HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Najla batace komai ba nan taruga dagudu cikin zafin nama tatunkari inda dodo gumar yake tafowa kamar giftawar walk’iya Najma taga Najla ta tafi kafin ta isa wajenshi Dodo Gumar ya sa dogon hannunshi ya hankad’ar da ita sai gata k’asa a kwance.
Ganin haka yasa Najma tafara jifanshi da sihiri kala kala ammah kokad’an sihirin baiyi tasiri a jikinshi ba haka yayi ta tunkaro inda take tsaye tana ja da baya daga k’arshe tayi sihiri wata wuk’a tabayyana a hannunta gab da zai iso tad’aga wuk’ar tasara mashi yasa hannu yatare sai ganin tirtsatsin wuta sukayi ya tashi cikin sauri taja da baya tana kallonshi cike da mamaki, cacimota yayi yad’aga sama zai maka da k’asa Najla da ke kwance tana ganin haka tataso takai mashi naushi ta baya hannunshi yad’aga yajawota yahad’e kansu da Najma sannan yasakesu suka fad’i k’asa, k’ara suka saki nan yayo wajensu zai fad’a masu kusan lokaci guda sukayi tsafi duk suka ‘bace suka fad’a gefe d’aya yafad’i k’asa saida wajen da yafad’i yayi rami, kafin suyi yunk’urin mik’ewa har ya tashi ya yo kansu, saurin ja da baya sukayi nan Najma ta ta’ba zobenta ta’bace, kafin Najla tayi wani yunk’urin ya cafko mata wuya ya d’ageta sama kakari tafara yi nan yai wurgi da ita tafad’o k’asa a sume…

Najma na ganin haka tabayyana cikin sauri ta bayanshi takai mashi naushi yacafkota yawulwula yakada da k’asa wata irin kururuwa yayi wadda tasa gabad’aya dajin ya amsa hatta Najla da ke sume saida yafarfad’o a galabaice.
Makekiyar k’afarshi yad’aga zai murje Najma da ita nan tasaki k’ara, cikin sauri Najla tamik’e ganin abinda yake shirin yi ma ‘yar uwarta yasa tafalfala dagudu ta isa wajen tana zuwa wani irin tsalle tayi tafad’a saman kan dodon cikin zafin nama tazaro wuk’ar da tasaka cikin safar k’afarta kafin yayi wani yunk’uri ta yanki kunnenshi guda na dama, wata irin kururuwa yayi yai wurgi da Najla tafad’o k’asa tim tana rik’e da kunnen nashi, jini ne yafara tsartuwa daga wajen da tacire kunnen, k’ara Dodo gumar yasake saki wadda gabad’aya saida dajin ya amsa tsuntsaye suka dinga zubowa dafa sama a sume sannan yajuya aguje yabar dajin dan tseratar da ranshi yanufi gidanshi.

Najla numfashi tafara safkewa sama sama sannan tajuya takalli Najma da tunda Dodo Gumar yad’aga k’afa zai mirjeta tasume, yun k’urin mik’ewa tayi amma takasa saboda gabad’aya jikinta ciwo yake, dak’yar tasamu tamik’e tana rik’e da kunnen Dodo Gumar tanufi wajen da Najma take a sume tana zuwa tafad’i tad”aga hannu tafara bubbugata sai chan tabud’e idanunta, tashi zaune Najla tayi tana haki tanuna ma Najma kunnen Dodo gumar da ke hannunta.
Mitstsike idanu Najma tayi tasake bud’awa tana ma Najla kallon mamaki, mik’a mata kunnen tayi tana cigaba da murmushi, shammatarta Najma tayi takai mata wani irin duka a fuska nan Najla tasulale tafad’i a sume.

Ganin haka yasa Najma tamik’e tana cigaba da kallonta nan taga jinin da ya’bata wajen ta ida tabbatarwa da Najla ta yi nasara akan Dodo Gumar wata irin k’ara tasaki cikin ‘bacin rai tace k’arya ne Najla wannan nasarar tawa ce ba taki ba, murza zoben hannunta tayi nan yanuna mata komai yafaru tsakanin Najla da Dodo Gumar wasu irin hawayen bak’in ciki ne suka gangaro mata duk’awa tayi tad’auki kunnen dodo gumar takalli Najla da ke sume tayi murmushi tace wannan nasarar tawace Najla ke a nan rayuwarki zata k’are, tana gama fad’in haka tasaka kunnen a cikin ‘yar jakkar tsafinta sannan tajuya cikin sauri fuskarta d’auke da farin ciki takama hanyar fita daga cikin dajin

