KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

_*Part 1 Free pages ne*_
_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
_Sis Nerja’art✍????_
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 9*
**MASARAUTAR NAIRAN**
Sarki Nawar tun lokacin da aka yanke hukuncin tafiyar su Gimbiya Najla dajin Kursad hankalinshi yake a tashe a duk lokacin da yakasance shi kad’ai toh baida aiki sai shiga damuwa ba dan komai ba sai dan Najla dan ya fi tausaya mata akan Najma dan baya jin ta Najma ya san tana da k’arfin tsafin da zata iya tseratar da kanta daga hannun Dodo Gumar….
Yau ma dai yana zaune a cikin d’akinshi shi kad’ai yana wannan tunanin Najla tashigo tasameshi ganin yanayin damuwa atattare da fuskarshi yasa hankalinta yatashi tataka ta isa wajen da mahaifin nata yake zaune
Sarki Nawar d’ago kai yayi ganin itace yasa yasakar mata murmushi tare da rik’o hannunta yazaunar da ita gefenshi.
Cike da nuna damuwa tace Ya Abbana hak’ik’a ganinka a cikin wannan yanayin ya d’aga min hankali sosai kuma na san ba dan komai kashiga wannan damuwar ba sai akan tafiyar da zamuyi Dajin Kursad.
Ajiyar zuciya yasafke yace tabbas maganarki hakane Najla ina tunanin tafiyar da zakuyi ban saniba ko zaku dawo gareni ko bazaku dawo ba saboda na san had’arin da yake tattare da Dodo Gumar musamman ma ke nafi tausaya mawa sama da ‘yar uwarki.
Murmushi tasakar ma mahaifin nata tace Abba kacire kowace damuwa a cikin ranka ni da ‘yar uwata zamuje mudawo lafiya ko da sau d’aya zuciyata bata karaya ba akan tafiyar da zamuyi ni na amince zanyi ba wai dan insamo abinda ake buk’ata ba sai dan kawai intaimaka ma ‘yar uwata ita tasamo.
Tsayawa Sarki Nawar yayi yana binta da kallon mamaki yakasa cemata komai.
Kwantar da kanta tayi saman k’irjinshi tace Abbana zamu dawo gareka addu’arka kawai muke buk’ata karok’ar mana Dodo Gostan dan neman nasara.
Shafa kanta yayi yace kar kidamu ina akan haka a kullum d’iyata.
Lamo tayi a jikinshi tamaida idanunta talumshe sai kuma chan tad’ago tace Abba ina da tambaya akwai wani abu da yad’aure min kai ranar da naje fada har nafad’i.
Fuskar Sarki Nawar canzawa tayi dan tabbas ya san tambayar da zatayi mashi, janyeta yayi daga jikinshi yace kar kidamu da abinda yafaru ya ke ‘yata dan hakan ba wani abu bane…
Turo k’ofar da akayine yasa duk suka juya suka kalla, Sarauniya Wailah ce tashigo tare da kuyanginta ganinsu yasa taja tatsaya tana jifan Najla da mugun kallo.
Najla zame jikinta tayi daga na mahaifin nata tace Abba bari inje akwai abinda nakeson yi yanzu.
Toh shikenan Najla.
Mik’ewa tayi tsaye tanufi inda Sarauniya Wailah take tsaye d’an rissinawa tayi tagaisheta a maimakon ta amsa sai tawurga mata wata muguwar harara, murmushi kawai Najla tayi tara’ba ta gefenta tawuce…
Tana wucewa Sarauniya Wailah tataka cikin sauri ta isa wajen da Sarki Nawar yake zaune tazauna daga gefenshi tace shin miyasa kake fifita Najla akan Najma meyasa kafi janta a jiki?
Kauda kanshi yayi gefe yace wannan tambayar ke kikasan amsoshinsu ni dai abu d’aya nasani dukansu ‘ya’yanane kuma ina k’aunarsu.
