KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Batare da ya ce mashi komai ba yayi ma matar nuni alamun tazauna
Amsar folder d’inta yayi yace me yake damunki……
__________
Gimbiya Afra da Afreen ne zaune a tank’amemen parlornsu kowa hannunshi rik’e da waya suna danna inda kuyanginsu suke ta kaiwa da kawowa suna masu hidima, Gimbiya Farha ce tashigo cikin parlorn nan Kuyangin suka zube suna kwasar gaisuwa, yatsine fuska tayi tawuce tazauna kusa da su Gimbiya Afrah sai a lokacin su Gimbiya Afrah da Afreen suka d’ago kai suka kalleta murmushi suka sakar mata kusan a tare sukace Wow Sis wannan irin kyau haka da kikayi, kinga yadda kika had’u kuwa?,,, Gimbiya Afrah tak’arashe tambayar
Murmushi Gimbiya Farha tayi tare da gyara zama tace Sisters ku dai kubari kawai ai dole sai da gayu
Kallon juna sukayi sukai murmushi sannan Afrah tace ke dan Allah Sis ko dai anhango wani guy d’in
Yatsine fuska tayi tace kun san dai babu wanda zan so in ba Yarima ba ammah shi sai wani ja min aji yake yana shan k’amshi
Haba Sis duk fa laifinki ne mun ce kije kifad’a mashi abinda yake cikin ranki ammah kin k’i
Uhm taya kuke tunanin zan iya fayyace mashi sirrin da yake cikin raina alhali bai bani fuska ba, kuna gani ko dariya bai cika yi a gabana ba
Afrah ta’be baki tayi tace indai Bro ne haka yake muma kina ganin yadda yake wani basar wa in yaganmu, wallahi har tsoron yi mashi magana nake indai ba na ga yana cikin fara’a ba jiya ma daga na je part d’inshi yana barci ban saniba ina shiga yafarka bakiga fad’an da yayi min ba har saida nayi kuka ai Bro shi dai halinshi sai shi duk wadda ta aureshi ta bani….
Tun kan tarufe baki Gimbiya Farha tatari numfashinta tace a’a wallahi kidaina cewa haka ni ai ahaka nake son abuna kuma zan aureshi a hakan inyaso bayan aurenmu sai incanza abuna
Su dukansu dariya sukasa suka fara tsokanarta,
Mik’ewa Gimbiya Farha tayi tace ku dai kuka sani bari inje ink’ara gyara fuskata dan nasan Yarima yana gab da dawowa zan je intareshi dan yaga kwalliyata k’ila yayaba in fara burgeshi.
Su dukansu binta sukayi da kallo batare da sunce komai ba dan sun san abinda tace d’in mawuyacine yafaru saboda sun san d’an uwan nasu ciki da bai……
_*Part 1 Free pages ne*_
_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
_Sis Nerja’art✍????_
09035938246
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA…*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 6*
..Daidai lokacin Sarki Nawar yatunkaro turakar cikin sauri dan tuni ya ga abinda yake faruwa a cikin madubin tsafinshi yana shigowa tsawa yadaka ma Najma ba shiri tayi saurin safke idanunta k’asa wannan hasken ya’bace, isowa ya ida yi wajensu cikin ‘bacin rai yace Najma me kike aikatawa haka ‘yar uwartaki zaki cutar da ita?
‘Dago kai tayi takalli mahaifin nasu fuska a had’e sannan tace Abba ita bakaga abinda tayi min ba sai ni zakaga abinda nayi mata shin wai meyasa kake son nuna banbanci tsakanin ni da ita ko dan kaga ita tana daga cikin k’abilarku ni kuma ina cikin ta mahaifiyata? Na rasa dalilin da yasa kake fifita Najla akaina kana nuna min ka fi k’aunarta!
Tsawa yadaka mata yace yi min shuru Najma bazan d’auki wannan shashancin naki ba, tun kuna yara ina k’ok’ari wajen ganin na had’a kawunanku ammah keko kink’i yadda da hakan a fili kike nuna baki k’aunar ‘yar uwartaki, ni a wajena ku dukanku babu banbanci dan duk ni nahaifeku babu wacce tafi wata a cikinku ina baki shawara kisafke wannan bak’ar zuciyar taki kija ‘yar uwarki a jiki…
‘Dan guntun murmushi Najma tayi tace dole kace haka Abba wannan duk dad’in bakine dan a zahiri gashinan kowa ya gani kuma ya sani ka fi k’aunar Najla akaina kaduba kaga yadda kagyara mata wannan ‘bangaren kazuba mata komai mai kyau da tsada shin ni da mahaifiyata ka yi mana hakan?
Ran Sarki Nawar k’ara ‘baci yayi yace Najma kina bak’in ciki da ‘yar uwarki dan kawai na yi mata wannan? Shin ke sau nawa ina maki wani abu ita ban mata ba kin ta’ba gani ko da a fuska ta nuna?
Jinjina kai tayi tace koma menene kaje kayi Abba saidai inaso kasani bazan ta’ba son Najla ba..
Tsawa yadaka mata yace ya isa haka Najma kiwuce kibar wajen nan tun kan ranki ya’baci!
Juyawa tayi a fusace tawuce tatafi…
Idanun Najla cika sukayi da k’walla jin furucin da ‘yar uwartata tayi Sarki Nawar yana ganin ta wuce yayi saurin isa inda Najla take yarik’e mata hannu yana cewa sannu Najla ina fatan babu abinda yasameki?.
‘Dan guntun murmushi tayi tace babu komai Abba
Tsura ma hannunta idanu yayi ganin yadda jini yakwanta yasa yajata suka shiga parlornta suka zauna yana rik’e da hannun nan yayi mata tsafi hannunta yakoma kamar yadda yake..
‘Dan guntun murmushi tayi ahankali tace nagode Abba
Cike da damuwa yake kallonta yace Najla kidinga hak’uri da yanayin ‘yar uwartaki tana da zafin rai sosai nasan fushi ne yasa tayi wannan furucin
Hawayen da Najla take dannewa ne suka gangaro mata tayi saurin sadda kanta k’asa
‘Dago mata da kai Sarki Nawar yayi yace nasan hakan da tayi baiyi maki dad’iba kicigaba da hak’uri komai zai zo k’arshe
Janye kanta tayi gefe tace har sai yaushe hakan zai faru? Abba kana gani yadda Najma take nuna min tsana ita da Didi bansan me nayi masu ba kaine kad’ai nake kallo inji dad’i, ina jin tsoron wani lokaci wanda zai rabamu bansan ya rayuwata zata kasanceba
Gaban Sarki Nawar saida yafad’i yayi saurin jawota yarungume a jikinshi damuwa ce k’arara tabayyana a fuskarshi rasa abinda zai ce ma Najla yayi dan shima kanshi abinda yake yawan d’aga mashi hankali kenan a duk lokacin da yatuna..
Kuka tadinga yi k’asa k’asa nan Sarki Nawar yafara shafa bayanta alamun lallashi chan dai yadaure yace Najla kidaina wannan tunanin bana ji akwai abinda zai rabani da ke zamu cigaba da kasancewa a tare bazan ta’ba bari acutar da ke ba kinfi kowa sanin yadda nake k’aunarki babu abinda bazan iya yi saboda ke ba.
Rage sautin kukanta tayi tare da zame kanta daga jikin mahaifinta tana kallonshi
Rik’o hannunta yayi yace kiyarda da ni Najla ni mahaifinki ne zan cigaba da baki duk wata kulawa da tadace bazan ta’ba bari acutar min da ke ba