HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

 

Sarauniya Wailah tana komawa turakarta kasa zama tayi sai kaiwa da kawowa da take tana tunanin hanyar da zata ‘bullo ma Yarima tana cikin haka wani tunani yafad’o mata daidai da shigowar Farha da mamaki take kallon mahaifiyartata tace Mama lafiya naganki haka?
‘Dagowa Sarauniya Zaiba tayi takalleta tace lafiya lau Farha saidai Yarima bana tunanin zai amince ya aureki cikin ruwan sanyi batare da munyi wata dabara ba.
Hawaye ne lokaci guda suka gangaro mata tace yanzu Mama kina nufin bazai aureni ba?.
Tsaki Sarauniya Zaiba tayi yace kinga matsalarki abu kad’an sai ki nemi kizubar da hawaye toh ke inbanda ma abunki taya kike tunanin zan zauna inzuba mashi idanu yak’i aurenki ai dole insanyaya maki rai ‘yarleleta kinfi kowa sanin inaso ki auri Yarima ba dan komai ba sai dan nan gaba kizama Sarauniyar k’asar Miraj sannan ki haifa mashi d’an da zai gajeshi sarauta.
Saurin zuwa tayi tarungume mahaifiyartata tace nagode sosai Mama ashe kina sona irin haka.
Shafa kanta tayi tace fiye ma da haka nake sonki ‘yarlele yanzu dai kibar min komai a hannuna wuce kije d’akinki kihuta dan na ga kamar kin kwaso gajiya daga school.
Yatsina fuska tayi tace wallahi kau Mama na kwaso gajiya sosai kisa akawo min abinci na a d’akina.
To shikenan kar kidamu zan sa, wucewa Farha tayi tanufi ‘bangaren d’akinta nan Sarauniya Zaiba tatura wata kuyanga tace taje takira mata wata amintacciyar baiwarta mesuna Salwa, cikin sauri kuyangar tafita dan cika umurnin uwargijiyarta…

 

**** *****
…Sarki Nawar a sukwane yafito daga cikin turakarshi yanufi ‘bangaren Gimbiya Najla yana zuwa yasameta kwance saman gado tana bacci ja yayi yatsaya a gefen kanta yana kallonta daidai lokacin tabud’e idanunta ganin mahaifinta yasa tayi saurin tashi zaune cike da mamaki tace Abba.
Yanayin da tagani tare da shi saida gabanta yafad’i dan yana cikin yanayi na damuwa, cikin sanyin jiki tace me yafaru Abbana.
Maimakon yabata amsa sai ma rik’o hannunta da yayi yace taso muje d’akin abun bauta.
Bata musaba tamik’e tabishi suka fito daga gidan sarautar suka doshi d’akin Dodo Gostan suna isa mai tsaron d’akin yai saurin bud’e masu k’ofa suka shiga ciki, babban d’akine wanda yake d’auke da wani k’aton gunkin wani tsafaffen Dodo siffarshi abun tsoro duk an yayya’beshi da zinarai a jikinshi a k’asa wani bak’in maye ne fuskarshi baje da bak’in gashi yana zaune yana kallon gunkin.
Najla bin d’akin tafara yi da kallo kafin Sarki Nawar yarik’ota suka zauna bayan bak’in mayen suna zama nan duk suka rufe idanunsu hasken d’akin ne yafara d’aukewa yana dawowa nan bak’in mayen yafara kirari cikin wata irin murya marar dad’in saurare yana yabon abun bautar nasu har lokacin su Sarki Nawar idanuwansu suna a rufe wata irin iska tataso cikin d’akin wata irin murya sukaji me kama da haniniyar doki ance kufad’i buk’atarku, sarki nawar ne yabud’e idanunshi yamik’e cikin iskarnan yanufi wajen da gunkin nasu yake yana isa yazube yayi sujjada daidai lokacin iskar tatsaya cak, Najla mik’ewa tayi itama tabi bayan mahaifin nata tana zuwa tatsugunna a gefenshi taruntse idanunta tare da had’e hannuwanta waje guda..

Sarki Nawar ahankali yad’ago kanshi cike da damuwa yajuyo yadafa kan Najla nan tabud’e idanunta takalleshi d’an guntun murmushi yayi yace tashi muje.

