KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Su dukansu dariya suka sa tace kunga kutaso muje ‘bangarenshi watak’il yasaurareni idan yaga tare nake da ku
Zaro idanu sukayi waje sukace mu suwa?
Ta’be baki tayi tace ku k’annenshi ni ba wai maganar son da nake mashi zanyi mashi ba ko da ace murmushinshi nagani zan ji dadi, dan Allah kutaso…
Mik’ewa sukayi gabad’aya suka fito nan kuyangi suka so sutake masu baya ammah suka ce a’a suyi zamansu, a jere suke tafiya har suka isa ‘bangaren Yarima Ayran inda Bodyguard d’inshi suke tsaye a bakin k’ofa suna zuwa suka ce masu suyi hak’uri Yarima ya bada izini kar abar kowa yashiga dan hutawa zaiyi
Su dukansu kallon juna sukayi sai kuma suka juya dan sun san basu da damar shiga tunda har yabada umurni memartaba ne kad’ai zai iya shiga idan ya so….
Yarima Ayran kwance yake saman makeken gadonshi da yak’ara k’awata mashi bedroom d’inshi da komai yaji dan anzuba mashi kaya masu kyau da tsada kamar ba gobe ba ma iya nan ba hatta parlonshi ya tsaru k’arshen tsaruwa kamar ba a Nigeria ba
Idanun nan nashi a lumshe suke kamar me yin bacci ammah a zahiri ba baccin yake ba…yana a haka d’aya daga cikin wayoyinshi tafara ringing ahankali yabud’e idanunshi yajawo wayar batare da ya duba me kira ba yakashe wayar gabad’aya sannan yatashi yafito parlor a wajen da computer shi take ajiye yanufa yaja kujera yazauna yakunnata yahau saman network dan gabatar da wani aiki nashi dan shi d’in Allah ya yi shi me yawan bincike akan aikinshi…
Kiran sallar la’asar ne yasa yatashi saida yak’ara watsa ruwa sannan yafito sanye cikin k’ananun kaya da suka k’ara fiddo mashi kyaun shi
Masallacin da ke cikin gidan sarautar nasu yaje yayi sallah bayan sun gama ne yatsaya gaisawa da mutane kamar yadda yasaba kafin daga baya yawuce yanufi turakar mahaifiyartashi yana shiga babu kowa a parlor sai kuyangi da bayinta suna ganinshi suka zube jiki yana rawa suka fara kwasar gaisuwa batare da ya amsa su ba yawuce yanufi bedroom d’inta dan ya san indai bata parlor toh tana cikin bedroom yana shiga yasameta zaune saman darduma tana addu’a dan haka yaje kusa da ita yazauna har saida tashafa sannan shima yashafa
Juyowa tayi tana kallon d’an nata fuska d’auke da murmushi tace Ayran an dawo ko?
Shima murmushin yayi yace Eh Ummina yau na yi missing d’inki sosai
Shafa kanshi tayi tace nima haka ina fata dai ka ci abinci
A maimaikon yabata amsa sai ma kwantar da kanshi da yayi a saman cinyarta ganin haka yasa tadinga shafa mashi kai shi kuma yamaida idanunshi yalumshe, fuskarta d’auke da murmushi tace Ayran ka san dai bana son kana zama da yunwa ya kamata kadinga cin abinci kar kajawo ma kanka wani ciwon ko kuma kai likita ne ka san komai akan hakan
Murmushi kawai yayi batare da ya ce komai ba
Idanu ta tsurra ma fuskar d’an nata da idanuwanshi suke a lumshe cikin ranta tana mamakinshi kwatakwata magana bata dameshi ba wani lokacin indai za’ayi mashi magana toh murmushi kawai zaiyi shine amsar da zai bayar, Sarauniya Marwa da Maimartaba abun tun yana damunsu har yadaina damunsu dan sune kad’ai suka fahimci halin d’an nasu inda wasu mutanen suke mashi kallon girman kai ne gareshi sai wanda yazauna da shi ne sosai yake d’an fahimtar ba haka ba…
Shigowa su Afreen sukayi d’akin suna k’wala ma Ummin tasu kira ganin Yarima Ayran yasa suka ja suka tsaya batare da ya tashi daga jikin mahaifiyartashi ko yabud’e idanunshi ba yayi masu nuni da hannu alamun sufita
Juyawa sukayi cikin sauri suka bar d’akin a parlor suka zauna Afrah tace oh ni su Bro ba’a girma shi kullum yana manne da Ummi yayi ta zuba shagwa’ba ko mu bama yin yadda yake
Ta’be baki Afreen tayi tace ai duk su Ummi da Abiy ne suke shagwa’bashi mu yazo yayi aure muhuta da wannan mulkin nashi da yake nunawa har akanmu
Uhm ni ba ma wannan ba Sis abinda yake bani mamaki da shi wani lokacin kamar ba shi ba sai yasake muyi hira ammah daga inda mulkin yamotsa mashi toh shikenan muma kanmu sai ya shafemu…
Dariya Gimbiya Afreen tayi tace ni ko Sis halin Bro yana burgeni sosai komai na shi cikin tak’ama da nuna isa yakeyinshi zan so inga matarshi ko ya zatayi…
Rik’e baki Gimbiya Afrah tayi tace kirufa mana asiri kar yaji kinga taso muje turakar yakumbo tun d’azu ta aiko akiramu na mance ban fad’a maki ba lokacin kin shiga d’akin research kina asssignment…..
