KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Suna fita ‘bangaren Sarauniya Nuwairah da yasha gyara suka nufa komai na cikinshi sabone anzuba kayan alatu da ado sosai har ya fi nata had’uwa mamakine yakamata taja tatsaya takalli d’aya daga cikin dattijon kuyangin tace sharmiza yaushe aka yi wannan shirin batare da na saniba
Cikin girmamawa tace ranki yadad’e kusan sati guda kenan sarkine yabamu umurnin hakan yace kar mubari kisani har sai idan mun gama ya yi hakane dan kawai yasaki farin ciki
Murmushi tayi ba tare da ta ce komai ba tawuce tana cigaba da duba ko’ina cikin ranta tana jinjina ma mahaifin nata da irin k’aunar da yake nuna mata daga k’arshe tayanke shawarar zuwa wajenshi dan haka tawuce gaba kuyanginta suna take mata baya har fada Sarki yana hangota yayi saurin mik’ewa daga saman gadon mulkinshi yaje yatareta murmushi Najla tasakar mashi tare da sunkuyawa alamun girmamawa saurin d’ago mata kai yayi yarik’o mata hannu sukaje suka zauna saman gadon mulkinshi sallamar duk fadawanshi yayi suka fita daga cikin fadar yarage daga shi sai ita
A karo na biyu Najla tayi murmushi sannan tarik’o duka hannuwan mahaifin nata tace Abbana hak’ik’a na yi farin ciki sosai da irin k’aunar da kake nuna min saurin d’aura hannunshi yayi a saman bakinta yace kidaina cewa haka Najla hakan da nake maki shine daidai ina k’aunarki sosai kamar yadda nake k’aunar mahaifiyarki a yanzu kece kad’ai nake gani madadinta inji dad’i tun bayan tafiyar Nuwairah bana iya barcin kirki ina ji a raina kamar akwai ranar da abun bauta zaya maido min ita saidai nasan hasashen da nake bazai ta’ba zama gaskiya ba dan Nuwairah ta dad’e da barinmu bazamu sake ganinta ba
Hawaye ne suka gangaro ma Najla sai a lokavin tace Abba na bi duk hanyar da tadace ammah bansamu nasarar samun Umma ba dan alk’alamin tsafina yana nuna min cewa bata raye tuni su Dodo Farras sun shanye jininta sun ba abun bauta gangar jikinta,,, tak’arashe maganar tana hawaye
Jikin Sarki Nawar ya yi matuk’ar yin sanyi da jin kalaman da d’iyartashi tayi tabbas baiyi mamakin hakan ba dan shima kanshi ya san abinda tafad’a haka yake shima ya yi bakin k’ok’arinshi abinda tsafinshi yake nuna mashi kenan ya san tuni rayuwar Nuwairah ta k’are yana so ne yakwantar ma d’iyartasu hankali ne sai gashi ta san komai agame da hakan
Najla ganin yadda yayi shuru yasa tamik’e tana jin yadda zuciyarta take tafarfasa sai a lokacin sarki yadawo hayyacinshi rik’o hannunta yayi yafiddo zobe a cikin alk’yabbarshi yazira mata a babban yatsa idanu tazuba ma zoben tana kallon yadda yake ta k’yalli yahaska mata hannu lokaci guda hawaye suka gangaro daga idanunta ahankali tace Ummana
Cikin sanyin jiki yace a yau na cika umurnin mahaifiyarki ya ke ‘yata inaso kisan cewa wannan zoben tun kaka da kakanni muke da shi kuma muna saka ma matanmu fararen mayu kawai saboda kinsan mu d’in mun fito daga jinsin fararen mayu wannan dalilin ne yasa kowane sarki da zai mulki garin nan yake mallaka ma matarshi har sai lokacin da rai yayi halinshi muka koma a duniyar Dodo Farras sannan ‘ya’yanmu wad’anda zasu gaji sarauta suke mallakarshi suna sa ma matansu toh ni kuma a yanzu kinga banda wani d’a namiji wannan dalilin ne yasa nake da burin ace ke kika mallakeshi ashe itama mahaifiyarki ta ci burin hakan dan kawai saboda ta san nima zan so hakan, ina fata zaki kula da shi sosai kar kibari kirabu da shi akowane lokaci yakasance yana tare da ke Najla rabuwa da shi daidai yake da rabuwa da mulkina sarautar k’asar nan zata iya komawa hannun bak’ak’en mayu
Najla jikin mahaifin nata tafad’a tare da fashewa da kuka tace Abbana nagode sosai da irin k’aunar da kake nuna min ina sonka sosai mahaifina