Mik’ewa tayi yarik’e hannunta suka fito daga cikin d’akin dodo gostan suka nufi gidansu na sarauta…

suna isa a turakar Sarki suka wuce nan duk yasallami masu kula da shi d’akin yarage daga shi sai Najla, gefenshi tazauna tana kallonshi har ta bud’e baki zatayi magana yatari numfashinta ya ke ‘yah ta hak’ik’a na san dole kiyi mamaki akan yanayin nan da kika ganni a ciki kuma na san sai kin tambayeni dalilin zuwanmu d’akin Dodo Gostan.
Idanu Najla tazuba ma mahaifin nata tana kallonshi.
Janye idanunshi yayi gefe sannan yacigaba da cewa ba komai bane yad’aga min hankali face wani mafarki da nayi ammah tunda muka shiga d’akin Dodo Gostan na ji zuciyata ta nutsu.
Sai a lokacin Najla tayi murmushi, shafa kanta yayi shima yana murmushin yace ina alfahari da ke ya ke kyakkyawar ‘yata wadda nake fata ace kece kika gaji masarautar naira.
Fara’ar da take fuskarta ce taragu nan tayi saurin girgiza kai tace a’a Abbana ba nice yadace inmulki k’asar nan ba ‘yar uwatace yadace saboda itace babba sannan babu abinda zai rabamu da kai muna tare.

Cikin sanyin jiki yace Najla ba zan ‘boye maki ba zuciyata ta fi aminta da ke akan mulkin k’asar nan sama da ace ‘yar uwarki ce saboda nasan jama’armu na mayu zasuyi farin ciki su ma sannan na san bazaki ta’ba nuna banbanci a tsakaninsu ba kamar yadda ke da mahaifiyarki bakuda halin k’abilancin k’asar nan na rashin k’aunar da ke tsakanin farare da bak’ak’en mayu sannan kina da tausayi wa nak’asa da ke wannan dalillan ne yasa nake ganin kin fi ‘yar uwarki cancanta kece kad’ai yadace kimulki k’asar nairan ko bayan rai na….

Wannan maganar da yafurta daidai da Gimbiya Najma zata shigo cikin turakar mahaifin nasu yadoki kunnenta, ja tayi tatsaya gabanta yayi mummunan fad’uwa lokaci guda gashin jikinta yamimmik’e fuskarta tacanza kala.

Gimbiya Najla idanu kawai tazuba ma mahaifin nata tana saurarenshi saidai ko kad’an bataji sha’awar son mulkar k’asar nan ba, tunani tafara idan har haka ya kasance ‘yar uwarta bazata ta’ba bari azauna lafiya ba dan a fili ta fito ta nuna mata itace zata gaji mulkin mahaifin nasu.
Dafata yayi yace kidaina tunanin komai Najla babu abinda zai faru kuma da sannu Dodo Gostan zai kar’bi addu’ata sannan ina k’ara gargad’inki kikula da zoben nan na hannunki kuma kirik’e sirrin maganar nan da mukayi kar kisanar da kowa saboda gudun kar wani rikici yatashi dan na san halin ‘yar uwarki..
Najla rasa abinda zatace ma mahaifin nata tayi nan tayi saurin fad’awa jikinshi tafashe da matsanancin kuka.
Hawaye ne suka gangaro ma Sarki Nawar yasa hannu yagoge sannan yashiga lallashin ‘yar tashi…

Gimbiya Najma da ke tsaye wajen kamar gunki hawaye sun gama wanke mata fuska zuciyarta tana tafarfasa har zata bud’e k’ofa tafad’a cikin d’akin sai kuma tafasa tajuya cikin sauri tawuce tabar wajen, murza zoben hannunta tayi nan ta’bace ba’a d’au lokaci ba sai gata ta bayyana cikin gidan kakanta boka gobar daidai lokacin da Boka gobar da Sarauniya Wailah suke zaune ta kawo ma mahaifin nata ziyara a ‘boye suna gaisawa sai ganin Najma sukayi ta bayyana a gabansu rai ‘bace zuciyarta tana ta tafarfasa da mamaki suke kallonta ganinta cikin wani irin yanayi me wuyar misultawa basu ankara ba sai ganinta sukayi ta zube gaban boka gobar ta ruk’o mashi duka k’afafunshi.

Sarauniya Wailah ce tace lafiya Najma me yafaru?

Najma kallon Boka Gobar tayi da shima yake kallonta bud’e baki tayi dak’yar tace ya kakana hak’ik’ ranar yau ta kasance rana mafi muni agareni kaicona da wannan ranar ta riskeni ina neman taimakonka a wannan ranar inaso zan yak’i Mahaifina da duk wani wanda yake tare da shi dan bazan ta’ba barinsu ba.

Boka Gobar janye k’afarshi yayi daga rik’on da tayi mashi tare da mik’ewa tsaye cike da mamaki yace wannan wace irin magana ce kike Najma?

Sarauniya Wailah ma mik’ewa tayi tace anya kina cikin hayyacinki mahaifin naki zaki yak’a?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button