Ummi kallon fuskar d’an nata tayi tayi Ayran ya kamata kadinga ba ‘yan uwanka lokaci suna zama suyi hira da kai kaine kad’ai d’an uwansu idan baka sake masu ba wa zakayi mawa
Ahankali yabud’e idanunshi fuska d’auke da murmushi kamar ba zaiyi magana ba sai kuma chan yace Ummi yaran ne sun cika surutu sosai kinsan ni kuma bana son hayaniya…
Duk dai da haka kadinga d’an basu lokaci ta haka ne zasuyi sabo da kai.
Daga kai kawai yayi alamun toh sannan yamaida idanunshi yalumshe…..
Gimbiya Afrah da Afreen ‘bangaren kakarsu suka nufa suna shiga suka sameta zaune a parlor tana cin kwad’on zogale inda masu yi mata hidima suke tsaitsaye suna jiran tabasu umurnin suyi mata wani abu, tana ganinsu murmushi tayi tace ‘yan biyu ikon Allah kamar kun san tunaninku nake a yanzu haka cewa nake zan aika akai maku kwad’o gashi na sa and’iba maku acikin kula..
Zama sukayi kusa da ita suna yatsine fuska sukace kakus wannan kuma menene shi haka kamar ciyawa?
Ta’be baki tayi tace shi dai ne uwarku da ubanku suka ci suka girma magulmatan yara
Murmushi sukayi atare sukace Allah yaja da ran yakumbo tuba muke
Sharesu tayi tacigaba da cin kwad’onta ganin haka yasa sukace toh shikenan tunda baki farin cikin zuwanmu bari mutashi mukoma inda muka fito
Ture plate d’in zogalen tayi nan wasu mata sukayi saurin zuwa suka tara mata wani kwano aka tsiyaya mata ruwa tawanke hannunta tare da kurkure baki bayan ta gama ne tace ai idan baku tafi ba ni zan koreku dan ban iyawa da iya yinku kokuma gwara ku kan wanchan uban d’an jin kan yana tafiya yana k’ambo ya iya yayi aure ya k’i ya kama yai ma mutane zaune inma banda abun Memartaba ai da za’ba mashi mata akayi tunda shi ya tsaya ruwan ido shi adole ga mai kyau me farin jinin ‘yanmata
Gimbiya Afrah da Afreen ko me zasuyi inba dariya ba dan sosai maganarta tabasu dariya
‘Dan guntun tsaki taja tace ku dai kuka sani kunji da shi gaskiya ce dai sai na fad’eta ku ma d’in banga zaman da kuke acikin gidan nan ba har yanzu bakuyi aure ba
Afrah kallon Afreen tayi tai mata nuni da idanu alamun sutashi sutafi, d’an rissinawa sukayi sukace Allah yaja da ranki tsohuwa mun barki lafiya..
Gyara zama yakumbo tayi tace asauka lafiya marassa son afad’i gaskiya.
Batare da sun ce komai ba suka mik’e suka fito suka bar turakar Yakumbo suka koma tasu, yatsina fuska Afreen tayi tace wallahi Sis yakumbo ta sa mana idanu dayawa kullum batada magana sai ta mun k’i yin aure duka fa nawa muke yanzu fa muke 200level a karatunmu ga ma Sis Farha nan itada take final year ai ita yakamata ayi ma maganar aure ba mu ba..
Ke kike ma bin ta maganar yakumbo ni yanzu duk abinda zata ce baya damuna dan babu auren da zanyi sai na gama karatuna….
Knocking d’in k’ofar da akayi ne yasa suka bada izinin ashigo
Wata kuyanga ce tashigo taduk’a takwashi gaisuwa cikin girmamawa sannan tace ranku yadad’e ko akwai abinda kuke buk’atar akawo maku…
Afreen ce tace kije kikawo mana fruit salad..
Amsawa tayi da angama ranki yadad’e sannan tamik’e cikin sauri tafita…..