KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
_Sis Nerja’art✍????_
09035938246_*KUWWA DA KUWWA*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 14*
Sarauniya Zaiba ganin kwana d’aya biyu Yakumbo bata kirata tayi mata maganar yadda sukayi da Memartaba ba kuma shima Memartaba baice mata komai ba akan maganar Yarima da Farha, ga Farha da tatusota a gaba kullum tambayarta take yadda sukayi da Yakumbo saidai tace basuyi maganar ba, daga k’arshe dai Farha tamatsa mata akan tatambayi Yakumbo yadda sukayi da Memartaba dan haka Sarauniya Zaiba tashirya taje turakar yakumbo bayan sun gaisa ne nan suka fara hira a cikin hirar ne Sarauniya Zaiba tace wai Yakumbo ya kukayi da Memartaba akan maganar Yarima mu fa mun matsu musha shagalin d’an lelen Sarki.
Rik’e baki Yakumbo tayi tace wane ni ai abari inmutu maza subinne ni Yarima ya fi k’arfina dan da na kirashi nayi mashi maganar ko kallona baiyi ba bare yatankani saima latsar waya da yakeyi kinsanshi da wannan mugun miskilancin nashi daga k’arshe ma yatashi yatafi yabarni tun daga ranar ma ko zuwa yagaisheni bai sake ba.
Ta’be baki Sarauniya Zaiba tayi tace lallai Yarima halinshi sai shi ammah ai baza’a sa mashi idanu ana kallonshi ba kyau ace anza’ba mashi mata tunda shi baiji girman kanshi zai barshi yaza’ba.
Yakumbo tace ai kibarni da shi ni zanyi maganin wannan miskilancin nashi inma banda abunshi ga ‘yar uwarshi a gida tunda baida wadda yakeso ai sai ya aureta arufa ma juna asiri.
Wani irin dad’i Sarauniya Zaiba taji cikin ranta tace wallahi kau Yakumbo nima abinda nace kenan ai da ace su Memartaba zasu amince Yarima nashi me sauk’i ne.
Uhm ni ai banda bakin magana Zaiba dan Yarima ya watsa min k’asa a ido su ma iyayen nashi kamar bayanshi suke ji dan jiya ma da Umminsu tashigo nayi mata magana saidai tasunkuyar da kai tana murmushi tace insha Allahu zasuyi mashi magana.
Murmushi Sarauniya Zaiba tayi tace lallai kam har da d’aurewar gindi yasamu daga wajensu ammah ni zan sake tuntu’bar memartaba.
Yakumbo tace toh shikenan.
Bayan sallar azahar Memartaba yashigo cikin gida kamar yadda yasaba dan cin abinci, yana zaune a cikin turakarshi Sarauniya Zaiba kasancewar itace da miji a ranar tana zaune kusa da shi yana cin abinci jira kawai take yagama tayi mashi magana.
Bayan ya gama ya kimtsa cikinshi yajuyo yakalleta itama d’in kallonshi take murmushi yayi yace Zaiba da alama akwai magana atare da ke toh idan kin shirya sanar da ni ina saurarenki dan inason fita.
Gyara zama tayi tace tabbas hakane ranka yadad’e akwai magana atare da ni kuma ba a kan komai bane sai akan Yarima.
Da mamaki yake kallonta yace Yarima kuma?.
Murmushi tayi tace Eh ranka yadad’e a gaskiya zaman da Yarima yake hakanan babu aure bai daceba ya ci ace zuwa yanzu Yarima ya mallaki matarshi kaduba kaga abokinshi Salim d’an waziri shi yana gab da yin auren ammah shi ko niya baida shi.
Murmushi Sarki Abdullah yayi yace Zaiba kenan toh ya kukeso inyi bayan laifin d’an nakune ku yakamata kuzauna kukwatanta mashi yazo yayi aure.
