KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Kallon d’aya daga cikin fadawanshi yayi nan yayi saurin bud’e mashi abinda akasa aka rufe kwandon.
Kayan adone na yakutu, lu’u lu’u zinarai da dai sauransu jinjina kai sarki yayi sannan yace aje akai ma Sarauniya Nuwaira.
Amsawa tayi da toh angama ranka yadad’e nan tasake kwasar gaisuwa sannan tad’auki kwandon cikin sauri tamik’e tafita.
A chan cikin gidan sarauta wanda girmanshi zai kai girman gari guda cikin gidan ‘bangare ‘bangare ne, d’aya daga cikin ‘bangaren tanufa wanda yasha ado anzuba mashi kayan k’yale k’yale sosai komai na cikinshi abun kallo ne.
K’wank’wasa wata k’ofa tayi nan k’ofar tabud’e dakanta wata kyakkyawar macece fara shimfid’e saman kujerar zinari wasu fararen halittu zagaye da ita sai hidima suke mata.
Wannan kuyangar saurin zubewa tayi k’asa tace Allah yataimake ki Sarauniya sak’o daga Sarki.
‘Daya daga cikin kuyangita ne tazo ta amshi kwandon taje gaban Sarauniya Nuwaira ta ajiye sannan tabud’e mata.
Murmushi Sarauniya Nuwaira tayi tace ashiga da su ciki.
Tun kan tarufe baki wannan bafadiyar tata tad’auka cikin sauri ta yi cikin wani d’aki da shi…..
Tunda tadoso kanta a cikin gidan sarautar jama’ar ciki suka fara zubewa suna k’wasar gaisuwa ammah babu wanda takalla daga cikinsu haka tawuce cikin takunta me jan hankali, da idanu suka bita suna yabon kyawunta da zubin halittarta dan komai nata na daban ne kamar mahaifiyarta.
Hanyar ‘bangarenta tanufa tana cikin tafiya sai ji tayi daga bayanta ankira sunanta.
Ja tayi tatsaya dan ko bata juya ba ta san me kiran nata, tana nan tsaye wasu bak’ak’en kuyangi suka fara isowa wajen sai a lokacin tad’aga kai takallesu su dukansu duk’ar da kai sukayi alamun girmamawa.
Wata kyakkyawar budurwace bak’a sanye cikin kaya na alfarma ta iso wajen tare da sauran kuyanginta, kallonta Najla tayi nan Najma tasakar mata murmushi tace me kika shirya ma gobe da takasance ranar farin ciki agaraku fararen mayu?
Tsayawa tayi kallonta dan yanayin yadda tayi magana yasa Najla tagane akwai wani abu acikin zuciyar Najma dan ko murmushinta kagani toh tabbas na mugunta ne.
‘Daga mata gira Najma tayi tace kinyi shuru ya kamata kice min wani abu ya ke kyakkyawar farar mayya.
Sai a lokacin itama Najla tayi murmushi sannan tabud’e baki cikin siririyar muryarta me dad’in saurare tace abinda nashirya ba lallai bane kowa yasanshi musamman ma bak’ak’en mayu da basu da hurumi a cikin shagalinmu
Bushewa da dariya Najma tayi tace dakyau Najla ina son irin wannan jarumtar taki da rashin tsoro hakan yana burgeni sosai.
Murmushi kawai Najla tayi batare da ta ce mata komai ba tawuce tayi tafiyarta.
Da idanu Najma tabita tana murmushin mugunta har saida Najla ta’bulle sannan tata’ba hannunta nan Najma ta’bace ‘bat
Kuyanginta suna ganin haka nan suma duk suka ‘bace…..
Gimbiya Najla Cikin tafiyarta me jan hankali ta isa wajen wata k’ofa me siffar d’awisu wadda aka k’awatata da zinarai tana zuwa wajen k’ofar nan gashin da ke jikin d’awisun yabud’e sai ga wani had’ed’d’en parlor ya baiyana.
Taka lumtsumemen kafet d’in da ke shimfid’e daga farkon parlorn tayi sai ga wasu mata su kusan ishirin sun bayyana a zaune k’asa suna sanye da kaya iri d’aya duk sun duk’ar da kai alamun girmamawa.
Cike da nuna isa take tako nan tawuce tatsakiyar parlorn tanufi wata babbar k’ofa da wasu fararen kuyangi biyu suke tsaye suna gadi ganinta yasa duk suka zube sukayi mata sujjada, batare da ta ce komai ba tawuce tashiga cikin had’ed’en bedroom d’inta da yaji kayan alatu komai na ciki an k’awatashi da lu’u lu’u da gold, kayan jikinta tacire tafad’a cikin wani toilet wanda shima tsarinshi abun kallo ne tana shiga tafad’a cikin wani bathtube me kama da swimming pool nan wasu halitta masu kama da agwagi sukazo suka fara wanke mata jiki, kwance tayi cikin ruwan tare da maida idanunta tarufe ahaka suka dinga cud’ata saida suka wanketa tas sannan tafito daga cikin ruwan.
