KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Boka Ambar ne yace ya shugabana Najla ta aikata zunubi ya kamata kufansheta da wani abun yanka mafi girma dan Gunki Gostan yagaugauta yafe mata.
Sarki ne yayi saurin cewa na fansheta da manyan shanu guda ukku.
Jinjina kai Boka Ambar yayi sannan yad’auki bokitin jinin yawatsa shi a bayansu inda sauran jama’a sukayi sujjada ahankali suka d’ago kansu tare da shafa gashin kansu sannan suka mik’e tsaye, wasu halittu masu kama da doduna ne suka fiddo manyan ganguna suka fara kad’awa nan aka fara rera wak’a kowa yana kai hannunshi wajen wuta yana d’an ta’bawa sannan yajanye hannun cikin sauri suna cikin haka dajin ya amsa da wata irin k’ara me kama da kukan hadari nan take gabad’ayansu suka zube k’asa sukayi sujjada, k’asa ce tafara girgiza duk sai kowa yayi tsit, walkiya tafara haskawa lokaci guda wutar tamutu duk sai suka d’ago kansu ahankali hayak’ine yakauraye dajin a tsakiyar inda suka kunna wutar sukaga wani Dodo k’ato fari fat da shi da ka ganshi kamanninshi irin na tsohon biri ne abun tsoro zaune yake bisa wata kujera gashi duk ya baje mashi fuska, in ba ka saba ganinshi ba idan ka hangeshi daga nesa sai ka sume..
A karo na biyu suka sake duk’awa sukai sujjada sannan Boka Ambar yamik’e tsaye yafara kirari yana cewa muna mik’o gaisuwa ya shugaban fararen mayu, rayuwarmu fansace agareka ya kai shugaba Dodo Farras a yau ne shekaru biyar suka cika shekarun da muke sadaukar da rayuwar d’aya daga cikin fararen mayu gareka dan samun kusanci da kai shugaban Fararen mayu wanda muka gaji hakan tun kaka da kakanni.
Wannan dodon numfashi kawai yake safkewa yana bin jama’ar da sukayi sujjada da kallo yana bud’e hanci, Boka Ambar saurin zubewa yayi saman gwiwoyinshi tare da runtse idanunshi, wata irin murya sukaji wadda tasa gabad’ayansu saida suka firgita saboda k’arfi da k’ararta gabad’aya dajin saida ya amsa…..
Na ji dad’in zagayowar wannan ranar a yanzu zan gabatar da takobina agareku duk inda yatsaya ya zama dole abani d’aya daga cikin dangin wanda tatsaya wajenshi kunsan haka al’adar take idan har kuna son cigabanku da samun d’aukakarku da ta jikokinku fararen mayu a cikin garin Nairan.
Su dukansu amsawa sukayi da mun yarda da haka ya shugabanmu mu masu biyayya ne agareka.
Hannunshi yad’aga sama sai ga wata farar takobi tazinari ta bayyana a hannunshi runtse idanunshi yayi yafara karanto wasu d’alasimai nan gabad’aya jamar wajen suka mik’e tsaye kowa yayanki gefe guda yatsaya shi kad’ai tare da runtse idanunsu.
Sunyi kusan awa d’aya a haka sannan suka fara jin motsi kamar na tafitar ingarmar doki, ahankali yasaki takobin hannunshi nan tafara tafiya saman iska tatunkaro wajen da dubban jama’ar suke tsaye mata da maza yara da k’ananu bin tagabansu tadinga yi d’aya bayan d’aya saida tazagaye gabad’ayansu sannan a karo na biyu tatunkaro wajen da su sarki Nawar suke tsaye tana zuwa sai jin k’arar fad’uwarta sukayi k’asa dak’arfi nan gabad’aya kowa yabud’e idanunshi dan ganin inda wuk’ar tafad’a sai ganinta sukayi a gaban Sarauniya Nuwaira, duk wani mahaluk’i da yake wajen sai da yafirgita dan hakan bai ta’ba faruwa ga sarki ba sai wannan karon, shi kanshi Sarki Nawar zufa ce tafara kwarara a jikinshi yana kallon Sarauniya Nuwairah da tayi mutuwar tsaye, muryar Dodon sukaji yana cewa maraba gareki ya ke takobina a yau kin taki babbar sa’a dan kin fad’a a babban gida mafi girma da daraja a cikin garin Nairan, ya kai Sarki Nawar a yau gidanka nabak’unta dafatan zakayi farin ciki da wannan bak’uncin nawa albarkata tacigaba da yad’uwa a cikin gidanka dan haka ya zama dole kabada d’aya daga cikin iyalanka jinsin fararen mayu inyi romo da kansu insha jininsu dan samun albarkata.
