HAUSA NOVELKUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

KUWWA DA KUWWA Complete Hausa Novel

Sarki Nawar da gimbiya Najla kukan zuci kawai suke su dukansu ransu ya yi masu zafi akan rashin Nuwairah inda su Gimbiya Najma suke ta farin ciki a cikin ransu suna jin ranar yau ta fiye masu kowace rana.
Sunyi kusan minti goma a haka kafin daga baya Boka Gobar yayi shuru duk kusan lokaci guda suka bud’e idanunsu sai gani sukayi wannan alk’yabba ta k’one k’urmus saidai toka a cikin makarar, Najla fashewa tayi da kuka tare da yin baya zata fad’i sarki yai saurin tarota tafad’o jikinshi a sume

Ganin haka yasa Tsoho Abnar yayi saurin kiran fararen kuyanginta suka zo suka kamata aka fita da ita

Tokar aka had’a waje guda aka juye cikin wata had’ad’ar kwalba ta zinari yamik’a ma Sarki Nawar….

Sarki Nawar yana kar’ba nan yaji hawaye sun cika mashi idanu jikinshi yad’auki yin ‘bari saurin mik’a ma Tsoho Abnar yayi yajuya cikin sauri yafita yabar fadar

Gimbiya Najma da Sarauniya Nuwaira murmushi sukayi sannan suma suka juya suka fita daga cikin Fadar

Tsoho Abnar ne yad’aura kwalbar a saman karagar sarki nan duk suka duk’a cikin girmamawa sannan kowa yajuya yafita yabar Fadar…….

 

_*Part 1 Free pages ne*_

_Part 2 na kud’i ne za’a sameshi a naira d’ari biyu (N200) kacal tahanyar turo kati Mtn digit ta wannan number 09035938246 ko kuma ayi transfer ta account number 3154324400 *First Bank* zaka tura shedar biya ta hanyar yin screenshot a wannan number 09035938246_

 

*GARA’BASA! GARA’BASA!! GARA’BASA!!!*
_Akwai gara’basar k’ayatattun novels d’inmu guda ukku zaku samesu akan farashi me sauk’i ???? *KUWWA DA KUWWA* na Sis Nerja’art, tare da novel d’in *SAHUN GIWA* na sharararriyar marubuciyar nan watau *HAFNAN* sai littafin *MARUBUCIYA* na fasihar marubuciyar nan *UMMUDILSHAD*_
_Za’a samesu gabad’aya cikin sauk’i da rahusa akan naira d’ari biyar (N500), ga masu buk’atar biyu daga ciki zasu turo naira d’ari ukku (N300), ga wad’anda zasuyi transfer ta bank ga account number d’in da za’a turo ta shi 0824409678, (Mustapha Hafsat Access Bank), ga kuma wad’anda zasu turo katin zasu turo *Mtn* digit ga wannan number 07013872581_
_kar kubari abarku baya acikin wannan gara’basar ko da kud’inka sai da rabonka_
*Muna maraba da masoyanmu????????????*

_Sis Nerja’art✍????_
[8/31, 8:16 PM] Mu’az: _*KUWWA DA KUWWA…*_
_(Bata korar buzu)_

_Story nd Written_
*By*
_Sis Nerja’art✍????_

_Follow me on wattpad Sis-Nerja_

_Facebook user name: Sis Nerja’art_

*GARGA’DI*
_Wannan labarin k’irk’irarren labari ne ban yarda wani ko wata su sarrafa min labari ba ta kowace fuska batare da izini na ba_

_PART 1_

*PAGE 1 nd 2*

K’asar *Nairan* k’asa ce da takasance k’asa mai yalwatar arzik’i kuma k’asar ta shahara a duniya kasancewar k’asar mayu ne kad’ai suke rayuwarsu a cikinta babu bil’adam ko d’aya duk mutumin da yayi gigin zuwa garin saidai yazama gawa.

maitar tasu ta samo asaline tun kaka da kakanni, za’a iya cewa gadarta suke inda wasu kuma tasu maitar takasance ana samar masu da ita ne ta hanyar tsafi.

A tsarin garin duk jaririn da aka haifa a ranar za’a kaishi wani d’akin tsafinsu da suke kira d’akin *Dodo Gostan* inda yakasance ana ajiye jariri tsawon awa ukku a ciki indai har jariri baiyi kuka ba toh tabbas ya kasance acikin mayu wad’anda suka gaji maita.
Inko har jariri yayi kuka toh hakan yana nufin bai kasance daga cikin mayu ba dan haka shugaban matsafansu wanda yake mallakin d’akin dodonsu gostan shine zaiyi amfani da sihirinshi ta hanyar maida jaririn nan yazama maye.

