KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

_Sis Nerja’art_
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA…*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 8*
Gimbiya Farha zaune take a d’akinta na kwalliya, inda ma’aikatanta masu kula da kwalliyarta suna tsaye wajen kanta suna ta gyara mata fuska, kuyanga guda ce take rik’e da babban madubi Gimbiya Farha tana duba fuskartata da ake ta gyarawa, ana cikin kwalliyar Sarauniya Zaiba taturo d’akin tashigo tsayawa tayi fuska d’auke da murmushi tana kallon d’iyartata, ma’aikatan yunk’urin duk’awa sukayi zasu gaisheta tace a’a sucigaba da abinda suke nan tazo tazauna, Gmbiya Farha sawa tayi aka tsayar da kwalliyar tad’ago tana kallon mahaifiyarta da take ta faman murmushi, itama mayar mata da martanin murmushin tayi tace Mamana na yi kyau?
Jinjina kai Sarauniya Zaiba tayi tace kinyi kyau sosai ‘yah ta wannan kwalliya haka da ake ta tsantsarawa sai ina?
Turo baki tayi tace ina fa kawai yi ne saboda Yarima inaso ayi min kwaliyar da zata ja hankalinshi yaji na burgeshi
Washe baki Sarauniya Zaiba tayi tace dak’yau ‘yata kinyi tunani me kyau nima kaina zan so hakan dan bana da buri da yawuce inga aurenki da yarima
Cikin jin dad’in maganar mahaifiyartata tace dagaske kike mama kema kina son aurena da yarima?
Me zai hana ai ni sai na fi kowa murna idan hakan ya kasance duk wannan lalla’bawar da kikaga ina yi mashi ina yi ne kawai dan insamu yasoki
Cikin shagwa’ba tace Ammah Mama yarima ya cika jin kan tsiya kina gani ko kallon kirki bai cika yi min ba sannan kema d’in d’auke maki kai yake kece kawai kike binshi, ahaka kina ganin zai amince yasoni, ni fa wallahi shi nakeso
Haba ‘yarlele menene abun tada hankali kisha kurumunki indai ina nan baki da miji sai Yarima kinga maida hankali agama maki kwalliyar kifita kafin yadawo nasan shima sai kwalliyar nan ta burgeshi dan kina da kyau sosai saidai yadanne kafurar zuciyarshi yak’i nuna hakan
Cikin jin dad’i Gimbiya Farha tace nagode sosai Mamana, mik’ewa Sarauniya Zaiba tayi tafita tabasu waje dan a ida kwalliyar….
Had’ewa tayi cikin wata kyakkyawar gown ta material wadda tasha kwalliya tad’aura alk’yabba sama tsayawa tayi a gaban mirror tana sake duba kanta tana k’yasa irin kyaun da tayi tana hango yadda Yarima Ayran zai dinga kallonta idan yaganta,,, wata kuyanga ce tashigo d’akin dagudu babu ko neman izini juyawa Gimbiya Farha tayi a fusace zata rufeta da fad’a nan Kuyangar tayi saurin zubewa k’asa tace ranki yadad’e ga motar Yarima nan tana shigowa cikin gida…
Tana jin haka juyawa tayi cikin sauri tafita nan Kuyanginta suka take mata baya inda biyu daga cikinsu suka rik’e mata doguwar alk’yabbarta da ke sharar k’asa cikin sauri tafita daga cikin turakarsu daidai da Yarima Ayran ya faka motarshi a chan wajen da aka tanada na ajiye motoci, zaune yayi a cikin motar yana waya hakan ne yaba Gimbiya Farha damar zuwa wajen motar tashi…
Isowarta ya yi daidai da gama wayarshi yabud’e motar yafito tsayawa yayi yana kallonta ganin haka yasa tagyara tafiyarta ta iso fuska d’auke da murmushi ganin yadda yake kallonta cikin ranta tace daman nasan indai kaga wannan kwalliyar sai ka k’yasa
Kuyanginta ne suka zube suna kwasar gaisuwa bai amsa masu ba sai ma cigaba da kallon Gimbiya Farha da yayi
‘Dan langwa’be kai tayi tare da yin fari da idanu tace sannu da dawowa Yarima daman na fito ne zan je apartment d’in Ummi shine naga ka dawo nace bari inzo inmaka sannu da dawowa.