Itama murmushin tayi tace haba ranka yadad’e mu asuwa kaine dai yakamata kayi mashi magana in yak’i sai kaza’ba mashi mata tunda kana da ikon hakan kaduba kaga yadda ake fama da shi ankawo mashi hotunan ‘yanmata kala kala ammah ya nuna babu wacce tayi mashi haka ma kasa aka turo ‘ya’yan abokanka dan yagansu kuma yaje yaga wasu ammah ya nuna babu wacce tayi mashi a cikinsu…
Murmushi Memartaba yayi yana dannar wayarshi da take hannunshi
Cigaba tayi da cewa ranka yadad’e ya kamata kaduba maganata baidace ace kamar kai ba a matsayinka na babban sarki ace d’anka Yarima yana zaune babu aure bayan duk wata dukiya yana da ita shin idan baiyi aure yanzu ba sai yaushe zaiyi ko sai bayan mutuwarmu? Sannan kaduba kaga ‘yar uwarshi yadda take k’aunarshi tana binshi ammah ko kad’an baya kulata kullum nuna mata tsana yake shin hakan da yakeyi ya dace kenan…..bud’e k’ofar da akayi aka shigone yasa taja bakinta tayi shuru saboda yanayin takun tafiyar da tajiyo yasa tagane Yarima ne, sai a lokacin sarki yad’ago kai yakalleta sannan yamaida kallonshi ga yarima d’an da yad’auki son duniya yad’aura mashi murmushi yayi yace ga ma d’an halak d’innan muna maganarshi
Juyawa Saraujiya Zaiba tayi tawatsa ma Yarima harara hankalinshi yana ga mahaifinshi bai ma san tana yi ba, cikin takunshi na k’asaita yanufi d’aya daga cikin kujerun yazauna fuskarshi d’auke da murmushi yace kayi hak’uri Abiy na so inbari sai da anjima idan ka fito fada mutattauna toh kuma da k’arfe hud’u zan shiga theater room saisa nazo yanzu.
Murmushi shima Sarki Abdullah yayi yace kar kadamu d’ana duk yadda kayi daidai ne daman ga Mamanku nan yanzu take maganarka ta ce ka k’ii fito da mata har yanzu susha bikki.
Kallo d’aya Yarima Ayran yayi mata yad’auke kai inda itama Sarauniya Zaiba tahad’e fuska saboda wani irin haushinshi da takeji saboda abinda yaima ‘yarta.
Canza maganar Yarima yayi ta hanyar cewa Abiy akwai kud’ad’en da nake son shigar da su a cikin asusun tallafi na marayu saisa nace bari infara yin shawara da kai.
Jinjina kai yayi yace hakan da kayi daidai ne ai ko bakayi shawara da ni ba bawani abu bane tunda taimakone zakayi kuma da guminka ne, kallon Sarauniya Zaiba yayi da tayi shuru yace kinga d’an naku baya son maganar auren saisa yai saurin canza zance na rasa meyasa yake gudun aure,
Ta’be baki tayi batare da ta kalli inda Yarima yakeba tace toh ai shikenan bari dai inbaku waje kutattauna naga kamar da magana yazo, Memartaba yace nima naga kamar haka Ayran dan ko gaishe da mamar taku banga kayi ba.
Murmushi yayi yace Abiy mun gaisa da ita ai d’azun, saurin juyowa Sarauniya Zaiba tayi takalleshi taga ya had’e fuska kamar bashine yayi maganar ba yana dannar waya, wani irin k’ululun bak’in ciki ne yatsaya mata batare da ta ce komai ba tajuya tafita tabar turakar cikin ranta tana jinjina ma halin Yarima da kwatakwata baya girmamata ammah ya zama dole tayi maganinshi…..
Bayan fitar Sarauniya Zaiba Memartaba kallon Yarima Ayran yayi yace Yarima meyasa kake nuna ma Farha tsana bayan itama ‘yar uwarkace sannan ai inaga ba laifi bane ga wanda yace yana sonka.
Kallon mahaifin nashi yayi ahankali yabud’e baki yace Abiy ita Farha tace tana sona?
Murmushi memartaba yayi yace ko batace ba ai ba aibu bane dan ka aureta.
Shuru Yarima Ayran yayi batare da ya ce komai ba ganin haka yasa Memartaba yace shikenan dai Ayran ni bazan maka dole ba zan barka ka auri wadda kakeso kana da wannan damar saidai shawarar da zan baka dan Allah kanutsu kamaida hankali akan maganar aure indai ba ka fi so sai bayan raina sannan zakayi aurenba.
Cikin kwantar da murya yace kayi hak’uri Abiy insha Allahu zan yi da zarar na samu matar da nakeso.
Shikenan Yarima Allah yaza’ba mafi Alkhairi.
Ameen Abiy……