KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Da idanu Najma tabita tana jin wani irin haushi dan ko tafiya taga Gimbiya Najla tana yi tana kararraya sai abun ya bata haushi taga kamar da gangan take dan ta ga tana da zubi me kyau, chan kuma sai tayi murmushi ahankali tace Najla kwanakin mutuwarki sun fara tsayawa……
Tafiya sai k’ara matsowa take ana gobe ne zasu shiga dajin Kursad Sarki yasake tara yaran nashi a cikin fada da tacika da jama’a kowa ya laharta dan labarin shigar da su Gimbiya Najma zasuyi dajin Kursad ya zagaye duka kewayen k’asar Nairan.
Bayan sun hallara ne sarki yasake sanar da mutane abin mamakin da ‘ya’yanshi zasuyi wanda duk cikin garin nairan anrasa wanda zai iya shiga dajin kursad, nan ma akaita surutu ana mamakin jarumtar ‘ya’yan sarki da rashin tsoronsu…
Bayan nan Sarki yajuya ga yaran nashi yace shin ko akwai wani temako da kuke buk’ata daga garemu game da tafiyar da zakuyi gobe?
Gimbiya Najma ce tayi saurin girgiza kai tace bamu buk’atar taimakon komai.
Juyawa yayi ga Najla tun kan yayi magana itama tagirgiza kai.
Ajiyar zuciya yasafke yace toh shikenan saidai ina k’ara tunasar da ku akan had’arin da ke cikin dajin Kursad ya kamata idan kun shiga kuhad’a kanku kuyi komai tare dan samun ku’buta da rayuwarku.
Gimbiya Najma girgiza kai tayi tace ko da bamu had’a kawunanmu ba babu d’aya daga cikinmu da ita kad’ai bazata iya tunkarar dodo kursad ba,,, tak’arashe fad’i tare da juyawa takalli Najla tace ko ‘yar uwata?
Murmushi Najla tayi tace hakane Abbana.
Shima murmushin yayi yakoma bisa kujerarshi yazauna.
Tsoho Abnar ne yace toh shikenan zaku iya tashi kuje ku ida shirye shiryenku dan bazamuso musan shirin da kowa take ba dan munsan kunyi shiri na musamman, ammah kafin nan ko kuna buk’atar akawo maku mutane kuci kurwa da zuciyarsu sannan kusha jininsu dan kuk’ara jin k’arfin jikinku?
Gimbiya Najma ce tace Eh zan so haka.
Juyawa yayi ga Najla takauda kanta gefe tace bana buk’atar komai.
Murmushi tsoho Abnar yayi yace toh shikenan hakan ya yi…
Bayan angama tattaunawa suka tashi kowa yakama gabanshi, da marece Sarki Nawar yashiga turakar Gimbiya Najla yasameta kwance saman makeken gadonta ta d’age kai sama kamar me tunanin wani abu, ganin mahaifin nata yasa tatashi zaune tana murmushi.
Zuwa yayi yazauna kusa da ita tare da rik’o hannunta yana kallon zobunanta guda biyu d’aya na tsafinta wanda yakasance kariya agareta gudan kuma na gadon su wanda yake tun kaka da kakanni yamallaka mata shi, cire mata na tsafin yayi yasafko k’asa yazauna yanad’e k’afafunshi, runtse idanunshi yayi yana rik’e da zoben gam nan yafara karanto wani irin yare me kama da yaren china nan take wuta tabayyana a hannunshi sakin zoben yayi k’asa nan wutar tazagaye zoben cigaba yayi da karatun d’alasiman ita dai Najla tana zaune saman gado tana kallonshi
Ya dad’e a haka kafin daga baya yabud’e idanunshi nan wutar tamutu zoben yayi jajir da shi, huru tafin hannunshi yayi wani farin ruwa yabayyana yad’auki zoben yarik’e a hannunshi me d’auke da ruwan nan hayak’i yafara tashi saida hayak’in yadaina fita sannan ruwan ya’bace yajuyo yayi yakalli Najla yarik’o yatsanta yasaka mata zoben, har ta bud’e baki zatayi magana yayi mata nuni da tayi shuru dan haka taja bakinta tayi shuru tana kallon mahaifin nata batare da ya ce mata komai ba yamik’e yafita daga d’akin…
Kallon zoben tayi taga babu alamun canzawa a tare da shi wannan jan da yayi saboda zafin wuta ya baje, murmushi tayi takoma takwanta….
