HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Gimbiya Wailah da Najma bushewa sukayi da dariya saida sukayi me isarsu sannan Najma tace taya kike tunanin zamu zo maki bayan kinsan a yanzu ke ba kowa bace awajenmu mahaifiyar da kike tak’ama da ita ta bar duniyar inaso kisan cewa zaki cigaba da zama cikin gidan sarautar nan saboda mahaifinmu kawai ammah daga inda yashud’e kema kanki dole kibar gidan nan

Najla idanu tazuba mata cike da mamaki take kallonta dan a yanzu ta ida gasgatar da k’iyayyar da suke nuna mata ta zarce tunaninta hannu tasa tagoge hawayen da suka gangaro mata karaf idanunsu suka kai akan zoben da ke hannunta lokaci guda sukayi saurin ja da baya suna mata kallon mamaki…

Gimbiya Najla bata gane abinda yasa su haka ba tajuya cikin sauri tanufi hanyar fita daga cikin turakar inda Kuyangarta da ke chan nesa da su tayi saurin zuwa tatake mata baya suka ficce……

 

_*Part 1 Free pages ne*_

_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_

 

*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*

_Sis Nerja’art✍????_
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA…*_
_(Bata korar buzu)_

_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_

_Follow me on wattpad: Sis-Nerja_

_Facebook user name: Sis Nerja’art_

_PART 1_

*PAGE 3*

Gimbiya Nuwairah ture Sarki Nawar tayi cikin sauri tajuya tanufi wajen ramin, sarki Nawar yana ganin haka yai saurin bin bayanta har ya kusa isa wajenta nan wani abu me kama da glass yabayyana a gabanshi yashiga tsakaninsu bubbugawa yadinga yi tare da k’wala ma Nuwairah kira, saida ta isa wajen ramin sannan tajuyo takalleshi fuska duk hawaye sannan tajuya tafad’a ciki, wata irin razanannar k’ara yasaki nan yasulale k’asa a sume.

 

……Gmbiya Najla a firgice tafarka daga baccin da take tare da fasa k’ara da dukkan k’arfinta tace Ummahhhhh!

Gabad’aya kuyanginta suka bayyana a cikin d’akin lokaci guda, janye blanket d’in da take lullu’be da shi tayi tamik’e cikin sauri hanyar k’ofa tanufa tana zuwa tabud’e dagudu tafita kamar zata tashi sama inda kuyanginta suka take mata baya daidai da zata fita daga gate d’in gidan aka shigo da Abbanta a sume, tana ganin haka ta ida tabbatar ma kanta abinda tagani acikin mafarkinta gaskiya ne dan haka tasulale a nan wajen tasume nan ma aka sake wani rikicewar…..

Duk wannan abun da yake faruwa Gimbiya Najma tana kallo acikin madubin tsafinta murmushin mugunta kawai takeyi,,, tana gama gani tamik’e cikin sauri tanufi ‘bangaren mahaifiyarta Sarauniya Wailah tana zuwa tasameta zaune tsakiyar bak’ak’en kuyangi da bayinta ganin Gimbiya Najma yasa gabad’ayansu suka zube k’asa jiki yana rawa suka fara mik’a gaisuwa ammah ko kallonsu batayi ba tanufi wajen mahaifiyartata tana cewa Didi yau ina cikin farin ciki na zo maki da albishir me dad’i…..
Cike da d’oki Gimbiya Wailah tagyara zama sannan tace ina saurarenki ya annurin zuciyata da wane irin albishir ne hakan kika zo min ko kina nufin kin samu abokin rayuwa.

