KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Ruwa yad’ebo yakwarara mata tafarka cikin sauri taje tarungume mahaifinta tana kuka..
Boka Abnar dafa k’irjinshi yayi da k’arfi yashiga karanto wasu d’alasimai da suka sa saida d’akin yad’an girgiza nan wani haske yafito daga cikin allon sihirinshi yadaki k’irjin Sarki Nawar sai gashi yana tari.
Saurin rik’o hannunshi boka abnar yayi nan Najla tayi murmushi tare da rungumeshi, ahankali murya chan k’asa yakira sunanta.
cikin jin dad’i ta amsa tace sannu Abbana meyasa Didi tayi maka haka?
‘Daga mata kai kawai yayi tare da yin d’an guntun murmushi ahankali yace Najla ba abinda yasameni na warke, sannan yamaida kallonshi ga Boka Abnar.
Yanayin yadda yake kallonshi yasa yagane akwai maganar da yake son yi dan haka yace Najla kid’an bani waje akwai wani aiki da zanyi yanzu.
Sumbatar goshin mahaifinta tayi sannan tamik’e ba dan ta so ba tafita.
Rik’o hannunshi Boka Abnar yayi yace hak’ik’a abokina banji dad’in abinda Wailah ta aikata maka ba shin meyasa takeson ganin bayanka?
Bud’e baki yayi ahankali murya chan k’asa yace Abnar shin akwai abinda nake aikata ba daidai ba a cikin mulkina? Shin ina nuna banbanci tsakanin jinsin fararen mayu da na bak’ak’en mayu?.
Girgiza kai Boka Abnar yayi yace kod’aya kai d’in me adalci ne.
Murmushin k’arfin hali Sarki Nawar yayi yace bansan me na aikata ma Boka Gobar da Sarauniya Wailah ba suke son ganin bayana tabbas sunyi nasara akaina tunda tsafinsu ya yi tasiri a jikina kuma bana bak’in cikin mutuwata saidai ina tsoron abinda zai faru da ‘yata Najla.
Girgiza kai Boka Abnar yayi yace kadaina cewa haka babu abinda zai faru da ita zan kular maka da ita sosai.
Cikin k’arfin hali yace ban san yadda rayuwa zata kasance ba saidai inaso ko bayan raina aba Najla sarautar k’asar nan dan itace kad’ai tacancanci tamulki k’sar nan idan har anaso asamu mulki cikin adalci inko har Najma ce nasan saidai akasin haka, gabad’ayansu ‘ya’yana ne kuma na san halin kowa ina da dalilin da yasa nace haka kasanar ma sauran manyan fadawa wannan maganar da nayi sannan inaso kafad’a ma Najla sirrin da muka dad’e muna ‘boyewa wanda babu wanda yasanshi inba ni da kai ba inaso itama tasani…
Hawaye ne suka gangaro ma boka abnar cike da jin tausayin abokin nashi yace ranka yadad’e zanyi dukkan abinda ka umurceni da shi saidai abun bak’in cikine ace na kasa taimakonka da komai akan lafiyarka.
‘Dan guntun murmushi Sarki Nawar yayi yace kar kadamu abokina daman tuni irin wannan ranar tadad’e tana bibiyata sai yanzu ubangiji gostan yanuna min ita…yana fad’in haka yaruntse idanunshi yafara bacci…
Hannu boka Abnar yad’aura akan fuskar Sarki Nawar yayi mashi tsafi dan samun sauk’in rad’ad’in ciwo sannan yamik’e cike da bak’in ciki yafito.
A parlor yasamu Najla zaune tana jira sugama tattaunawa tana ganin ya fito tayi saurin mik’ewa ta isa wajenshi, shafa fuskarta yayi yace kikwantar da hankalinki dasannu Sarki Nawar zai warke yakoma kamar yadda yake a da, wannan duk rad’ad’in zafin sihiri ne yake galabaitar da shi a yanzu zanje inyi bincike a d’akin tsafina zan samo mafita yadda zamuyi mukarya wannan sihirin da ke a jikinshi.
Saurin fad’awa jikin Boka Abnar tayi tafashe da kuka tace na gode sosai da wannan taimakon da zakayi mana ina tsoron inrasa mahaifina.
Shafa kanta yayi yace kar kidamu zanyi bakin k’ok’arina sannan kikula da kanki bari inje indawo.
‘Daga mashi kai tayi alamun toh nan yawuce yatafi ita kuma takoma cikin d’akin mahaifin nata tasameshi yana bacci, daga gefenshi tazauna tana kallonshi cike da jin tausayinshi cikin ranta tana mamakin abinda Didi ta aikata mashi, daga k’arshe tamik’e tafita daga d’akin har lokacin bata daina hawaye ba
Duk wannan abun da yake faruwa su boka Gobar suna kallo acikin madubin tsafinshi inda Najma ma take zaune a cikin d’akinta tana kallon komai.