Jikin Sarki Nawar rawa yafara yi nan da nan tsoro yad’arsu a ranshi dan ko kad’an bai ta’ba tunanin hakan zai faru a cikin iyalansa ba kallon Gmbiya Nuwairah yayi da itama take kallonshi hawaye sun wanke mata fuska, gabad’aya jama’ar wajen tsit sukayi dan abun ya basu mamaki sosai.
Sarki Nawar maida kallonshi yayi ga Dodo Farras cikin sauri yazube k’asa yayi sujja cike da girmamawa yace ya shugabana ina neman alfarma a wajen……wata irin gigitacciyar k’ara suka ji anyi cikin murya me ban tsoro akace babu neman alfarma a duk lokacin da muka buk’aci rayuwar mutum d’aya daga kowace zuri’a bayan kowane shekaru biyar wannan babban kuskure ne agareka ka san sharud’d’an mu ya zama dole abamu indai har anason cigaba da rayuwa inko ba haka ba zamu k’wata ta k’arfin tsiya yanzu za’bi ya rage gareka kabamu ‘yarka ko matarka.
Nan hankalin Sarki Nawar ya ida tashi cikin sauri yad’ago kanshi gabad’aya yama rasa ya zaiyi, muryar yaji a karo na biyu ance dak’ik’u kad’an suka rage maka inba haka ba mu zamu za’ba da kanmu.
Gimbiya Nuwairah tana jin haka tayi saurin rik’o mijin nata hawaye suna cigaba da wanke mata fuska tace ya kai mijina wannan itace ranar da nake ce maka na san bazan cigaba da rayuwa ba ni zan je dan Allah kakular min da d’iyata sosai dan Najla itace rayuwarmu daga ni har kai.
Saurin girgiza kai yayi yace a’a Nuwairah hakan ba zai yuwu ba kibarni ni na za’bi inmutu ku kuma kuje kucigaba da rayuwa ke da Najla dan bana son in rasaku ina k’aunarku sosai.
Murmushi tayi tace shin ka amince kasa’ba ma al’adar da aka gada tun kaka da kakanni dan kawai saboda mu? Baka tsoron abinda zai biyo ba? Kai fa sarkine kuma jama’a na buk’atar cigaba da zama da kai nidai dan Allah kakular min da ‘yata kar kamance itace rayuwarmu zamu iya sadaukar da komai saboda ita miyasa bazaka bari intafiba bayan ka san umurnine daga shugabanmu abun bautar mu.
Shuru sarki Nawar yayi yana sauraren matar tashi nan wata irin tsawa tafara tashi wani rami ne yabayyana a chan wajen da Dodo Farras ya’bace murya ce suka jiyo daga cikin ramin ana cewa lokaci yana k’ure maka ya kai sarki Nawar!!!…….
_*Part 1 Free pages ne*_
_Gareku masoya Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_
*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAWUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA*_
_(Bata korar buzu)_
_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_
_Follow me on wattpad Sis-Nerja_
_Facebook user name: Sis Nerja’art_
_PART 1_
*PAGE 4*
Gimbiya Najla ba k’aramin tashin hankali tashigaba akan rashin mahaifiyarta Sarauniya Nuwairah da tayi gabad’aya kuyangi da bayinta sun tausaya mata dan shi kanshi Sarki Nawar ba’a magana dan baya jin kanshi gani yake Najla akayi ma mutuwar ba shi ba, gabad’aya daina zama tayi cikin gidan sarautar tana ke’be kanta a chan cikin lambun gidan tasha kukanta ita kad’ai in ta gaji tayi shuru abu d’aya yake d’ebe mata kewa wata yar tsuntsuwace me kyau k’arama idan tasafka a wajen da Najla take zama sai tayi ta yin abinda zai d’ebe mata kewa haka zata shagala tana kallonta har sai zuciyarta ta rage daga k’unar da takeyi mata bata dawowa turakarta har sai gari ya yi haske lokacin baka ganin kowa waje gabad’ayansu suna ‘boye kawunansu a cikin gida saboda gudun kar zafin rana yata’basu yayi masu illa a jiki dan safiyarsu itace matsayin darensu lokacin ne suke samu sukwanta suhuta kafin rana tafad’i sufito sufara hidimunsu na yau da kullum…