HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Mik’ewa Najma tayi nan hawaye yacigaba da wanke mata fuska tace tabbas ya zama dole inga bayan duk wani mahaluk’i da zai nisantar da ni daga sarautar garin nan duk wanda baya son ingaji sarautar k’asar nairan toh baida sauran amfani agareni, shin Abbah bai san iya lokacin da nad’auka ina burin son mallakar k’asar nan ba? Shin bai san irin k’aunar da nake ma sarautar k’asar nairan ba?..

Boka Gobar matsowa yayi kusa da ita yace ya ke jikata ina so kinutsu kisanar da ni komai dan akodayaushe ina tare da ke shin me yafaru?

Goge hawayen fuskarta tayi tace Kakana a yau kunnuwana sun jiyo min abinda yatarwatsa duk wani farin ciki nawa, Mahaifina najiyo da bakinshi yana fad’a ma Najla cewa ita yakeso tagaji sarautar k’asar nairan bayan ranshi, meyasa sarki zaya min haka alhali ya san nice kad’ai yadace in mulki k’asar nan…
Wata irin k’ara Sarauniya Wailah tasaki cike da firgita tace inaaa wannan bazai ta’ba yuwuwa ba bazan ta’ba bari hakan yafaru ba alhali kina raye ya zama dole sarautar k’asar nairan tadawo hannun bak’ak’en mayu juyawa tayi takalli mahafin nata tace Abbana hak’ik’a muna neman taimakonka ya kamata agaggauta yin wani abu kafin Sarki Nawar yasanar da ‘yan majalisanshi akan abinda yake ranshi.
Murmushi Boka Gobar yayi yace ya zama dole inyi wani abu anan dan nima kaina ina da buri sosai akan son ganin sarautar k’asar nairan ta dawo hannun bak’ak’en mayu kuma tarihi yafara daga cikin zuri’a ta, tunda har Sarki Nawar yafito yanuna ya fi son Najla tamulki k’asar nan, zama yayi k’asa yatank’washe k’afarshi yaruntse idanunshi yana karanto wasu d’alasimai nan take kayan tsafinshi suka bayyana agabanshi bud’e idanunshi yayi yad’akko wani tsinke me kamar gashin tantabara yafara zana wani abu a saman k’asa yana gogewa ya yi kusan mintuna ashirin yana haka kafin daga baya yad’ago kai yakallesu fuskarshi atamk’e yace tabbas abin dogarona ya nuna min hanya guda ce kawai zamu iya bi kimulki k’asar nan…yana fad’in haka yayi shuru yana kallonsu.
Gimbiya Najma ce a fusace tace kowace hanya ce abi ta ya kai kakana tun kan Sarki yafito fili yafad’i k’udurinshi akan Najla, bazan ta’ba damuwa ba ko da ace zai tasa ranshi dan ni a yanzu mulkin nan ya fiye min komai.
Jinjina kai Boka Gobar yayi yace tabbas wannan ce hanyar kawai da nagano zamu bi musalwantar da ran sarki idan munyi hakane kawai zaki samu damar milkar k’asar nairan.
Murmushi Najma tayi tace fiye ma da hakan ayi idan har zan mulki k’asar.
Shima murmushin yayi sannan yajuya yakalli Sarauniya Wailah da ke tsaye nan itama tayi murmushi tace na goyi bayan hakan na k’wammace inrasa mijina akan ‘yah ta tarasa sarautar k’asar nan.

Jinjina kai Boka Gobar yayi yace da kyau na ji dad’in hakan saidai hanya d’aya ce yadace mubi idan har munason salwantar da ran Sarki Nawar cikin sauk’i… Najma ce tatari numfashinshi tace kafad’i kowace hanya ce zamu bi ya kai Kakana.

Kallon Sarauniya Wailah yayi yace ammah hakan kamar zai d’anyi mana wahala dan kece zakiyi wannan aikin.
Murmushi tayi tace kafad’i komenene zanyi.