Wani irin kallo yayi mata a dunk’ule kamar wanda baya son yin magana yace Nagode sannan yagifta ta gefenta zai wuce tayi saurin cewa Yarima daman…..d’aga mata hannu yayi batare da ya ida jin abinda zata ce ba yawuce yanufi ‘bangarenshi
Wani irin k’ululun bak’in cikine yatsaya ma Gimbiya Farha ganin irin dizgin da Yarima yayi mata a gaban kuyanginta da Fadawanshi da suke tsaye chan gefe suna jiran shi,,,
Juyawa tayi cikin ‘bacin rai dasauri takoma ‘bangarensu tana zuwa turakar mahaifiyarta tashige batare da ta nemi izini ba Sarauniya Zaiba da ke zaune tana shan fruits sai ganin d’iyartata tayi kamar anjefota tana zuwa tafad’a jikinta tare da fashewa da kuka
Hankalin Sarauniya Zaiba tashi yayi tace lafiya Farha me yafaru? Wanene yata’ba ki?
Cikin sheshek’ar kuka tace Mama Yarima ne..!
Rai a ‘bace tace tashi kifad’a min me Yariman yayi maki wallahi indai ta’baki yayi bazan ta’ba hak’ura ba
‘Dago kai tayi cikin kuka tace ba shi ne ba dan kawai na yi mashi magana shine yawulak’antani a gaban kuyangina yawuce yayi tafiyarshi
Cikin d’aga murya tace Kam bala’i yariman dakanshi yawulak’anta min ke har kika zubar da hawaye, toh wallahi kibarni da shi inma yana nufin baya sonki toh ya yi k’arya a tafin hannunmu yake ya zame mashi dole yasoki, kinga yi shuru kidaina kuka indai ina raye bazan ta’ba bari kizubar da hawaye ba wanene Yarima da har zai wulak’anta min ke
Goge hawayen fuskarta tayi tace wallahi Mama ina sonshi.
Kibarni da shi Farha ya zama dole shima yasoki shi ba ma jin dad’inshi bane ya samu kyakkyawar mace kamarki tana sonshi
Turo baki Gimbiya Farha tayi tace ammah ai shima yana da kyau ga aji da kud’i
Buge mata baki Sarauniya Zaiba tayi tace rufe min baki dan yana da kyau sai kin wani yaba ke kike ja ma yana maki wulak’anci ina ruwanki da kyaunshi na ki kyaun yadace kiyaba..
Turo baki gaba Farha tayi alamun fushi
Kwantar da murya Sarauniya Zaiba tayi cikin lallashi tace Farha kiyi hak’uri kinji zan yi magana da memartaba.
A’a Mama kar kiyi mashi magana yanzu kibari sai na fad’a ma Yarima ina sonshi idan har bai aminceba sai afad’a ma memartaba
Murmushi tayi tace toh shikenan ‘yah ta yadda kikeso ai haka za’ayi
Itama murmushin tayi tace Yauwa Mamana yanzu bari intashi inje wajensu Afrah
‘Bata fuska Sarauniya Zaiba tayi tace kedai bakiji tun kina k’arama nake son nisantar da ke da wad’annan ‘ya’yan wannan aljanar matar ammah kin k’i kidaina shige masu
Dariya Farha tayi tace kai Mama yanzu Ummi itace aljanah
Yatsine fuska tayi tace aljanah ce mana inba aljannu ba su wa suke da irin wannan kyaun nata..
Yadda Sarauniya Zaiba tayi maganar ya ba Gimbiya Farha dariya sosai saida tadara sannan tace tana dai da kyau dan kyaunta ne Yarima yad’akko saisa gashinan masha Allah kamar mutum yasace yagudu.
Tsaki Sarauniya Zaiba taja tace ai saiki tayi.
Mik’ewa tayi tace Mama bari inje kisa ahad’a min ferfesun d’awisu yau shi nake sha’awar ci da dare.
Kar kisamu damuwa dole ayi miki abinda kikeso.
Murmushi tayi tace yauwa Mamana sai na dawo….
______******_____
Zaune suke suna kallon wani Series film Gimbya Farha tashigo su dukansu d’ago kai sukayi suna kallonta ganin wani irin had’uwa da tayi murmushi tasakar masu tace twins ya kuka ganni?
Kusan a tare sukace kin fito a Gimbiyarki matar Yarima
‘Dan guntun tsaki taja tace kudaina tuna min wallahi halin Yarima sai shi duk wannan gayun da naci ammah bai sa yatsaya yakalleniba bare har yayaba
Gimbiya Afreen ce tace kai Sis kika sani ko yana da wadda yake so?
Harararta Farha tayi tace kince haka daman tunda kina k’aunar yayan naki sosai kin saba goya mashi baya nidai babu ruwana ban damu da hakan ba dan ni ina sonshi taya ma za’ayi na gida bai k’oshi ba aba na waje