Lokaci guda Gimbiya Najma tahad’e fuska batare da ta ce komai ba saida tayi shuru na kusan minti goma sannan tayi murmushi tace Didi kece kad’ai zaki iya min maganar aure in iya yafewa dan bana k’aunar maganar bazan ta’ba auren wani mahaluk’i ba acikin jinsin nan namu har sai lokacin da nasamu sarautar garin nan nazama abun koyi da burgewa a ko’ina..
Murmushi Sarauniya Wailah tayi cikin jin dad’in abinda d’iyarta tafad’a tace dakyau Annurin zuciyata ina jin dad’in hakan a duk lokacin da kika nuna kina da gurin zama magajiyar sarautar mahaifinki, ammah ya kamata a yanzu kisanar da ni abinda yasaki farin ciki har naga fuskarki ta nuna murnar da ban ta’ba ganin irinta ta shimfid’u akan fuskarki ba.

Fashewa tayi da dariya tace fiye da hakan ma zaki gani a fuskata nazo ne inmaki albishir da mutuwar Sarauniya Nuwairah wadda aka sadaukar ma Dodonsu da ita a wajen bautarsu.

Wani irin dad’i Sarauniya Wailah taji tace kin tabbata Najma hakan ya faru da gaske?

Had’e fuska Gimbiya Najma tayi tace Didi tunda nake ban ta’ba zuwar maki da labarin da bai faru da gaske ba tabbas abinda nafad’a maki gaskiya ne.

Bushewa da dariya me k’arfi Sarauniya Wailah tayi tace tabbas wannan labarin da kika zo min ya yi min dad’i sosai ya ke ‘yata,,, mik’ewa tayi tanufi wajen bangon tsafinta tatsaya nan tafara rubuta wasu abubuwa da ba wanda zai iya gane abinda take rubutawa dan rubutun ya yi kama da na ‘yan china.

Mik’ewa Gimbiya Najma tayi tabi bayanta wani irin haske ne yabayyana a jikin allon lokaci guda yad’auke sai ga hoton sarki da Najla kwance shame shame a k’asa a sume kuyangi da fadawa suna ta k’ok’arin d’aukarsu dan sushigar da su cikin turaka.
Sarauniya Wailah kallon Najma tayi nan suka bushe da dari saida suka natsa daga dariyar da suke sannan Gimbiya Najma tace ba haka naso ba Didi naso ace har da rayuwar Najla tasalwanta dan na tsaneka na tsani inbud’e idanuna inganta a cikin gidan nan nice kad’ai wadda yakamata akalla dasunan d’iyar Sarki Nawar….

Kar kidamu da wannan ya ke d’iyata kibarta itama d’in da sannu tarihinta zai rushe acikin masarautar nan….
Su dukansu dariya suka sace kyalkyalewa da ita a karo na biyu saida sukayi me isarsu sannan suka tsagaita da dariyar da suke cike da annashuwa da farin ciki dan ranar yau ta kasance masu tamkar ranar haihuwar su……..

A chan ‘bangaren Sarki Nawar lokacin da yafarfad’o daga doguwar sumar da yayi Boka Abnar ne tsaye a gefenshi yunk’urin tashi zaune yayi nan Abnar yataimaka mashi yace kabi ahankali ya shugabana jikinka babu k’arfi sosai.

Wasu irin hawaye ne masu zafi suka gangaro mashi yayi saurin rik’o hannun Boka Abnar yace ya kai abokina hak’ik’a wannan ranar ta kasance min ranar bak’in ciki agareni ban ta’ba tunanin zan rasa Nuwairah ba bansan wane hali ‘yata zata shiga ba akan rashin uwa da tayi…..
Saurin toshe mashi baki da hannu boka Abnar yayi yace kadaina cewa haka kar ka aikata sa’bo alhali ka san wannan shine zai sa albarka yacigaba da yad’uwa a cikin iyalanka shekaru dubu kenan ana wannan bautar duk bayan shekara biyar sannan kafin kai iyalan sarakuna kusan d’ari aka sadaukar ko ka mance da Sarki Humaiza da yarasa tilon d’iyarshi a dalilin gasar, ko ka mance da Sarki Naffar da yarasa d’anshi da yafi k’auna a duniya?

Ajiyar zyciya Sarki Nawar yasafke tare da sa hannu yagoge hawayen fuskarshi

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button