Shuru yad’anyi na lokaci kad’an sannan yace ga hanya mafi sauk’i wadda baza’a gane ba itace kikawo min naman da Sarki Nawar zai ci gobe da rana ammah kitabbata soyayyen nama ne idan har kin kawo ni zan tsafe shi yadda da ya ci shikenan saidai wani ba shi ba, juyawa yayi yakalli Najma yace kekuma kisan dabarar da zakiyi kisamo zoben nan da yamallaka ma Najla dan rabata da zoben shi zai taimaka kimulki k’asar nan idan har kika barta da shi toh tabbas bazaki ta’ba mulkar k’asar nairan ba..

Gimbiya Najma tare da Sarauniya Wailah lokaci guda suka bushe da wata irin mahaukaciyar dariya cike da jin dad’in maganar da Boka Gobar yayi sukace mun amince da hakan zamu aikata abinda ka umurcemu da shi..

Jinjina kai yayi yana murmushin mugunta ahankali yace Sarki Nawar k’arshenka ya zo dasannu labarinka zai shud’e a doron k’asa…..

***** *****

Lokacin da Baiwa Salwa ta iso duk’awa tayi cike da girmamawa tagaishe da uwar gijiyartata, Gimbiya Zaiba tana yatsina ta amsa ciki ciki sannan tace na san bakisan dalilin da yasa nakiraki ba.
Cikin girmamawa tace Eh ranki yadad’e.

Juyawa Sarauniya Zaiba tayi tabada umurni duk kuyangin da suke cikin d’akin suka fita sannan tacigaba da cewa na san bazaki manta shekarun baya ba da nata’ba aikenki a chan k’auyen Lasbir kika samo min magani wanda nayi amfani da shi wajen ganin na auri memartaba,,, yatsine fuska tayi yace kokuma maganin da kika kawo min ba shine yataimaka na auri memartaba ba dan baiyi tasiri ba kawai dai gani yayi yana sona saisa ya aureni.

Baiwa Salwa k’ara duk’ar da kanta tayi tace angaisheki ranki yadad’e.

Kud’i tajawo daga gefen kujerar da take zaune tamik’a mata tace rik’e wannan a wannan karon bana son ayi wasa, kimaida hankali ga abinda zan ce maki saboda na amince da ke saisa nakeyi maki aike irin wannan kije chan k’auyen lasbir wajen malamin nan kisamo min maganin da ‘yata zata mallaki zuciyar Yarima yaji baya son kowa idan ba ita ba, kuma duk abinda takeso sai ya yi mata, idan har kikayi min wannan k’ok’arin toh zan ‘yantaki.
Cikin jin dad’i Salwa tace toh ranki yadad’e angama zanyi k’ok’ari sosai wajen ganin na samo maganin wanda zakiji dad’inshi indai nice kikwantar da hankalinki.

Ta’be baki tayi tace ya dai rage naki sannan wannan maganar da mukayi idan har naji ta a wani wajen sai na yankaki.
Saurin rik’e baki Salwa tayi tace Allah yahuci zuciyarki bama zaki ji ta a ko’ina ba.
Jinjina kai Sarauiya Zaiba tayi tace shikenan kitashi kije kishirya a yanzu nakeson kije wad’annan kud’in ki’boyesu wanda zaki ba malam ne, sai ga wannan kekuma kirik’e na mota da na abinci ne.
Amsa tayi tace toh ranki yadad’e angama insha Allahu zakiji bayani me dad’i daga gareni…

 

Tana fita murmushin mugunta Sarauniya Zaiba tayi tace Yarima da ni kake ja zan baka mamaki dan sai na safke maka wannan jin kan naka dole kadinga bin yadda muke so, yanzu zamu fara wasan…….

 

_*Part 1 Free pages ne*_

_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_

 

*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*

_Sis Nerja’art✍????__*KUWWA DA KUWWA*_
_(Bata korar buzu)_

_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button