Shafa kanta yayi yace kar kidamu Najla duk abinda nayi maki cancanta ce tasa haka nima kaina ina k’aunarki sosai
K’arar da suka jiyo ne daga wajen fada yasa Sarki Nawar yayi saurin janyeta daga jikinshi tare da sakar mata murmushi yace kishiga cikin gida ta k’ofar baya a yanzu na yi bak’i suna gab da isowa cikin fadar nan
Murmushi itama tasakar mashi tare da jawo hannunshi tasumbata sannan taruntse idanunta tafara karanta wasu d’alasimai sai gata ta ‘bace ‘bat a daidai k’ofar gidan nasu na sarauta ta’bulla inda tabar kuyanginta suna jiranta ganinta yasa duk suka duk’a suna kwasar gaisuwa batare da ta amsaba tawuce gaba tanufi ‘bangaren Sarauniya Wailah d’aya daga cikin kuyanginta ne tace ranki yadad’e nan ai hanyar ‘bangaren Sarauniya ne
Murmushi tayi tace ina sane da hakan
Su dukansu jinin jikinsu suka sha sai d’aya daga cikinsu tayi k’ok’arin cewa ranki yadad’e kigafarcemu muna jin tsoron shiga ‘bangaren Sarauniya Wailah, ja tayi turus tatsaya batare da ta juyo ta kallesuba ganin haka yasa mai maganar tacigaba da cewa ba dan komai ba sai dan yadda take nuna mana a matsayinmu na kuyangin mahaifiyarki na tabbata shigarmu a cikin turakarta sai ta azabtar da mu kitaimaka kibarmu kitafi da ko d’aya daga cikinmu..
Shuru Najla tayi tana saurarenta tabbas abinda tafad’a ta san gaskiya ne dan ita kanta ta ta’ba gane ma idanunta hakan a lokacin da mahaifiyarta ta aiki wasu kuyanginta sukai ma Sarauniya Wailah wata kyauta nan fa tadinga fad’a tasa Ba’kak’en bayinta suka dinga azabtar da su ba ita tabarsu suka fito ba saida tak’one masu jiki da wutar tsafi sannan tasa aka fiddosu aka yada a k’asa wanda dalilin hakan yasa suka mace, sannan ta aika ma Sarauniya Nuwairah da sak’on gargad’i kar tak’ara bari Kuyanginta sushigo mata cikin turaka idan ko ba haka ba sai ta dinga rabasu da rayuwarsu duk abinda takeso ko zata kawo tazo dakanta ko tasamu bak’ak’en kuyanginta tabasu sukawo mata…
Jin ta yi shuru yasa gabad’ayansu suka zube suna neman gafararta ahankali tace zaku iya komawa ke kuma sharmiza kizo muje tare
Tun kan tarufe baki gabad’ayansu suka ‘bace sai dai sharmiza da tarage nan Gimbiya Najla tawuce Sharmiza tana take mata baya har cikin parlorn Sarauniya Wailah inda bak’ak’en kuyanginta suke cike mak’il suna ta mata hidima isowarta a cikin parlorn yasa gabad’aya suka juyo suna kallonta tamkar tauraruwa dan ta sha kyau da kayan ado sosai, Gimbiya Najma da ke zaune kusa da mahaifiyarta idanu tazuba ma Najla tana mata kallon mamaki inda itama Sarauniya Wailah kallon da take mata kenan…
Cikin tafiyarta ta k’asaita ta iso wajen kujerar mulkin Sarauniya Wailah tana zuwa tataka matattakar zinarin da ke shimfid’e a k’asa ta ida isa wajen kujerar, Gmbiya Najma ce a fusace tace minene dalilinki na zuwa cikin turakar mahaifiyata?
Batare da ta bata amsaba taduk’a k’asa gefen k’afar Sarauniya Wailah suna ganin haka suka kalli juna suka yi murmushi, Najla jin shuru Wailah bata dafa kanta ba yasa takai hannu zata ta’ba k’afarta tureta Wailah tayi tai saurin mik’ewa tsaye tace kar kisaki kita’ba min k’afa domin ni ba uwarki bace..
Jin haka yasa jikin Najla yai sanyi sosai dariyar Najma tajiyo tana cewa taya a matsayinki na farar mayya zaki zo kidafa k’afar mahaifiyata ko itama d’in kurwarta kikeson ci ko zuciyarta dan ku fararen mayu haka kuke baku barin bak’ak’en mayu dan kunsan zuciyoyinsu suna da dad’i sosai idan aka gasa
Cikin sanyin jiki Najla tamik’e tana murmushi tace na zo ne inkawo sak’on gaisuwa agareki Didi dan a jiya Ummah tacika sati biyu da barin duniya ammah ban ganku kunzo min yau ba kamar yadda aka saba a al’adar garin ana zuwa a kunna wuta azauna ana kukan bak’in cikin rashin da akayi ni kuma saidai nayi ni da kuyangina,,, tak’arashe fad’a k’wallah ta cika mata idanu