KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Jin buk’atar da suka zo da ita yasa jikin sarki yayi sanyi sosai dan ya san tunda har suka furta toh dole hakan za’ayi..
Tsoho Abnar ne yace ranka yadad’e ya kamata kace wani abu kaima.
Murmushi Sarki Nawar yayi tare da safke ajiyar zuciya yace shikenan na yadda da wannan shawarar taku..
Cikin jin dad’i boka Gobar yace yauwa ranka yadad’e mungode sosai da kafahimcemu idan ba damuwa ya kamata akira mana su musanar da su buk’atar da mukazo da ita agaresu dan su kasance cikin shiri kafin lokacin da zamu yanke tafiyar…
Sarki Nawar tura wasu Fadawanshi yayi suje suyo mashi kiran Gimbiya Najma da Najla, bayan kamar minti goma suka dawo suka sanar da sarki sun isar da sak’onshi….
Gimbiya Najma ce tafara shigowa cikin fadar nan fadawa suka fara kwasar gaisuwa batare da ta kulasu ba tawuce tana yatsina taje tazauna kujerarta da tasaba zama tun tana k’arama kallon mahaifin nata tayi tad’auke kai batare da ta ce komai ba dan har yanzu fushii take da shi babu wanda yatanka mata bata fi minti biyar da zama ba saiga Gimbiya Najla ta shigo cikin shigarta ta alfarma gabad’aya mutanen fadar suka duk’e suna gaisheta kamar yadda sukayi ma ‘yar uwarta fuskarta d’auke da murmushi tawuce tanufi inda mahaifinta yake zaune yana kallonta, Gimbiya Najma ranta ‘baci yayi lokacin da taga Najla ta shigo fadar chan kuma sai tayi murmushin mugunta tazuba mata idanu tana kallonta har saida Najla tazo daidai wajen matattakalar da zata taka tahau inda kujerar mulkin mahaifinta da tasu take nan takubce sai gata k’asa sarkine yafara mik’ewa tsaye kafin sauran fadawa sumik’e
Wani irin rad’ad’in zafi ne taji ya ziyarci yatsanta saurin fiddo k’afar tayi daidai da jini ya fara fitowa daga yatsanta wani irin haskene yayi saurin fitowa daga idanun Tsoho Abnar yadaki k’afanta sai ga wani bak’in jini ya fara fita, Najma da sauran Fadawa har sun zaro ido waje ammah suna yin tozali da bak’in jini duk sai suka safke ajiyar zuciya wasu daga cikin fadawan ne suka nufo wajen cikin sauri, Najla na ganinsu tad’aga masu hannu alamun kar su iso dan haka duk suka ja suka tsaya..
Sarki da ke a rud’e rik’e k’afar yayi yace sannu Najla bari induba maki k’afar, juyawa tayi takalli Najma da tahakimce a saman kujera tana murmushi kallonta tayi na d’an lokaci kafin daga baya tajuyo takalli mahaifin nata da duk yanuna damuwa akan ‘yar fad’uwar da tayi murmushi tayi ciken nuna juriya tace Abba ba wani zafi ciwon bari insa magani
Hannunshi yasa yadafe inda jinin yake fita yace a’a Najla na san da zafi bari insa maki magani yadda zai daina radad’i
Murmushi kawai tayi batare da ta ce komai ba nan sarki nawar yarik’e wajen da taji ciwo yayi mata tsafi nan wani farin k’yalle yabayyana a hannunshi yasa yad’aure mata nan take tadaina jin rad’ad’i a wajen
Rik’eta yayi yataimaka mata tamik’e yace ko inmaidake turakarki kikwanta kihuta?
Ganin yadda idanun mayu duk suke a kansu yasa tagirgiza kai tace A’a Abba na daina jin zafin wajen..
