KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 15*
Sarauniya Wailah sawa tayi aka shirya ma sarki irin namam da yafi so watau naman d’awisu da na mutum nan tad’auka a’boye tafita da shi daga cikin sarautar takai chan gidan mahaifinta boka gobar, yana ganinta d’auke da naman yayi murmushi yace dakyau ‘yah ta ina fata dai wannan shine naman da Sarki Nawar yafi so?
Murmushi tayi tace Eh Baba tabbas baida naman da yafiso sama da wad’annan.
Jinjina kai Boka Gobar yayi sannan ya amshi naman yashiga da shi d’akin tsafinshi a saman allonshi na tsafi yabaje naman yad’akko wani gari yazuba a kannaman sannan yashafeshi da wani jan abu me kama da jini, runtse idanunshi yayi yafara tsibbace tsibbace saida yagama tsafe naman sannan yabud’e idanun nan wani farin haske yafito daga cikin idanunshi yashiga jikin naman nan, murmushin farin ciki yayi sannan yad’akko naman yarufe acikin takarda yakawo ma Sarauniya Wailah da take zaune tana jiran shi, murmushi tayi tace Baba dafatan angama komai?
Shima murmushin yayi yace abu d’aya yarage shine Sarki Nawar yaci wannan naman daga inda yaci shi shikenan ya gama tashi saidai yasaurari mutuwarshi.
Dariya Sarauniya Wailah tayi tace haka nakeso Baba tunda dai har yanuna ya fi son Najlah toh mu kuma sai munga bayanshi saidai yayi hak’uri, yanzu bari inyi sauri inje inkai naman dan lokacin dawowarshi daga Fada ya kusa.
Boka Gobar yace hakane kimaida hankali fatana ubangiji Dodo Gostan yataimakemu.
Cikin sauri Sarauniya Wailah takoma gidan sarauta dan ma kar aganta ta k’ofar baya tabi dan yawanci indai zataje wajen mahaifinta toh bata cika bin ta k’ofar gaba ba saboda bataso sarki yafara tunanin wani abu akanta da mahaifinta.
Duk wannan abun da ake Sarki Nawar yana chan Fada shi da Fadawanshi ankawo mashi mutane da akaje farauta aka kamo a nan cikin Fada aka yake aka fed’e nan duk Fadawanshi suka tashi suna lashe jinin da aka zubar sannan aka kawo ma Sarki Nawar mutanen da aka bank’are yace kuje kawai kuyi shagali da su nan sukaita murna a d’anyensu suka dinga yanka suna ci, mik’ewa yayi yace bari yashiga cikin gida idan yafito zasuje sugano Boka Gobar da yau bai samu zuwa Fada ba ance baya da lafiya, amsawa sukayi da toh Ubangiji Gostan yataimakeka ya shugabanmu.
nan yakalli Boka Abnar yace idan na fito akwai maganar da nakeso muyi da kai.
Murmushi Boka Abnar yayi yace angama ya shugabana.
Yana shiga cikin turakarshi yaci karo da gasassun naman da yake so daga gefe guda kuma lemune me d’auke da jini aka had’a mashi zama yayi yana murmushi nan yad’akko zai ci zoben hannunshi ne yafara haske hakan yanuna mashi akwai wani abu da zai faru ko yafaru, har zai ajiye naman yafasa ci sai yatuna Sarauniya Wailah ce tashirya mashi dan tun jiya dadare tasanar da shi zata shirya mashi naman da yafi so dakanta saboda tunawa da farkon had’uwarsu rana irin ta yau ce, wata had’ad’d’ar flower ce yaga an ajiye daga gefe guda murmushi yayi yad’akko flower yana dubawa tabbas ya san kyauta ce daga wajen Sarauniya Wailah, ajiyewa yayi yafara cin naman cikin ranshi yana tunanin kyautar da zaiyi ma Wailah wadda zata burgeta sosai, haka yaita cin naman yana korawa da lemunshi me d’auke da jini ahaka har yagama.
Baiyi minti biyar da gama ci ba nan yafara jin kasala yana rufeshi mamaki ne yakamashi yafara tunanin akwai wani abu zoben hannunshi ne na tsafi yaga ya yi bak’i dan haka hankalin Sarki Nawar yatashi wasu hawaye masu zafi suka gangaro mashi, cikinshi ne yaji ya fara murd’a mashi yamik’e dak’yar yana dafa bango yashiga cikin bedroom d’inshi yakwanta kan kace mi zazza’bi me zafi ya rufe shi, yana dafe da cikinshi da yake ta yi mashi ciwo yaruntse idanunshi yafara karanta wasu d’alasimai nan kwalwarshi tafara tariyo mashi mafarkin da yayi jiya wanda yad’aga mashi hankali watau mafarkin ranar mutuwarshi, d’an guntun murmushi yayi ahankali yabud’e baki yace tabbas wannan itace ranata, cikinshi ne da yamurd’a yasa yayi wata irin k’ara kan kace mi ya fara fitar da numfashi sama sama sai ganin wani haske yayi ya ‘bullo daga saman d’akin ya shiga cikin jikinshi, sai ji yayi gabad’aya jikin ya yi mashi nauyi baya iya ko motsa wani ‘bangare na jikin nashi.
