KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Boka Abnar cigaba yayi da cewa Kar kamance idan da ace Sarauniya Nuwairah bata salwantar da ranta ba da d’iyarka Najla zasu d’auka sannan zaka aikata babban zunubin da Dodo Farras bazai ta’ba yafe maka ba kar kakasance cikin sarakuna marassa biyayya kamar irinsu Sarki Kamir wanda yanuna taurin kai daga k’arshe yarasa sarauta da mulkinshi hatta dukiyarshi ta dalilin haka sarauta tadawo cikin zuri’arku shekaru dubu ukku da suka shud’e….
Girgiza kai Sarki Nawar yayi yace Abnar baka fahimce ni ba ina tsoron halin da Najla zata shiga na tabbata a yanzu haka tana cikin mawuyacin hali.
Tausayinshi yakama Abnar yace dole ne sai kunji wannan rad’ad’in daga kai har Gimbiya ammah ya kamata katuba kanemi gafarar Dodo Farras dan nasan a yanzu yana fushi da kai sosai
Jikinshi sanyi yayi yace hakane kaje na baka izini kasa ayanka duk wata dabba da tadace anema min yafiyar Dodo Farras sannan zuwa anjima zanje dakaina cikin d’akin tsafi in nemi yafiyarshi dakaina, ina fatan hakan yayi.
Murmushi Abnar yayi yace tabbas hakan ya yi na tabbata Dodo Farras zai safko daga fushin da yake da kai..
Shima murmushin yayi yace zan aikata hakan ya kai abokina yanzu bari inje inga halin da Najla take ciki kaje kashirya duk abinda yadace da nadawo muwuce d’akin Dodo Gostan…
Saurin mik’ewa Abnar yayi yace angama ranka yadad’e,, d’an rissinawa yayi sannan yajuya cikin sauri yafita yabar turakar.
Wasu zafafan hawaye ne suka zubo daga cikin idanun sarki Nawar nan yafara tunanin daren jiya da yau yadda Sarauniya Nuwairah tadinga nunawa kamar daman ta san zata bar duniyar,,,
A fili yace kodai Dodo Farras yana fushi akan ‘boyayyen sirrina wanda daga ni sai Abnar muka sanshi saisa yahukunta ni ta hanyar rabani da Nuwairah,, gabanshi wani irin mummunan fad’uwa yayi yai saurin runtse idanunshi sai kuma chan yabud’e cikin sauri yamik’e yafita daga cikin turakarshi….
_________
Gimbiya Najla bud’e idanunta tayi dak’yar ahankali tafara tuno abinda yafaru da ita wasu irin hawaye ne masu d’umi suka kwaranyo daga cikin idanunta cikin sauri tatashi zaune kuyanginta ne kewaye da ita daga masu yi mata tausa sai masu yi mata fifita tsawa tadaka masu wadda tasa saida d’akin ya amsa, cikin sauri jikinsu yana rawa suka ‘bace gabad’ayansu yarage ita kad’ai ce a d’akin dafe kanta tayi da dukkan hannuwanta biyu tafara rusa kuka tana cewa shikenan Ummana na rasaki a daidai lokacin da nake buk’atar kasancewa tare da ke wanene zai kula da ni alhali baki kusa da ni bazanso kisalwantar da ranki saboda ni ba ya zama dole in d’akko ki a duk inda kike….
Saurin ta’ba hannuwanta tayi nan ‘yar computer tsafinta tabayyana zoben hannunta taciro tad’aura a saman computer wani farin haske yabayyana fara dannawa tayi tana motsa baki ahankali wani bak’in d’aki yabayyana wata irin k’ara taji wadda bata ta’ba jin irinta ba dan saida tarazana nan take hasken computer yad’auke gabad’aya, cikin sauri taruntse idanunta tare da d’aura hannunta saman computer tafara karanta wasu d’alasimai sai ga hasken computer ya dawo bud’e idanunta tayi batare da ta daina karanta d’alasiman tsafin ba wannan bak’in d’akin yasake bayyana a fuskar computerta wasu arrors guda ukku suka bayyana tayi saurin danna wajen d’aya nan hasken d’akin yabayyana…
Hoton Sarauniya Nuwairah tagani kwance k’asan d’akin daga gefenta wuta ce take ci inda jinin jikinta yake gangarowa yana shiga cikin wutar tana ta k’ara huruwa da ka gani ka san babu rai a tare da ita….
K’ara Najla tasaki tare da ture computer gefe daidai lokacin Sarki Nawar yashigo cikin sauri ya iso inda take yana zuwa ya rungumeta jikinshi.