Kamata yayi sukaje tazauna saman kujerarta sannan shima yakoma saman tashi kujerar nan fadawa suka dinga mata sannu ammah banda Najma da har lokacin murmushi bai kaudu daga fuskarta ba
Boka Abnar ne yabada izini aka goge jinin da Najla tazubar, bayan komai ya natsa Boka Gobar yayi gyaran murya yace na san zakuyi mamaki akan kiran da Sarki yayi maku toh ba akan komai bane sai dan kawai mun yaba da jarumtarku dan ku d’in zaratan mata ne masu kamar maza wannan dalilin ne yasa muka nemi amincewar sarki akan aturaku dajin kursad ku farauto mana dodo gumar ba wai gawarshi mukeso ba kunnenshi na ‘barin dama kawai mukeso kuyanko mana dan munsan ba k’aramin abu bane kashe Dodo Gumar dan shi d’in matsafine sosai na san babu wanda bai san tarihinshi ba a cikinku duk wanda yashiga dajin mawuyacine yafito a raye ammah ku bana jin ta taku nasan gunki gostan zai taimaka maku, ya kuka ce akan haka?
Tun da aka fara bayani su dukansu idanu suka zuba ma Boka Gobar suna saurarenshi har saida yakai aya sannan Najma tayi murmushi tace toh menene ladar duk wanda yasamu damar kasheshi ko yaciro kunnenshi na dama?
Boka Gobar murmushi yayi yace akwai lada me tsoka da za’a bashi sannan ta haka ne zamu ida gasgatarwa zaku iya mulkin k’asar nan bayan ran sarki….
Najla murmushi tace wannan ba wani abu bane ni da ‘yar uwata zamu je dajin kursad zamu kawo maku abinda kuka buk’ata
Mamakine yakama sarki Nawar dan baiyi tunanin Najla zatayi saurin amincewa da hakan ba ammah yaga fuskarta bata tare da wata damuwa..
Murmushin yak’e Gimbiya Najma tayi tace wannan haka yake mu zamu kawo maku sannan ta haka ne za’a gane tsakanin ni da ‘yar uwata wacece tafi jarumta…
Boka Abnar ne yace wannan haka yake saidai inaso kusan cewa ba kowane sihiri bane yake kama Dodo Gumar sai kun had’a da k’arfin damtse
Ajiyar zuciya sarki nawar yasafke yace bana jin ‘ya’yana akan hakan nasan zasu iya…
Toh shikenan ya kamata atsayar da shawarar lokacin tafiyar sannan kuma su yakamata sufitar da lokaci tunda sune masu zuwan,,, cewar Boka Gobar.
Gimbiya Najma ce tayi karaf tace mun tsayar da sati me zuwa rana irin ta yau,
Tsoho Abnar ne yace shin hakan da ‘yar uwarki tace ya yi maki Gimbiya Najla?
Murmushi tayi tace hukuncin da ‘yar uwata tayanke shine daidai…
Gabad’aya mayun da ke cikin fadar saida suka jinjina ma wad’annan matan ganin ko kad’an basu nuna tsoro atare da su ba sannan babu alamar karaya, shi dai sarki duk wannan abun da ake yak’e kawai yake hankalinshi atashe yake dan bai san yadda zata kasance ga ‘ya’yan nashi ba…..
Bayan an gama tattaunawane aka sallami kowa nan sarki yakama Gimbiya Najla dakanshi yarakata har turakarta a chan ne yanuna mata damuwarshi akan tafiyar da zasuyi, saidai tayi murmushi tanuna ko a jikinta wannan ba wani abu bane.
Ganin yadda bata damu ba yasa Sarki Nawar yad’an kwantar da hankalinshi saidai yana jin d’iyartashi sosai yana tsoron yarasata….
Bayan an tashi fada ne Boka Gobar yaja Najma gefe d’aya yana murmushi yace jikata ina fatan hakan ya yi maki babu wata matsala?
Bushewa da dariya Najma tayi tace ina da masaniya sosai akan hakan da kayi kakana sannan nasan zaka taimaka min..
Jinjina kai yayi yace wannan haka yake zuwa gobe kizo gida kisameni akwai abinda nakeso mutattauna dan bana so aganmu tsaye a nan wajen azargi wani abu.
Amsawa tayi da toh nan sukayi sallama kowa yakama gabanshi…
_*Part 1 Free pages ne*_
_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*