Bud’e baki tayi zatayi magana yatari numfashinta yace kirik’e maganar da take a bakin ki ni a yanzu zan fita zamuje Farauta, mik’ewa yayi batare da ya jira jin abinda zata ce ba yaficce….
****
Gimbiya Najma ce zaune a cikin d’akin tsafin kakanta boka gobar fuskarta d’auke da murmushi tace Kakana shin ya kake gani game da wannan tafiyar da zamuyi ni da ‘yar uwata?
Dariya Boka Gobar yayi yace ina ganin nasara atattare da ke dan a yanzu zan fara tsumaki da wani sabon tsafi kafin lokacin tafiyar naku yayi saboda shiga dajin kursad sai da shiri saboda had’arin da ke tattare da dodo gumar ya kasance sihirtaccen Dodo wanda sihiri baya kama shi kusan shekarunshi dubu d’aya kenan a cikin dajin duk wanda yasaki yashiga saidai afito da gawarshi inma an samu gawar ta shi dan cinyewa yake, ammah ina ji akwai nasara atattare da zuwan da zakuyi ke da ‘yar uwarki idan kuka had’a k’arfi zaku samo abinda ake buk’ata.
‘Bata fuska tayi tace wannan ne kuma bazai yuwu ba bazan iya had’a k’arfi da ita ba saboda na zarceta wajen komai ni fatana idan har muka shiga dajin tamutu a chan ni kad’ai indawo hakan ne zai sa hankalina yakwanta insamu nutsuwa dan ganinta da nake raina yana ‘baci sosai.
Katseta yayi yace me kike ci na baka na zuba ai indai ina raye babu wanda zai mulki k’asar nairan in ba ke ba sannan nima yana daga cikin dalilin da yasa nakeso kuje tare da ita yadda zata halaka a chan, ke dai kiyi k’ok’ari kisamo mana kunnen dodo gumar
Murmushin jin dad’i tayi tace kar kadamu kakana ni zan kafa tarihi a k’asar nan yazama ni ce farkon wadda zata farauci rayuwar Dodo Gumar.
Shafa kanta yayi cikin jin dad’in kalamanta yace na san zaki iya ya jikata a yanzu bari mufara aikin namu, mik’ewa yayi yad’akko wani kwano cike da jini yazo yana zagayeta yana karanta wasu d’alasimai, maida idanunta tayi tarufe tana ji yashek’a mata jinin a saman kanta……..
**** ****
Gimbiya Najla ce tafe ita da kuyanginta ta sha ado bayan ta je wajen mahaifinta a hanyarta takomawa turakarta suka had’u da Gimbiya Najma tana tafe tare da nata bak’ak’en kuyangin.
suna zuwa gab da juna duk suka ja suka tsaya nan kuyanginsu duk suka sunkuyar da kansu k’asa, Gimbiya Najla tafara sakar mata murmushi, da mamakinta sai ganin Najma tayi ta mayar mata da martani sannan tacigaba da kallonta bud’an bakinta sai cewa tayi Kyakkyawar farar mayya wadda take tak’ama da kyaunta shin ko akwai shirye shiryen da kike na wannan tafiyar da take fuskanto mu acikin dajin Kursad?
Murmushi Najla tayi a karo na biyu sannan tace shirye shirye yana wajenki Najma ni bana shirin komai.
Murmushin mugunta Najma tayi tace daman shiri ai na jarumai ne irina ba wai irinku ba, na san nasara tana tare da ni idan har muka shiga dajin kursad na san nice zanyo nasarar samo abinda ake buk’ata shawara d’aya zan baki itace idan har kina son cigaba da rayuwa kije kifad’a ma su mahaifinmu bazaki iya wannan tafiyar ba saboda bakida jarumta irin wadda ake so.
Murmushi Najla tayi batare da ta ce komai ba tagifta ta gefenta tawuce…