Shiryawa tayi cikin wata had’ad’d’ar gown wadda tabaje tana sharar k’asa, wasu ‘yanmata ne guda biyu suka bayyana a gefenta suka ce ranki yadad’e ko kina buk’atar taimakonmu
Girgiza masu kai kawai tayi nan tahad’e dogon gashinta waje guda tad’aure sannan tafito parlor cike da tak’ama take tafiya bisa kujerarta ta zinari tazauna nan tabada umurni gabad’aya halittun da suke cikin parlorn suka ‘bace sai wasu kuyangi biyu da suke tsaye suna tsaron k’ofa.
Zoben da yake manne a hannunta tafara murzawa nan wani haske yafito daga jikinshi daidai lokacin aka fara knocking d’in k’ofa wad’annan kuyangin da suke tsaye suka bud’e.
Wata hadima ce tashigo d’auke da wani k’aton tray tana zuwa d’an rissinawa tayi a gaban Gimbiya Najla sannan ta ajiye tray d’in tare da saurin duk’awa tafara k’wasar gaisuwa, kallonta kawai tayi batare da tayi magana ba nan baiwar tatashi tabud’e tray d’in da tashigo da shi, nama ne iri iri jibge a cikinshi, bin tray d’in tayi da kallo tace wannan naman duk na minene?
Baiwar cikin rawar murya tace ranki yadad’e sarauniya ce tabada umurni inkawo maki.
Jawo gashin kan baiwar tayi dak’arfi wanda dalilin hakan yasa saida baiwar tasaki k’ara, tura kanta tayi cikin tray d’in naman tace meyasa kika kawo min wannan bayan kinsan bana cin irinsu.
Cikin rawar murya tace kiyi min rai ranki yadad’e wallahi ba’ason raina nakawo maki su ba.
‘Dan guntun murmushi tayi tare da sakar mata kai tace na san ko aikin wanene wannan, yanzu ya zama dole kifita da wannan naman kije kikawo min irin wanda nake buk’ata.
Cikin sauri tad’auki tray d’in taficce, mik’ewa gimbiya najla tayi tashige fankacecen bedroom d’inta da yasha kayan alatu kamar ba a duniyar ba.
Washe gari haka ake ta shirye shirye gabad’aya garin Nairan hidima suke musamman ma idan akace dare ne dan daman indai dare ya yi mawuyacine kaga suna bacci lokacin ne mafi yawan mayun garin suke fita farauta cikin daji da safe zuwa lokacin da rana zata yi sanyi ne suke samu suyi bacci dan mafi yawansu basu cika fita in akwai rana ba musamman fararen mayu tana masu illa sosai.
A yau ko kamar sallar ko ma ace sallarsu ce kowa ya zage wajen shirya kanshi masu canza kamanni suna yi masu maida kansu siffa mekyau suna yi duk dan kowa yaga ya fi kyau.
Duk wannan hidimar da ake banda Gimbiya Najla dan ita daman chan wannan shagalin baya burgeta.
***** ****
Sarauniya Nuwairah tafe take kuyanginta suna take mata baya duk inda suka ratsa mayu ne suke zubewa suna kwasar gaisuwa saidai tabisu da murmushi ahaka suka isa ‘bangaren Sarki Nawar suna zuwa wajen k’ofa gabad’aya masu tsaron k’ofar da kimaninsu ya kai su talatin suka duk’a suka kwashi gaisuwa sannan aka bud’e mata k’ofa, kuyanginta a nan suka ja suka tsaya inda ita kuma tashiga ciki, tana shiga tasamu wata bak’ar kuyanga tsaye a bakin k’ofa hakan yasa tagane Sarauniya Wailah tana ciki, kuyangar saurin duk’awa tayi tagaisheta nan Sarauniya ta amsa sannan tawuce bisa d’aya daga cikin k’ayatattun kujerun Gold da suka k’ara k’awata parlon tazauna.
Tana zama bata dad’eba sai ga Sarauniya Wailah ta fito daga cikin bedroom d’inshi saurin mik’ewa Nuwairah tayi tare da sakar mata murmushi.
Ko inda take Sarauniya Wailah bata kalla ba tawuce tatafi da idanu Nuwairah tabita har lokacin fuskarnan tata tana shimfid’e da murmushinta me k’ara k’awatar da kyawun fuskarta sannan tajuya tanufi cikin bedroom d’in mijin nata.