HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Girgiza kai yayi yace a’a daidai lokacin yafara kakarin mutuwa hannunshi yasa yashak’e wuyanshi dak’arfi yabud’e baki yanaso yayi magana ammah yakasa nan kwayar idanunshi tazazzago waje, Najla mutuwar zaune tayi tana kallon mahaifin nata, daidai lokacin fadawanshi suka shigo d’akin cikin sauri dan tuni labarin halin da Sarki yake ciki ya riskesu suna shigowa numfashinshi yana d’aukewa.

Wata irin k’ara Najla tasaki tare da rungume gawar mahaifin nata su duka sukayo kanshi suka janye Najla suna ta’bashi suka gane babu rai a tare da shi nan d’aya daga cikinsu yace ubangiji gostan ya amshi abinshi wata irin k’ara tasaki taturesu gabad’aya takoma wajen gawar tarungumeshi tana cewa a’a Abba katashi kar katafi kabarni kamar yadda Ummana tatafi tabarmu.

‘Daya daga cikinsu ne yace ranki yadad’e saidai hak’uri, tsawa tadaka masu tace gabad’ayanku kufita kuban waje duk wanda yak’ara cewa Abbana ya mutu sai na kasheshi.

Cikin sauri gabad’ayansu suka fita suka bar d’akin yarage ita kad’ai sai gawar mahaifinta tarungumeshi tana ta rusa kuka….

Bakin Fada cika yayi mak’il da jama’a ana ta jira Fadawa sufito sufad’i halin da Sarkin nasu yake ciki suna fitowa daga cikin turakar Sarki suka sanar da jama’a Sarkin su ya cika, nan aka fara kururuwa ana koke koke daidai lokacin Najma tafito daga cikin gidan Sarauta sanye da kaya na alfarma hannunta rik’e da takobin Mullkin Sarki Nawar.
Kuyanginta ne suka zo da kujerar Sarauta sabuwa ta zinari suka ajiye a k’ofar Fada sannan suka take mata baya ta isa wajen kujerar tazauna, gabad’aya jama’ar da suke nan tsit sukayi suna binta da kallon Mamaki, kallonsu tayi nad’an lokaci sannan tamik’e tsaye cikin d’aga murya tace a yau mahaifina Sarkin garin nan ya mutu a yanzu nice shugabarku nice shugaba a k’asar Nairan ya zama dole kowane mahaluk’i yayi min mubaya’a fararen mayu da bak’ak’en mayu duk wanda yak’i haka zan kasheshi a yanzun nan zan shayar da takobina jininku,,, tana fad’in haka tazauna saman kujerar mulki tare da zare takobinta da take shek’i.

Gabad’aya dubban jama’ar fararen mayu da bak’ak’en mayu suka duk’a sukayi sujjada inda wasu suka dinga kwararowa daga wurare dadama suna yin sujjada haka aka dinga ‘bullowa ana sujjada dan muryarta saida takai duk inda ba’a tunani kuma kowa ya ji kiran da tayi, Murmushin jin dad’i Gimbiya Najma tayi sannan tabada izini kowa yad’ago kanshi, kallon Wazirin Sarki Nawar tayi da kanshi yake duk’e tace ya kamata kacika aikinka, cikin sauri yashiga cikin fada yad’akko hular sarauta wadda duk sarkin da zai hau ita ake sa mashi shedar an nad’ashi Sarki yazo yasaka mata a saman kanta sannan yad’akko takardar tsarin mulkin garin yamik’a mata nan aka sake duk’awa akayi mata sujjada, juyawa tayi takalli mahaifiyarta da take tsaye gefenta sukayi ma juna murmushin jin dad’i sannan tabada umurni kowa yamik’e tsaye, d’aga takobin hannunta tayi nan aka fara kururuwa ana mata kirari tana ajiyewa aka daina, juyawa tayi takalli Fadawa da suke sunkuye tace aje ashirya ma mahaifina afito da shi muyi mashi addu’a, amsawa sukayi da toh ranki yadad’e, juyawa tayi ‘bangaren da dakarun yak’i suke tsaye na ‘bangaren bak’ak’en mayu tace ku kuma kuje kufito min da ‘Yar uwata Najla ya zama dole tayi min mubaya’a a wajen nan, idan har ta k’i kud’akkota ta k’arfin tsiya kugurfanar min da ita a nan.
Amsawa sukayi da toh ranki yadad’e sannan kusan dakaru hamsin suka nufi cikin gidan Sarautar.

 

Har lokacin Gimbiya Najla tsugunne take a gaban gawar tana ta rusa kuka nan wata kuyanga daga jinsin fararen mayu tashigo cikin turakar sarki cikin sauri tamaida k’ofar tarufe cike da girmamawa tace ya shugabata ya kamata kitashi kibar masarautar nan dan a yanzu ‘yar uwarki ta aiko azo akawo mata ke, jama’arta suna nan dayawa sun nufo d’akinki.
‘Dago fuskarta tayi da tayi jajir saboda tsananin kuka takalli kuyangartata har ta bud’e baki zatayi magana sukaji anfara buga k’ofa dak’arfi, kuyangarce cikin sauri tanufo inda take tataimaka mata tamik’e tsaye tace na rok’eki kizo kigudu kibar garin nan kar ‘yar uwarki tacutar da ke ayanzu itace shugaba a cikin k’asar nan dole kowa yabi umurninta ke kad’ai nake ji dan nasan zata iya yi maki wani aabu
Girgiza kai Najla tafara cikin kuka tace kibarsu sushigo sukasheni rayuwata batada sauran amfani kiduba kiga Abba ne nan kwance a mace toh wane jin dad’i yarage min a rayuwa?

Cike da jin tausayinta tace duk da haka ranki yadad’e kiceci rayuwarki….bugawar da aka fara yi ne dak’arfi yasa duk suka juya suka kalli k’ofar duk k’arfin k’ofar ammah turota dakurun suke suna nema su’balleta dan cika umurnin shugabarsu a yanzu Gimbiya Najma………

 

_*Shin kuna ganin zasu samu nasarar kama Gimbiya Najla?*_
_*Shin Gimbiya Najla wane hali zata tsinci kanta a yanzu bayan ta rasa gabad’aya gatanta?*_
_*Ina labarin Boka Abnar da yashiga cikin d’akin tsafinshi?*_
_*Wane Sirrine wanda sarki nawar ya’boye babu wanda yasanshi sai shi da abokinshi Boka Abnar?*_
_*Kuna ganin cewa Najla zata samu damar tseratar da rayuwarta har taje wajen Boka Abnar yasanar da ita wannan ‘boyayyen sirrin?*_
_*Ina labarin Sarauniya Zaiba da tatura baiwarta taje tasamo mata maganin da zasu samu Yarima Ayran yaso d’iyarta Farha?*_
_*Shin zasuyi nasarar samun abinda suke so?*_
_*Shin kuna ganin Gimbiya Najma zata yafe ma Yarima Ayran laifin da yayi mata ko kuwa har yanzu tana nan akan bakanta bazata ta’ba hak’ura ba?*_

_Duk wani masoyina da masoyin novel d’in nan zai so jin amsoshin wad’annan tambayoyin.
kukasance da ni a cikin cigaban *KUWWA DA KUWWA* part 2_

*Ga duk me bukata zai biya Naira d’ari biyu (200) ta hanyar turo hoton katin MTN ko pin d’in katin ta wannan number 09035938246, ga masu yin transfer ta banki ga account number nan 3154324400 FIRST BANK, ga kuma wad’anda zasuyi Vtu zasu tuntu’beni dan jin k’arin bayani…

[ad_2]

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button