KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Yau ma Sarki Nawar ne yatunkaro turakar Najla tun kan ya isa kuyanginta suka dinga zubewa suna kwasar gaisuwa a nan ne d’aya daga cikinsu take shaida mashi Gimbiya Najla tana chan cikin lambu dan haka yanufi lambun…
Yana isa yasameta zaune ita kad’ai ta zuba ma gefe d’aya idanu tana kallo…
Zama yayi gefenta yai gyaran murya juyowa tayi takalleshi da rinannun idanunta sai kuma tajuyar da kai
Cike da jin tausayinta yace ya ke ‘yata hak’ik’a na san irin bak’in ciki da k’uncin da kike ciki akan rashin mahaifiyarki da kikayi saidai nima duk yadda kikeji nima kaina ina ji saidai ganinki a cikin wannan yanayin ya fi komai sosa min rai kina ware kanki ke kad’ai kizauna sannan ni kaina kin daina bari inganki bare har indinga ganin kyakkyawan murmushin nan naki da yake k’ara k’awata wannan fuskartaki na rasa gane kanki har na fara tunanin shin ko nima bana kyautata maki?
Saurin girgiza kai tayi tare da rik’o hannuwan Abbanta fuskarta d’auke da nadama tace kayi hak’uri kagafarceni Abbana ko d’aya ba haka bane narasa yadda zanyi in tursasa ma zuciyata akan inkoma yadda nake ammah na yi maka alk’awali zanyi k’ok’arin hakan dan farin cikinka dayardar abun bautarmu,
Shafa kanta yayi cikin jin dad’in furucinta yace nagode sosai ‘yah ta
Murmushi tasakar mashi nan shima yamaida mata martani……
Tun daga lokacin Najla tarage shiga damuwa saboda kar tatashi hankalin mahaifinta, duk rana Sarki Nawar sai ya je ‘bangaren Najla kusan sau biyar ya dubata duk wannan abun da yake ashe akan idanun Gimbiya Najma da mahaifiyarta nan abun yafara basu haushi…
Wata rana Najma ta je ‘bangaren Ssrki bayan ta dawo daga wajen kakanta boka gobar nan Fadawa suke ce mata ai bai dad’e da baro Fada ba suna tunanin yana chan wajen gimbiya najla…
Ran Najma ‘baci yayi har takasa ‘boye ‘bacin ranta cikin d’aga murya tace wai me Abba yake nufi da ni ne meyasa yakeson fifita wacchan farar mayyar akaina?
Ganin yadda tad’au zafi yasa gabad’aya fadawa suka zube k’asa cikin girmamawa sukace Dodo Gostan yahuci ran gimbiya
Ko kallon inda suke batayi ba nan tawuce cikin sauri tafita daga fadar ganin kamar zata ‘bata lokaci yasa ta’bace sai gata a ‘bangaren Gimbiya Najla fararen kuyangi suna ganinta sukayi saurin bud’e mata k’ofa dan basu iya ja da ita duk ma wanda yaso yayi mata gardama zai iya rasa rayuwarshi gabad’aya sun san halinta sosai bata d’aukar raini suna bud’e k’ofa sarki yana fitowa daga cikin bedroom d’in Najla nan yaja yatsaya a parlor yana kallon yadda tashigo rai ‘bace.
Tana isowa wajenshi d’an rissinawa tayi sannan tad’ago tace Abba na je turakarka aka ce min kana nan wajen najla
Murmushi yayi yace hakane ‘yah ta na zo duba ‘yar uwarki ne kinsan tun da tarasa mahaifiyarta take cikin kad’aici dole mudinga rage mata kewa…
Cikin d’aga murya tace to menene a ciki dan ta rasa mahaifiya ina ce ita d’in ta rasa ranta a hanya me daraja ba abun farin ciki bane agareta? Wanna daidai ne ace ka ba Najla gabad’aya lokacinka ni da mahaifiyata mudinga zuwa fada da turakarka ammah bamu samunka kullum maganar d’aya ce ace kana wajen Najla shin Abba Najla itace kad’ai d’iyarka da zaka fifitata akaina???
Ganin yadda take d’aga murya yasa sarki yace Najma ya isa haka bana fifita d’aya akan d’aya ko da ace kece kike cikin halin da Najla take ciki zan kula da ke kamar haka gabad’ayanku ‘ya’ya na ne ya kamata kidinga sanin maganar da zaki furta min a matsayina na mahaifi agareki
Ran Najma k’ara ‘baci yayi ganin yadda mahaifinta yake d’aga mata murya daidai lokacin Najla tafito daga cikin bedroom d’inta saboda hayaniyar da taji da mamaki take kallon Najma da tasan tabbas muryarta ce tajiyo wani irin k’ask’antaccen kallo Najma tayi mata sannan tajuya cikin sauri tafita tabar d’akin…
Juyowa Sarki yayi yakalleta hawaye ne suka cika mata idanu tajuya cikin sauri takoma cikin bedroom d’inta tare da maida k’ofa tarufe dan haka ne Sarki Nawar yajuya yafita daga ‘bangaren yana jin babu dad’i a ranshi…..
