wani irin haushi Dr Ayran yaji ganin babu alamun akwai ciwo atare da ita yakwatsa mata tsawa yace tatashi tabar mashi office batada hankali

Mik’ewa tayi cikin sauri sai ga hawaye sun gangaro daga idanunta cikin muryar kuka tace Yarima sonka ne yasa kaganni na zo asibitin nan kuma na so ace ka bani dama na fayyace maka abinda yake cikin zuciyata…..fuskarshi a murtuk’e yanuna mata k’ofa

K’warjini yayi mata sosai dan haka tajuya tana goge fuska tafita

Dafe kanshi yayi da hannu biyu cike da takaici,

Sister Khairat da ke tsaye a wajen k’ofa ta ji abinda patient d’in tace wani irin haushi yakamata patient d’in na fitowa takalleta tabushe da dariya, wata irin harara patient d’in tagalla mata tawuce tatafi, a karo na biyu Sister tatura mashi wata patient d’in yana d’aga kai yakalleta yaga kamar itama irin ta farko ce ganin yadda take tafiya tana karairaya nuni yayi mata da k’ofa alamun tafita

Ja tayi tatsaya tana kallonshi saida yak’wala ma nurse d’in kira tashigo kallonta yayi yace sau nawa ina ce maku kudinga turo min masu ciwo ba wai masu lafiya ba?.
Dabarbarcewa tayi tace am so sorry Doctor su ma sun ce basuda lafiya ne

Ta’be baki yayi yace kije kituro min manyan mata duk wata wadda ba babbar mace ba kikaima su Dr Najeeb sudubata.

Amsawa tayi da toh sannan takalli wadda ke tsaye tana kallon Dr Ayran tace sai muje ko?
A k’ule tajuya suka fita

Suna fita Sis Khairat takalli sauran ‘yanmatan da suke ta k’ara gyara kwalliya tabushe da dariya tace lallai taku ta sameku indai Dr Ayran ne bazai ta’ba kula ku ba daman kun hak’ura da shi, wasu daga cikinsu ne suka tasar mata suna cewa kema d’in ai kwalliyar kikayi saboda shi…

Shuru tayi tafara kiran folders d’in duk wadda taga ba babbar mace bace sai ta ajiye folderta gefe saida tacire folder kusan goma sannan tace ma sauran sutashi sutafi kwalliya bata biya kud’in sabulu ba dan ba Dr Ayran zai dubasu ba ya ce iyaye kawai zai duba..

Wani irin haushi yakamasu nan wasu suka d’auki komatsensu suka yi tafiyarsu masu jin ciwo ne suka bi bayan Sister Khairat taraba ma sauran Doctors folders d’insu…

Dr Salim yana gama duba patients d’inshi yafito yanufi office d’in Dr Ayran yana turawa yashiga yasameshi zaune yana dannar waya da mamaki yake kallonshi yace ashe ka shigo ya naga baka fara duba patients ba?

Shuru Dr Ayran yayi yana dannar waya kamar ba da shi yake magana ba, murmushi Dr Salim yayi yaja kujera yazauna dan idan da sabo ya saba da halin abokin nashi

Sun yi kusan minti biyar a haka sannan Dr Ayran yad’ago yakalleshi har ya bud’e baki kamar zaiyi magana sai kuma yafasa

Girgiza kai Dr Salim yayi cikin ranshi yace watau yau sarautar ta motsa…..Sis Khairat ce taturo k’ofa tashigo tace Doctor na raba masu folders d’in ga manyan matan nan na bari afara kiransu?
‘Daga kai yayi alamun eh
Nan tajuya tafita
Zaro idanu Dr Salim yayi waje yace ban gane manyan mata ba ina sauran ‘yanmatan da nagani zaune su fa sukace lallai sai Yarima ne zaka duba su

Yatsine fuska Dr Ayran yayi yace kar kusaki kusake bar min su kudinga dubasu dan na gaji da wannan halin nasu kuma….bai ida fad’in maganar da ke cikin bakinshi ba yayi shuru

Dr Salim danne dariyar da ke cinshi yayi yace toh ranka yadad’e ammah ai da ka yi hak’uri sun cigaba da zuwa watak’il zaka samu mata a cikinsu wadda tayi…

Maganar da ke bakinshi ce tamak’ale mashi lokacin da Yarima Ayran yawurga mashi wata uwar harara daidai da shigowar wata dattijuwa dan haka Yarima Ayran yace malam kabani waje zanyi aiki

Mik’ewa Dr Salim yayi yace angama ranka yadad’e idan ka gama zan dawo dan akwai abinda nakeso mutattauna

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button