KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Goge hawayen fuskarta tayi tare da yin guntun murmushi tace nagode Abba nah.
Shima murmushin yayi yaja kumatunta.
Mik’ewa tayi tace Abba zan shiga ciki inkwanta…
Rakata yayi har cikin bedroom d’inta saida yaga bata tare da wata damuwa sannan yafito a filin gidan yaga antara gawarwakin fararen mayun da Najma takashe tsayawa yayi yana kallonsu ranshi duk a ‘bace sannan yamaida kallonshi ga su Hasisa da ke duk’e k”asa suna mik’o gaisuwa yace kutabbatar an kwashesu anfitar da su batare da Najla ta saniba kuje ak’onasu sannan kucigaba da bata kariya kukular min da ita sosai idan har kuka bari wani abu yasameta gabad’aya sai na maidaku gawa,,, yana fad’in haka yawuce a fusace yaficce…
Shigarshi a turakarshi ya yi daidai da shigowar Sarauniya Wailah rai a ‘bace zama yayi saman d’aya daga cikin kujerun da suka k’awata d’akin daga gefenshi tatsaya tace ya kai mijina hak’ik’a banji dad’in abinda kayi ma ‘yata Najma ba shin meyasa kake son banbantasu ita da Najla alhalin su dukansu ‘ya’yanka ne?
‘Dan guntun murmushi yayi yace Wailah kece yadace inyi ma wannan tambayar ko kin d’auka duk abinda kike bana da masaniya akai, kwatakwata bakya son jan Najla a jiki kina nuna mata tsana dan kawai ta kasance d’iyar abokiyar zamanki kuma ta fito daga jinsin fararen mayu…
Akan me zan ja ta a jiki bayan bani nahaifeta ba sannan kaima kanka kana banbantasu kana nuna ta fi ‘yata bayan Najma itace zata kasance magajiyar garin nan bayan ranka ya kamata kagyara abinda kakeyi dan na fara gajiya da cin mutuncin da kake min ni da ‘yata
Murmushi Sarki Nawar yayi yace Wailah kece yakamata kizauna kiyi ma kanki fad’a idan har zaki gyara halayyarki zan fi kowa farin ciki akan hakan..
Wani irin kallo tayi mashi yajuya tafita daga turakarshi..
Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo ahankali yace Wailah kin kasa fahimtata har yanzun…
*** *** ***
Sarauniya Wailah tana barin turakar Sarki kuyanginta takira cikin fushi tafita daga gidan Sarauta tanufi gidan mahaifinta Boka Gobar tana isa tatarar ya shiga cikin d’akin tsafinshi dan haka tasamu waje tazauna tana jira yafito
Ta dad’e sosai kafin yafito yana ganinta murmushi yayi yace ashe dai madubin tsafina baiyi k’arya ba kece dai dagaske kikazo.
Kauda kanta tayi gefe ganin haka yasa yace Wailah daga ganin yanayinki akwai abinda yake damunki ko zaki iya sanar da mahaifinki?
Juyowa tayi takalleshi tace Baba abubuwa dadama suna damuna na fara gajiya da hak’urin da nake akan halayyar sarki…
Katseta yayi yace dakata Wailah me kuma sarkin yayi maki?.
Yatsina fuska tayi tace komai ma ya yi min nasan ka san yadda yake nuna banbanci tsakanina da Nuwairah lokacin da take raye yana nuna ya fi sonta sannan itama Najla yana banbantata da ‘yah ta shin me zai hana wannan abun yak’i yi min ciwo?
Ajiyar zuciya Boka Gobar yasafke yace na san haka a yanzu kuma me ya aikata maki?
Gyara zama tayi takwashe duk abinda Gimbiya Najma tafad’a mata da kuma yadda sukayi da sarki tafad’a ma mahaifinta, shi kanshi Boka Gobar abun ya yi mashi ciwo cize le’be yayi yace lallai Sarki Nawar baya kyautawa ni kaina abun yana min ciwo ina kauda kaina ne kawai bana nunawa sannan wannan matar tashi Nuwairah na yi bincike ba adadi akanta ammah tsafina ya kasa gwada min komai bansan da wane irin sihiri Sarki Nawar yayi amfani ba bayan duk wani Sihirinshi atafin hannuna yake inma wani yake tayashi na kasa gane ko wanene, kucigaba da hak’uri daga inda yashud’e shikenan garin Nairan zai dawo a hannunmu sai yadda mukayi da shi.
Ammah Baba kana ganin Sarki Nawar zai amince Najma tamulki garin nan alhali Najla tana a raye?