Duk wannan abun da yafaru Sarauniya Wailah, Gimbiya Najma tare da Boka Gobar suna zaune suna kallo acikin madubin tsafinshi wani irin dad’i sukaji nan suka dinga dariya hatta wannan farin hasken boka gobar ne ya aika ma sarki nawar da shi cikin jiki dan jikinshi gabad’aya yamutu, kallon Najma yayi da taketa murmushi tana kallon Sarki Nawar ta cikin madubin tsafi da yake kwance kamar gawa baya iya ko motsi saidai k’yafya idanu, Boka Gobar yace kin ga wannan hasken da yashiga jikin Sarki Nawar toh bazai ta’ba tashi dakanshi ba dan na kashe mashi garkuwar jiki sannan ranshi yana a hannuna a duk lokacin da naso zan rabashi da shi haka zai cigaba da kwanciya kamar gawa.
Bushewa da dariya Gimbiya Najma tayi tare da rungume kakan nata tace hak’ik’a na ji dad’in wannan jawabin naka ya kai kakana idan har nahau sarautar k’asar nan zan yi maka gaggarumar kyautar da ba’a ta’ba yi maka irinta ba sannan kuma kaine zaka kasance waziri na tare zamu mulki k’asar.
Wani irin dad’i Boka Gobar yaji yakalli Sarauniya Wailah da take kallonsu tana murmushi yace hak’ik’a kin haifa min jika me k’aunata daman tuni na ta’ba yin mafarki na zama waziri a k’asar nairan sai bayan kin auri sarki nawar nafassara mafarkin da d’iyatace zata auri sarkin garin ammah a yanzu sai gashi mafarkina yana gab da zama gaskiya.
Jinjina kai tayi tace wannan haka yake babana.
Kallon Najma yayi yace yanzu abu d’aya yarage mana kije kiraba ‘yar uwarki da wannan zoben kina rabata da shi toh ni kuma zan kashe sarki nawar.
Janye jikinta tayi daga jikin kakan nata tace yanzu ko zan aikata haka…
Haka jikin Sarki Nawar yaita k’ara tsananta batare da kowa ya sani ba.
*****
Gimbiya Najla tana zaune cikin turakarta ita kad’ai duk ta sallami kuyanginta dan tana so tahuta nan wata kuyangata tashigo dagudu tazo tazube agabanta tana haki tace ranki yadad’e ga Gimbiya Najma nan naga ta tunkaro turakarki saidai bamusan da me tazo ba a yanzu haka ga gabad’aya kuyanginki nan mun hallara a k’ofar turakarki bazamu bari tashigo ba ko da ace zata k’arar da mu.
Mik’ewa Najla tayi cikin sauri tayi hanyar fita daga cikin turakar dan tana tsoron Najma tacutar mata da kuyangi tana fita daga gabansu taja tatsaya daidai lokacin Najma ta iso wajenta itama taja tatsaya tana kallonta batare da ta ce mata komai ba.
Gabad’ayansu shuru sukayi suna kallon juna sai chan Najma tayi murmushi tace a yau na kawo ma ‘yar uwata ziyara a karo na farko a rayuwata saidai ban saniba ko zata kar’bi bak’unci na?
Mamakine k’arara yabayyana a fuskar Najla tazuba mata idanu tana kallonta hatta kuyanginta sunyi mamakin jin furucin Gimbiya Najma da kuma murmushin da suka gani a fuskarta a karo na farko a rayuwarsu.
Gimbiya Nalja kasa gasgata abinda kunnuwanta suka ji mata tayi ganin haka yasa Najma tamik’a mata hannu bata musaba tamik’a mata nata hannun tarik’e nan Najma takalli zoben hannunta sannan tace idan ba damuwa zamu iya shiga ciki?
Murmushi Najla tayi tace me zai hana, nan taba kuyanginta dama suka matsa suka shiga cikin parlorn a saman doguwar kujera suka zauna har lokacin Najma na rik’e da hannun Najla.
A karo na biyu tayi murmushi tace na san dole kiyi mamaki akan ganin da kika yi min a karo na farko na ziyarceki kiyi hak’uri da abinda yafaru a tsakaninmu sannan banzo dan in cutar da ke ba kawai dai na zauna na yi tunani naga ya dace muhad’a kawunanmu dan samun farin cikin mahaifinmu.