Najla tana baro turakar Sarki tanufi ta Sarauniya Wailah tana zuwa aka bud’e mata k’ofa tashiga sai ganin Najma tayi zaune ta kame saman kujera tana murmushi, takawa tayi ta isa wajenta har ta bud’e baki zatayi magana, Najma tatari numfashinta tace na san kinsan komai akan abinda yafaru kuma wannan shirinmu ne.
Da mamaki Najla take kallonta tace kina nufin kinsan komai akan abinda Didi ta aikata?
Murmushi Najma tayi tace wannan duk shirinmu ne ni da Didi da kakana, taya kike gani zan iya bari Abba yace kece zaki gajeshi alhali ina raye, akwai wanda yadace yamulki k’asar nan ne baya na?
Cikin ‘bacin rai Najla tace indai har mulkin kikeso ai da baki biyo ta haka ba dan ni bana da ra’ayin mulkin kukyale min Abbana ku kuje kuyi ta mulkin.
Bushewa da dariya Najma tayi tace aikin gama ya riga da ya gama na rabaki da zoben nan bazai ta’ba dawowa gareki ba sannan zan hau mulkin k’asar Nairan agaban idanunki kizama k’ask’antatta agareni sannan mahaifin mu zai bar duniya…
Wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro ma Najla tace baidace kice haka ba Najma Abba bazai ta’ba mutuwa ba ina nan da ke sai ya warke kuma sai kun amshi hukuncin abinda kuka aikata..
Dariya Najma tashiga yi babu k’ak’k’autawa nan Najla tajuya a fusace tafita……..
Fitar Najla ya yi daidai da lokacin da madubin tsafin Najma yafara k’ara alamar sanarwa saurin d’akkoshi tayi taduba sai ganin Kakanta tayi ya bayyana a ciki, murmushi tasakar mashi tace ina farin ciki sosai Kakana komai yana tafiya yadda yakamata sannan ina farin cikin sanar da kai na yi nasarar samun zoben hannun Najla.
Bushewa da Dariya Boka Gobar yayi yace daman na san samun zoben ba abune me wuya ba saidai ya zama dole mugaggauta gama komai yanzu saboda Boka Abnar yana gab da ‘bata mana shiri yana hanyar shiga d’akin tsafin shi kuma Sarki Nawar ya sanar da shi cewa bayan ranshi Najla yakeso tagajeshi dan haka shima Boka Abnar bazamu ta’ba barinshi ba sai munga bayanshi a yanzu kigaggauta zuwa kishirya sannan kitura asanar da jama’a Sarki baya lafiya yadda suna taruwa wajen fada ni kuma zanyi amfani da damata inkashe Sarki kinga mutuwarshi zatayi daidai da hawan mulkinshi sai kibarni da Boka Abnar.
Bushewa tayi da dariya tace dakyau Kakana gaskiya wannan shirin naka ya yi ubangiji gostan yataimakeka.
Shima dariyar yayi sannan ya’bace daga cikin madubin tsafin nata.
Mik’ewa Najma tayi cike da farin ciki tashiga cikin d’akin baccinta dan tashirya
Najla na shiga turakar Sarki Nawar tasamu masu kula da lafiyarshi tsaye bisa kanshi dan tun bayan fitar Boka Abnar yafarka yafara wani irin tsanwan amai duk sun rikice sun rasa yadda zasuyi da shi Najla tana ganin haka tafasa k’ara tare da rugawa tarungumeshi tana cewa sannu Abba zaka warke bari inje indawo, tana mik’ewa yarik’o hannunta nan taja tatsaya tana cigaba da kuka idanu yazuba mata yana kallonta yakasa cewa komai, ida rikicewa tayi takalli masu yi mashi hidima tace kukama min shi mufita da shi muje d’akin abun bauta murok’eshi na san zai tausaya mana yawarkar da shi..
Cikin sauri suka cika umurninta suka d’auki Sarki Nawar suka fito parlor bud’e baki yayi dak’yar yace kusafkeni nan, cikin sauri suka nufi wajen kujera zasu d’aurashi sama yace a’a k’asa yake so nan aka kwantar da shi, kallon Najla yayi yana murmushi tare da yi mata nuni alamun taduk’o da kanta zama tayi gefenshi tana sha fa fuskarshi cikin sheshek’ar kuka tace kayi hak’uri Abbana muje d’akin abun bauta.
Rik’e hannunta yayi cikin dauriya da rad’ad’in ciwo yace sun rabaki da zoben hannunki ko?
Duk’ar da kai tayi batare da ta ce komai ba.
Murmushin k’arfin hali yayi yace na san hakan zata faru Najla kiyi hak’uri da duk abinda zai faru da ke wannan itace k’addarata sannan kije kisamu Boka Abnar zai sanar da ke wani sirri da babu wanda yasanshi idan ba ni da shi ba nasan shi zai zama kariya ga rayuwarki kar kidamu da duk abinda su Wailah zasu yi maki, hannunshi da yake runtse yabud’e nan wani zobe yabayyana yace amshi wannan kisa a hannunki na san zai taimaka maki.
Cikin kuka ta amsa tasaka sannan tace Abba muje akaika d’akin abun bauta.