Shuru yayi yana nazarin maganar ‘yar tashi sai chan yayi murmushi yace kibarni da shi na san ta yadda zan ‘bullo mashi mu rabashi da Najla cikin ruwan sanyi batare da ya gane cewa shirine mukayi ba.
Wani irin dad’i taji a ranta tace nagode sosai Babana tabbas nasan tunda har kafurta toh zaka iya aikata komai..
Shafa fuskarta yayi yace fiye da hakan zan iya yi dan na dad’e ina shiri akan ganin mulkin wannan garin namu ya dawo hannunmu kuma sai gashi cikin ruwan sanyi Sarki Nawar ya nuna yana son aurenki a lokacin na yi farin ciki sosai ko da hakan yana cikin shirina shekaru goma nayi ina aiki akanshi kafin sihirina yakamashi…
Murmushi Sarauniya Wailah tayi tana kallon mahaifin nata
Shima murmushin yayi yace kinga kitashi kikoma gidanki dan bana so Sarki yagane kin zo wajena.
Mik’ewa tayi cikin sauri tace shikenan Baba sai na ji daga gareka, tana fad’in haka tawuce tafita daga cikin gidan mahaifin nata….
****Washe gari Fada cike take mak’il ana ta fadanci inda manyan fadawa suke gefen kujerar sarki zaune daga ciki har da Boka Gobar da ba’a fad’i ko yanke wani abu sai an nemi shawararshi ana cikin tsaka da fadanci yakalli Sarki yana murmushi yace ranka yadad’e agaskiya bazan ‘boye maka ba ‘ya’yanka suna burgeni sosai dan tun da nake ban ta’ba jin Sarkin da akayi a cikin garin nan ba wanda yake da ‘ya’ya mata tamkar maza wajen jarumta da jijircewa kai ba ma ni kad’ai ba a yau d’innan kafin in iso fada abinda naji wasu jama’a daga farare da bak’ak’en mayu suna tattaunawa kenan akan ‘ya’yanka wad’anda basu da makusa wajen komai…
Tsoho Abnar murmushi yayi yace wannan haka yake Boka Gobar Gimbiya Najla da Gimbiya Najma sun zama abun kwatance acikin garin nan namu.
Sarki Nawar wani irin dad’i yaji jin an yabi ‘ya’yanshi bakinshi yak’i rufuwa.
Gabad’aya mutanen fadar haka suka cigaba da yabon su Najma sarki ko sai gyad’a kai yake yana ganin kamar babu wanda yafi ‘ya’yanshi a cikin garin…
Boka Gobar ganin yadda ake ta yaba su Najma yasa yaji dad’i dan ya san a yanzu hak’arshi ta cimma inda yake so, gyara zamanshi yayi tare da yin gyaran murya yace ga shawara na zo da ita, a chan shekarun baya nasan kun san cewa duk Sarkin da yahau mulki yana ajiye tarihin da ko bayan ranshi baza’a ta’ba mancewa da shi ba sannan zai zama abin alfahari ga iyalan da yabari saboda hakane nayi tunani akan Sarkin mu me zai hana sarki ya amince atura su Najma dajin Kursad suje suyo mana farautar Dodo Gumar ba wai sukashe shi ba tunda na san kasheshi abune me matuk’ar wuya saboda had’arin da ke tattare da shi kawai dai muna so suyanko mana kunnenshi guda d’aya kamar yadda shekaru ashirin chan baya muka nema ammah aka rasa wanda zai iya toh tunda a yanzu gasu munsan su zasu iya mana wannan aikin.
Jin buk’aar da Boka Gobar yazo da ita yasa gabad’aya fadar tayi tsit ana kallonshi hankalin Sarki Nawar tashi yayi yazuba ma Boka Gobar idanu batare da ya ce komai ba
Ganin haka yasa Boka Gobar yagyara zama yai murmushi yace ya naga duk kun karaya haka bayan kun san su Najma zasu iya shiga ko’ina ne kuma sufito lafiya bana jin su Najla da Najma na san zasu iya wannan aikin dan su d’in zaratan jarumai ne sannan zamu koyar da su dabarun yadda zasu shiga dajin kursad sufarauto mana dodo gumar ta haka ne sunansu zai shahara a cikin duniya ba wai iya nan k’asar tamu kad’ai ba sannan ta haka ne zamu gane cewa su d’in zasu iya mulkar k’asar Nairan a matsayinsu na mata masu kamar maza…
Mutanen cikin fadar suka fara na’am da maganar da Boka Gobar yayi wani tsoho yace tabbas ka kawo shawara idan har suka shiga suka fito lafiya zamu amince d’aya daga cikinsu takasance magajiyar garin nan bayan ran sarki