Cikin ‘bacin rai tashiga ‘bangaren mahaifiyarta Sarauniya Wailah da kuyanginta duk saida sukayi mamakin ganinta a wannan halin nan take tasallami kuyanginta suka fita suka bar d’akin rik’o Najma tayi suka zauna sannan cikin nuna damuwa tace fad’a min wanene yata’ba min ke acikin fad’in garin nan? Taya zaki bar ranki ya’baci alhali kina da ikon taka kowa acikin garin nan a matsayinki na d’iyar sarki me jiran gado, ban sanki da fushi da yafiyaba kitaka duk wanda yayi maki kar ki rangwanta mashi….
Ajiyar zuciya Najma tasafke sannan tace Didi da ace ba Abba bane wani nadaban ne yayi min abinda Abba yayi min da sai na ga bayanshi
Idanu Sarauniya Wailah tazuba mata cike da mamaki tace wani abun ne yafaru?
Girgiza kai tayi tace menene ma bai faruba bansan abinda yake damun Abba ba bansan abinda yasa yake fifita Najla akanmu ba sahin ta fi mu ne a wajenshi?
Yatsina fuska Gimbiya Wailah tayi tace ke ma kike fad’a ana ji ai ni tuni na gama fahimtarshi akan yarinyar nan abinda yasa nake sharewa saboda a yanzu uwarta bata raye ni kad’ai ce agabanshi inyi kid’i da rawata babu abinda zai dameni
A fusace Gimbiya Najma tace idan ke babu abinda zai dameki to ni ina da shi dan na tsani yarinyar chan na tsani inbud’e idanu inganta acikin gidan nan ammah dasannu zanyi maganinta zan nuna mata cewa ni d’innan jikar Boka Gobar ne idan har kyau take tak’ama da shi zan ‘bata mata fuskarta ta yadda kowa zai tsani ganinta…
Murmushin jin dad’i Sarauniya Wailah tayi tace dakyau d’iyata wannan fusatar da kikayi ya tabbatar min da zaki iya komai kuma na ji dad’in hakan dan haka wuk’a da nama suna hannunki ko kad’an ban ce kiraga mataba kibi kowace hanya wajen ganin kin tauyeta batare da mahaifinku ya saniba saboda gudun kar wani abu yabiyo baya….
Ban damu da duk abinda zai biyo baya ba Didi nidai burina inga bayan Najla.
Jinjina kai Sarauniya Wailah tayi cikin ranta tana jinjina ma d’iyartata da kwata-kwata batada tsoro, zugata tadinga yi akan tasan yadda zatayi taga bayan Najla tarihinta yashud’e kamar yadda na mahaifiyarta yashud’e
Gimbiya Najla ce zaune a saman kujerarta ta sarauta inda kuyanginta fararen mayu sun zagayeta suna ta mata hidima k’wank’wasa k’ofa akayi nan tamaida kallonta ga k’ofar masu tsaron k’ofar ne suka bud’e wasu tsaffi biyu fararen mayu suka shigo daga cikin kuyangin mahaifiyarta idanu tazuba masu tana kallonsu suna matsowa wajen kujerar da take zaune suka zube suna kwasar gaisuwa kanta kawai tagyad’a masu alamun amsawa sannan suka d’ago kansu cikin girmama sukace ya shugabarmu sak’o ne daga Sarki shugaba ya ce a yanzu muje da ke chan turakar Sarauniya Nuwairah kiduba yadda aka tsara ancanza komai na ciki anzuba kayan ado da alatu na aban ado daban daban a yanzu ya zama mallakinki ke kad’ai munsan zaki fi k’aunar chan fiye da nan..
Shuru Najla tayi tana saurarensu dan ko kad’an batayi tunani hakan daga mahaifin nasuba saidai ta san ya yi hakan ne dan yasake kwantar mata da hankali
Gudar kuyangar ce tace ranki yadad’e idan kin bamu dama zamu iya sawa ad’aukeki keda kujerarki yazuwa turakar
Batare da tayi magana ba nan tamik’e gabad’aya kuyangi da bayin da suke cikin d’akin suka zube suna kwasar gaisuwa cikin girmamawa batare da ta kulasuba tawuce gaba duk suka mik’e suka bi bayanta