Da haka ne duk wanda yataso tun kaka da kakanni yake kasancewa maye a garin hakan shine al’adarsu kuma addininsu.

Abinda zai baka mamaki halittun da ke cikin garin basu kasance mutane bane saidai sun kasance masu siffa biyu wani ‘bangaren jikinsu na mutane wani ‘bangaren kuma na wata halittar daban ammah duk da haka akwai wad’anda tawayar da ke tattare da su batada yawa saidai suna amfani da k’arfin tsafinsu wajen canza halittarsu irin yadda suke so takasance…

A garin suna da wani sarki da ake kira da Sarki Nawar, sarkin ya kasance daga cikin fararen mayu kuma sun gaji maita tun kaka da kakanni yana da dukiya me tarin yawa wadda takasance ya gada tun zamanin kakanninshi na goma sha ukku sannan masarautar garin abun kallo ce saboda anzuba dukiya wajen ginata ta k’ayatu yadda yakamata duk mulkin mutum idan da zai samu damar zuwa k’asar Nairan sai ya raina kanshi domin mulki, Sarauta, izza, k’arfin dantse duk sarkin ya had’a, duk da haka abinda zai fi baka mamaki shine sarkin yana shimfid’a mulkinshi cikin adalci wa jama’arsa.

Yana da mata biyu inda tafarkon takasance cikin bak’ak’en mayu d’iya ce ga babban bokan garin watau Boka Gobar ita kad’aice d’iyarshi tana da kyau na gani na fad’a sun had’u da sarki ne wata rana ya kawo ma boka gobar ziyara a gidanshi lokacin da yaje bai sameshi ba yana d’akin tsafinshi shine ita tafito dan tashaida ma sarki mahaifinta baya nan tun daga nan da sarki yak’yalla idanu yaganta yakamu da sonta dan haka yasanar da boka, shi kuma baiyi wata wata ba wajen amince ma shugabanshi aka sha shagalin bikki.
shekararsu goma da aure sannan suka samu haihuwar d’iya mace wadda taci suna Najma ta kasance daga cikin bak’ak’en mayu sannan ta gaji maita wajen iyayenta.

A lokacin da suke shekara ta sha d’aya da aure ne yak’ara aure inda ya auro wata kyakkyawar mata wadda a k’asar aka k’iyasta babu me kyaunta dan batada tawayar komai, saidai abinda jama’ar k’asar suka kasa ganewa inda Sarki yasamota har sukayi aure sunyi amfani da tsafi wajen ganowa ammah sun kasa gano komai kan dole suka hak’ura dan haka ne ba wanda yasan sirrin sai shi kanshi Sarki da wani malaminshi kuma abokinshi Abnar,

Abnar abokine ga Sarki Nawar tun yarintarsu sun kasance aminnan juna kamar yadda iyayensu ma haka suka kasance.

Bayan ya auro matar shi Nuwaira wadda takasance daga cikin fararen mayu tana zaune da mijinta lafiya ta kasance macece me tausayi da son jama’a, suna da shekara biyu da aure sannan tahaifi d’iyarta mace ranar da tahaifeka gabad’aya k’asar saida labarin haihuwar yakewayeta dan a tarihin k’asar Nairan ba’a ta’ba haifo yarinya me kyaun jaririyar Nuwaira ba saidai ita d’in ba fara bace sosai kamar sauran fararen mayu ba kuma zata shiga layin bak’ak’ensu ba dan tana da haskenta sosai saboda haka ne aka dangantata ga fararen mayu kamar iyayenta, koda aka kaita d’akin dodo gostan bila’adadin jama’a sukaje suka zagaye d’akin dan jin shin jaririyar zata yi kuka ko bazatayi ba.
Har tsawon awa biyu shuru batayi kuka ba ana saura dak’ik’a talatin afiddota jaririya tafara tsala kuka nan hankalin sarki yatashi sosai da d’iyarshi bata kasance daga cikin mayu wad’anda suka gaji maita ba, ammah da yayi wani tunanin sai yashare dan hakane boka gobar yai tsafi aka sa ma jaririyar maita, da haka ne akayi suna akai shagalin da ba’a ta’ba yi a garin ba inda yarinya taci suna Najla.

 

Najma da Najla sun taso basu jituwa a tsakaninsu shekaru biyu ne tsakaninsu, tun suna yara mahaifinsu yake k’ok’ari wajen ganin sun had’a kawunansu ammah hakan bai yuwu ba dan haka hankalinshi yatashi saboda yana son yaran nashi sosai duk lokacin da zaije fada tare da su yake zuwa kujerar Najma tana a gefen haggunshi inda ta Najla take a gefen dama,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button