KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Gimbiya Najla har lokacin kallonta kawai take ta kasa gasgata maganar ‘yar uwarta bata ankaraba sai ganin Najma tayi ta rik’o hannunta ta d’aura saman kanta ta ce na rantse da ubangiji gostan bazan cutar da ke ba.
farin ciki ne sosai yaziyarci zuciyar Najla cikin sauri tarungume ‘yar uwartata tace nagode sosai Najma ha’ik’a ina farin ciki da wannan ranar da ‘yar uwata ta amince da ni amatsayin ‘yar uwa agareta.
‘Dago ta Najma tayi tana murmushi tace na fi ki farin cikin haka Najla sannan zan so kowa na garin nan yasan cewa mun had’a kawunanmu.
Murmushi Najla tayi tace zan so Abba yakasance mutum na farko da zai fara ganin hakan dan na san zai fi kowa farin ciki.
Hakane ‘yar uwata zan so hakan nima, daidai lokacin kuyangi suka fara shigo masu da abinci da nama iri iri suna ajiyewa agabansu, murmushi Najma tayi tace na ji dad’in wannan karramawar da nasamu koda a k’oshe nake saidai ya zama dole inci saboda yazama yau shine karo na farko da zan ci abinci tare da ‘yar uwata.
Hakane nima zanyi farin ciki da hakan.
Safkowa sukayi tare suna cin abinci har lokacin Najla bata sake sosai ba suna cikin ci Najma takalli zabban hannun Najla tace ‘yar uwata shin ko zaki iya bani wannan zoben naki ingani?
Najla murmushi tayi tace zan iya baki man me zai hana, bata kawo komai a ranta ba taciro zoben da taga Najma tana kallo tamik’a mata, amsa Najma tayi tana kallon zoben tana jujjuyashi a hannunta inda Najla tacigaba da cin abincinta tana murmushi, Najma cigaba tayi da juya zoben tace ammah dai yana da kyau sosai zoben nan.
‘Dagowa Najla tayi takalleta tace hakane saisa na fi son shi acikin zabban da ke hannuna.
Batare da ta mik’a mata ba tace ina ma ace zaki ara min shi abisa amana inje ayo min design shigen irinshi.
Jim Najla tayi tana kallonta batare da ta ce komai ba dan bata son ba kowa zoben saboda muhimmancinshi da gargad’in da mahaifinsu yayi mata akan takula da shi, dafata Najma tayi tace shin kina tunanin ko zan rabaki da zoben nan?
Girgiza kai Najla tayi tace ba wai haka ba.
Murmushi Najma tayi tace na yi maki alk’awali da anjima zan maido maki shi.
Kar kidamu ‘yar uwata kitafi da shi saidai ina so kikula da shi sosai.
Wannan ba wani abu bane zan kular maki da shi
Haka sukaita cin abinci suna ta’ba hira yanayinsu kawai zaka kalla kagane cewa suna cikin farin ciki a wannan ranar musamman ma Najla da kamar tahad’iye ‘yar uwartata saboda jin dad’i, suna gamawa Najla tafara mik’ewa tsaye tana murmushi tace ya kamata muje Abba yaganmu tare na san zaiyi farin ciki sosai, itama Najma mik’ewa tayi tana murmushi tace nima zan so ganin farin cikin da Abba zai shiga idan yaganmu tare mun had’e kanmu.
Rik’o hannunta Najla tayi suka jera suna tafiya su dukansu fuskarsu d’auke da murmushi duk wanda yagansu sai mamaki ya bayyana a fuskarshi dan ansansu ko kad’an basu jituwa ahaka har suka isa turakar mahaifin nasu suna shiga suka ga baya parlor dan haka suka shiga cikin bedroom Najla na k’wala mashi kira ganinshi da tayi bisa gado kwance ya yi shame-shame yasa tayi saurin sakin hannun Najma taje wajen gadon tana zuwa taja tatsaya tana kallonshi saida gabanta yafad’i nan tabud’e baki dak’yar takira sunanshi ammah taji shuru, jijjigashi tafara yi ammai bai ko motsi saurin juyowa tayi takalli Najma da ke tsaye chan gefe fuskarta d’auke da murmushi babu alamar damuwa atare da ita cike da rud’ewa Najlah tace Najma kizo kitaimaka min bansan me yasamu Abba ba. ko motsawa batayi ba bare tasa ran zata zo wajen da take, girgiza Sarki Nawar tashiga yi dak’arfi ammah ko motsawa baiyi ba nan ta ida rud’ewa tafasa wata gigitacciyar k’ara da gabad’aya d’akin ya amsa hatta masu tsaron k’ofar turakar sarki da ma’aikatnshi saida suka jiyota cikin sauri suka bud’e k’ofar suka shiga parlor ganin ba kowa yasa suka ja turus suka tsaya, kukan da Najla tacigaba da yi ne tana kiran sunan Abbanta yasa ukku daga cikinsu sukayi saurin shiga cikin bedroom d’in ganin yanayin da Sarki yake yasa d’aya yayi tsafi ruwa yabayyana a hannunshi yamakaka ma sarki nawar, ahankali sarki nawar yabud’e idanunshi nan Najla tayi saurin rungumeshi tace Abba me yasameka? Ya naji jikinka da zafi?.