Tafiya take dakyar tana had’awa da tsafi ahaka tasamu tafito daga cikin dajin kursad tana fitowa tasamu waje tazauna sannan tafara yan tsibbace tsibbace sai ga wani k’aton tsuntsu ya bayyana mik’ewa tayi agalabaice tahau saman tsuntsun nan yad’aga yalula sama da ita kwanciya tayi samanshi ahaka har ya isa da ita cikin k’asar nairan farin ciki fal a cikin zuciyarta tana isa tasamu taron jama’a cike a wajen fada nan aka fara murnar dawowarta safka tayi daga saman tsuntsun sannan tawuce tanufi cikin fada batare da ta saurari maganar da ake ta yi mata ba tana rik’e da jakkarta wadda tasa kunnen Dodo Gumar a cik, jinin da sukaga yana d’iga ne daga cikin jakkar yasa suka gane ta yi nasara nan sukaita murna inda wasu kuma suka fara tunanin ina Gimbiya Najla ko dai ita ta halaka jikinsu sanyi yayi sosai nan wasu suka fara koke koke…

Gimbiya Najma dagudu tashiga cikin fadar fuskarta d’auke da fara’a bakinta ya k’i rufuwa tana shiga tasamu su Mahaifinta da Boka Gobar sai Tsoho Abnar tare da wani dattijon bak’in maye zaune ja tayi tatsaya a bakin k’ofa cike da farin ciki tace Abba, Kakana na yo nasara, su dukansu babu wanda yace mata komai tabud’e jakkarta tafiddo kunnen dodon d’aga masu tayi tace kun gani.
Binta kawai sukayi da kallo batare da sunce mata komai ba ganin haka yasa fara’ar da ke fuskarta tarage sai a lokacin talura da madubin tsafin da yake hannunsu tabbas ta san sun ga duk abinda yafaru wasu hawaye ne suka gangaro mata tayi saurin sakin kunnen dodo gumar a nan wajen tafara ja da baya tana sheshek’ar kuka daga baya tajuya dagudu tabar fadar tanufi ‘bangarensu tana isa tasamu mahaifiyarta da sauran kuyangi ana ta murna bata bi ta kansu ba tashige cikin d’akinta tamaida tarufe a saman gado tafad’a tashiga rusa kuka tana bugun katifa tana cewa meyasa ba ni ce nayi nasarar cire kunnen ba meyasa Najla tayi min haka?.

Su mahaifiyarta cirko cirko sukayi ganin yadda tashigo bata ko kulasu ba nan tafara tunanin ko dai basuyo nasarar samun abinda sukaje nema ba d’aya daga cikin kuyanginta ne tace ranki yadad’e ina tunanin ‘yar uwarta ce tamutu a chan saisa take kuka.
Dariya Sarauniya Wailah tayi tataka ta isa wajen k’ofar d’akin Najma tafara bugawa tana cewa ‘yata zo kibud’e min wannan ranar farin ciki ce agaremu idan ma ‘yar uwartaki ta mutu ai ba wani abu bane mu da mukeson haka, a yau dai kowa zai shaida kece magajiyar Sarki Nawar bayan rashin.
Najma tana jinta tashare tacigaba da kukanta abun duniya duk ya dameta..

A chan ‘bangaren su Sarki da sukaga duk abinda yafaru a cikin madubin tsafi gabad’ayansu shuru sukayi kunya duk ya cika Boka Gobar dan duk a tunaninshi Najma ce zatayi nasara shine daliln da yasa yakunno masu komai dan sukalla, Sarki ko danna zoben da yake hannunshi yayi.
Najla da ke kwance a sume cikin wannan k’urmin dajin farkawa tayi dak’yar ta iya dafe kanta sannan tatashi zaune abinda duk yafaru ne yadawo mata a rai d’an guntun murmushi tayi tare da mik’ewa dak’yar tafara tafiya zobenta da taga yana haske ne talatsa sai gata ta ‘bace ‘bat kamar ancillota taga ta fita daga cikin dajin wani k’aton tsuntsune tagani a tsaye bata tsaya wata wata ba tahaye samanshi yatashi sama cikin lokaci kad’an ta iso k’asarsu, tana safka nan jama’ar da suke tsaye wajen fada suka fara murnar dawowarta ko cikin fadar bata shigaba tawuce tanufi ‘bangarenta tana isa duk wanda yazo yi mata magana saidai tad’aga mashi hannu ahaka tashige d’akinta tahau saman gado takwanta jikinta duk yana mata ciwo……..

 

_*Part 1 Free pages ne*_

_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button