Washe gari bayan rana ta fad’i suka fito dan tafiya dajin kursad Sarki Nawar kasa fitowa bankwana da yaran nashi yayi saboda halin bak’in ciki da damuwa da yake ciki yana ganin kamar bazasu dawo gareshi ba, Boka Gobar da Tsoho Abnar ne suka tsaya jiran fitowar su Najma bayan sun fito ne Najma tana sanye da kayan tsafi na k’arfe wanda mahaifinta yabata tasa dan samun kariya inda Najla take sanye da riga da wando ta tufke gashinta ta yi gammo da shi, Boka Gobar ne yasa aka yanka wani k’aton sa aka zuba jinin a cikin wata k’warya yad’auka yafara karanta wasu d’alasimai sannan yamik’a masu yace susha, Gimbiya Najma ce ta amsa tasha sosai sannan tamik’a ma Najla k’in kar’ba Najla tayi tatsaya tana kallon ‘yar uwartata da ke rik’e da kwaryar jini tana murmushi ganin haka yasa Tsoho Abnar yace kikar’ba kisha ‘yata, sai a lokacin takar’ba har ta kai baki zata sha sai kuma tafasa tasa hannu tad’ebo jinin tashafa a kanta sannan tamik’a ma Boka Gobar kwaryar.
Amsa yayi yana binta da kallo kamar me son yagano wani abu sai kuma chan yace idan akwai taimakon da kuke buk’ata zaku iya nema a yanzu kafin kutafi, su duka sukace babu.
Wuk’ak’e ne guda biyu Tsoho Abnar yamik’a masu yace na san wannan zaya taimaka maku, gimbiya Najma d’auke kai tayi tace bana buk’atar rik’e komai, Najla ce tad’auki wata ‘yar k’aramar wuk’a tasaka a cikin safar da tasa a k’afarta.
Boka gobar yace shikenan idan kun shirya zan kira Dodona wanda zai zo yad’aukeku a yanzu yakaiku wajen dajin kursad dan samun sauk’in tafiya.
Sukace sun shirya nan yayi tsafi wani bak’in dodo k’ato yabayyana a gabansu, kamawa sukayi kowa yahau gefe d’aya nan yatashi sama yalula dagudu….
Tunda suka fara tafiya babu wanda yace ma d’an uwanshi k’ala inbanda kalle kalle da suke yi gudu yake kamar giftawar walk’iya cikin lokaci kad’an ya isa wajen dajin kursad safka yayi k’asa daga nesa da dajin kad’an cikin wata irin murya me firgitarwa yace nan ne megidana yabani izini inkawo ku zaku cigaba da tafiyar kwana daya da wuni guda da k’afa kafin kudoshi gidan Dodo Gumar.
Su duka safka sukayi nan yatashi sama yakama gabanshi, ja sukayi suka tsaya suna bin dajin da kallo wanda yakasu hanya biyu, Najma juyowa tayi takalli Najla tana murmushi tace ni zan bi wannan hanyar ke kuma zaki bi wannan.
Itama Najla murmushin tayi tace toh shikenan ina mana fatan nasara.
Batare da Najma ta ce komai ba tawuce tadoshi cikin dajin ta hanyar da tace zata bi, ganin haka yasa Najla itama tabi tata hanyar…
Tafiya suke sosai a cikin bak’in dajin babu motsin komai a ciki sai kukan tsuntsaye tunda suka fara tafiya basu had’u da wani abun tsoro ko wanda zai firgitasu ba, kwana sukayi suna tafiya cikin dajin kowa shi kad’ai lokacin da rana ta fito duk suka samu cikin itace suka la’be har saida ranar talumshe sannan suka fito suka cigaba da tafiya gab da duhu zai fara suka fara jiyo wani irin gurnani me firgitarwa su dukansu cikin sauri suka nufi inda suke jin gurnanin basu ankara ba sai gani sukayi sun ‘bullo a hanya d’aya Najla da Najma.
Da mamaki suke kallon juna har Najma ta bud’e baki zatayi magana sai ji sukayi k’asar wajen ta fara girgiza wata irin iska me k’arfi tataso, tsuntsayen da suke shawagi a sama suna ta guduwa gurnanin yana tunkaro inda suke hakan ne yasa suka gane Dodo Gumar yana tafe inda suke su duka ja sukayi suka tsaya tare da gyara tsayuwarsu itatuwan da suke wajen ne suja dinga zubewa suna fad’uwa basu ankara ba sai ganin wani jibgegen dodo sukayi me girma sosai su dukansu saida suka firgita da suka ga girmanshi…
Najla ce tad’an ja baya tace Najma me yakamata muyi? Najma murmushi tayi tace kowa yayi abinda zai fisheshi duk wadda tayi k’ok’arin ‘ballo mashi kunne guda toh tabbas ta cancanci ajinjina mata.