Da idanu yabita yakasa ce mata komai saboda yanayin da yake ciki, Najla dafa k’irjinshi tayi tanemi tayi mashi tsafi daga haske yafito daga idanunta kafin yashiga jikin mahaifin nata sai hasken ya’bace nan ta ida rud’ewa tarasa me zatayi sakin Abban nata tayi tanufi wajen da Najma take tsaye har lokacin bata motsa ba, rik’o hannunta tayi tace dan Allah Najma kizo mutaimaka ma Abba yana cikin hali bansan me yasameshi ba…
Tun kan tarufe baki Najma ta fizge hannunta lokaci guda tahad’e fuska tace hakan ba zai ta’ba yuwuwa ba ke zaki iya taimakonshi ammah ni bazanyi hakan ba saboda bai cancanci hakan ba..
Mamakine yacika Najla nan tanemi kukan nata tarasa tana kallo Najma tajuya taficce daga cikin turakar..
Wasu hawayen ne suka gangaro mata tayi saurin komawa wajen sarki nawar tana ta’ba fuskarshi tafashe da wani sabon kukan tace bansan me zanyi maka kawarke ba Abba nah tsafina ya kasa taimaka min inwarkar da kai, kayi min magana Abba me yasameka?.
Da idanu kawai Sarki Nawar yake binta.
Juyawa tayi takalli ma’aikatan mahaifinta da suke tsaye su biyu tace kugaggauta kira min Tsoho Abnar yanzu…
Kafin tarufe baki har sun ‘bace.
Ba’a d’au wani lokaci me tsayi ba suka dawo tare da Tsoho Abnar cikin sauri ya iso wajen yana cewa me yafaru da Sarki Nawar d’in?
Fashewa da kuka tayi tace kaduba shi nima bansan abinda yafaru da shi ba.
Kallonshi Tsoho Abnar yayi yaga saidai yabi mutane da idanu ammah baya magana saita hannunshi yayi wajen k’irjin sarki nawar yaruntse idanunshi yafara karanto wasu d’alasimai ya dad’e yana karantowa kafin yabud’e idanunshi tashin hankali k’arara yabayya a fuskarshi yakalli Najla da ke tsaye ta yi zugum yace tabbas akwai matsala an jefi sarki da tsafi ta hanyar yi mashi asiri a cikin abinci.
Ya akayi hakan yafaru? Wanene yayi ma mahaifina hakan!!?,,, Najla tajefa mashi tambaya cike da tashin hankali.
Girgiza kai yayi yace wannan ne ban saniba saidai ya zama dole in sani, juyawa yayi yakalli mayun da ke tsaye yace kukoma akan aikinku.
Cike da girmamawa suka d’an rissina sannan suka juya suka fita.
Madubin tsafinshi yafiddo yad’aura a saman k’irjin sarki nawar nan yafara karanto wasu d’alasimai lokaci guda haske yabayyana a jikin madubin tsafin sai ga hoton Sarauniya Wailah ya bayyana ta’ba hoton yayi da yatsanshi nan yanuna parlorn sarki tun daga shigowar sarauniya wailah da nama har dawowar sarki yazauna yaci hatta murd’e murd’en da yayi saida suka gani
Najlah wata irin k’ara tafasa tadafe kanta da hannuwa biyu tace shikenan sun cutar min da Abba meyasa sukayi mashi haka? Saurin rik’o boka Abnar tayi da yake tsaye ya kasa ta’buka komai duk jikinshi ya yi sanyi tace dan Allah kayi wani abu akai bazan iya jure ganin Abbana cikin wannan yanayin ba…
Girgiza kai Boka Abnar yashiga yi yana kallon Sarki Nawar yace tabbas Wailah ta cutar da kai saidai na san wannan duk tsafin Boka Gobar ne dan shine kad’ai me k’arfin tsafi irin haka, kallon najla yayi da tasaki baki tana kallonshi jawayen fuskarta sun tsaya yace Najla ban san abinda zanyi ba saboda sihirinsu ya yi tasiri a jikinshi sun karya mashi garkuwar jiki….tun kan yarufe baki tuni Najla ta sulale k’asa a sume.