K’ara sautin kukan tayi tace Abba na rasa Ummana yanzu shikenan sun kasheta sun shanye jininta meyasa hakan yafaru? Meyasa ni baku sadaukar da ni ba ga Dodo Farras shin baku tausaya min ne? Kunfi son incigaba da rayuwa akan ummana? Ko bakusan halin da zan shigaba idan har narasaku??
Jikin Sarki Nawar sanyi yayi sosai yashafa kanta cikin jajircewa da dauriya yace ya ke ‘yata inaso kisani ni kaina ba a son raina hakan yafaru da Ummanki ba dan naso ace ta bari na salwantar da rayuwata ku kucigaba da take rayuwar, banason abinda zai rabani da ku, yau ina cikin matsanancin tashin hankali bansan ya zanyi ba, taya zan iya rayuwa babu d’aya daga cikinku
Saurin d’ago kai tayi takalleshi da idanunta da suka rine kamar garwashin wuta, girgiza kai tayi tace a’a Abba na fi son cigaban rayuwarku sama da tawa nice yadace ace bana raye….
Saurin sa hannu yayi yatoshe mata baki yace kidaina cewa haka Najla ina sonki fiye da yadda kike tunani bana son inga ranar da zan rasaki ke kanki kin san hakan wannan dalilin ne yasa kullum ina bincike akan rayuwarki duk wani abu da naga yana k’ok’arin cutar da ke ina rabashi da ranshi kiyi hak’uri da wannan k’addarar da tasamemu kiyafe min dan duk nine silar barin mahaifiyarki daga wannan duniyar
Tsayawa tayi tana kallonshi cikin rashin fahimtar inda zancenshi yadosa ganin yadda shima yake hawaye yasa tausayinshi yakamata tasa hannu tagoge mashi hawayen sannan tasakar mashi murmushi tace kadaina damuwa Abbana nima na daina daga yanzu bana son abinda zai ja inrasaka ina tsoron fushin Dodo Farras yahau kanka ya kamata muje mukusantar da kanmu da abu mafi girma dan neman yafiyarshi
Wani irin dad’i Sarki Nawar yaji ganin yadda tayi saurin fahimtarshi tagane ba shi ne yasadaukar da mahaifiyartaba, haka yacigaba da lallashinta har saida tad’an safko sannan yasa tatashi tasa alk’yabba suka fito yana ri’e da hannunta, fadawa, bayi, kuyangi jibgi guda ne a tsaye sunyi layi a wajen fada kowa ya yi tsit ahaka su sarki suka ratso ta tsakiyarsu duk inda suka zo wucewa sai mutane sun yi sujjada suna kwasar gaisuwa ahaka har suka isa wajen fada inda Boka Gobar da Sarauniya Wailah sai Gimbiya Najma suke tsaye su dukansu kowa ya sha alk’yabba ja sarki yayi yatsaya har lokacin yana rik’e da hannun Najla, d’ago kai tayi tasafke idanunta da sukayi jajir a kan fuskarsu Najma nan duk suka mik’a mata hannunsu na dama (a al’adarsu idan har akayi rashin wani yamutu to da anmik’a maka hannu tarik’e shine alamun anyi maka gaisuwa) tsayawa tayi tana kallon hannuwansu kamar bazata mik’a nataba saidai chan tamik’a ma Boka Gobar da Sarauniya Wailah, idanunta tasafke a fuskar Najma nan Najma tasakar mata murmushi k’wallar da take mak’ale a idanun Najla ne tagangaro sarki ne yad’an ta’bata sannan tamik’a ma Najma hannu ido cikin ido haka suka kalli juna kafin daga baya tajanye hannunta nan Sarki Nawar yaja hannunta suka shiga cikin fada nan d’in ma wasu dubban mutanen ne tsaye suna ganin shigowarsu Sarki suka zube suna kwasar gaisuwa ahaka su Sarki suka wuce zuwa saman karagar mulki yazauna bisa gadonshi na azurfa da lu’ulu’u nan Najla tazauna gefenshi tsoho Abnar ne yamatso yad’an rissina yagaishesu sannan yamik’a ma sarki hannu yai mashi gaisuwa daidai lokacin wasu mutane biyar suka shigo d’auke da makara ana zuwa aka ajiye a gabansu Sarki, Najla tana tozali da alk’yabbar da mahaifiyarta tasa ranar hawaye suka shiga kwaranya daga idanunta tayi saurin sa hannu tatoshe bakinta..
Boka Gobar da su Najma ne suka iso wajen makarar suna zuwa nan Sarki da Gimbiya Najla suka mik’e tsaye gabad’aya mutanen cikin fadar kowa yaruntse idanunshi Boka Gobar yafara karanta wasu d’alasimai na tsafi lokaci guda wuta tafara cin wannan alk’yabba hayaki yakauraye fadar…