NOVELSUncategorized

KWARATA 22

       Allah kuwa ya saka ma nemanshi albarka dan kano yake zuwa sarin atamfofi da shaddoji da yadika ,kafin shekar ya zagayo abubuwa sun fara canzawa domin Allah yasa ma neman albarka kuma Allahn ya yaddar mishi ! Dan ubangiji dayace maka zama zaka zama….

       Haka rayuwa taci gaba da tafiya cikin ƙanƙanin lokaci sunan Dikko Muhammad wato kakana ya fara zagawa a cikim garin katsina dan zuwa wannan lokaci ya baza yara suna neman mishi kuɗi dan kasuwar tafi ƙarfin mutum yanzu, kuma mutum ne shi mai kauta ,

      Shi kuwa Muhammad baban Dikko wato kakan babana ganin dukiya ta fara yawa hankalinshi ya fara tashi gashi har yanzu Dikko baiyi auren farko ba , kuma zuwa wannan lokaci ya rage zuwa gida dan sai yayi wata shidda ko fiye da haka baije gida ba , idan yaje malam yayi mishi magana yana daɗewa baizo ganin gida ba sai yace abubuwa sunyi yawa yanzu ma dakel ya samu yazo,

     Ganin haka yasa malam ya yanke shawara aura wa Dikko mata kuma “yar nan cikin ƙauyensu dan malam yace idan “yar gida ce yake aure dole za’a riƙa ganinshi ko baizo dansu ba zaizo dan matarshi,

Haka kuwa akayi malam ya aurowa Dikko mata bada saninsa ba yasa aka kawo mishi amarya har katsina, saida aka kawo amarya akayi masa bayani malam ya auro masa ita , bai wani ji komai ba yace Allah ya basu zaman lafiya, 

      Zaman lafiya sukeyi da matarshi Binta saboda matace mai haƙuri da kuma kauda kai da duk wani abu na rayuwa , saboda itama sai tayi wata nawa bata ga Dikko ba dan shi ba auren yake saurare ba duniyar kawai yake nema ita kuma Binta bata wani damu ba tunda ci da sha har sutura bata rasa ba , idan Dikko yazo mata as miji zasuyi rayuwar aure idan baizo ba babu abinda ya dameta…

       Haka dai rayuwarsu taci gaba da tafiya , kuɗin Dikko kuma har an fara zarginsu a cikin gari cewa tsafi yake yi , dan shima kanshi zuwa yanzu baisan iyakar abinda ya mallaka ba , koda Binta ta samu ciki gida Dikko ya maida ita ta aihu , tunda ya kaita bai sake komawa ba har ta aihu ta gama wanka baije ba, abinda ta aifa ma bai gani ba babanshi yayi duk abinda akeyi ma duk macen data aihu komai anma Binta da ɗanta da yaci suna Ummar wato mahaifina…

     Har Umar ya iya tafiya Dikko bai dawo ba kuma bai aiko ba yana can yana neman duniyarshi danshi matan ma basu ne gabanshi ba kuɗi kawai, baisan komai ba kuma baya gane komai sai naira , abun ƙauye aka fara tira iyayen Binta su kashe auren su mayar da Baban Dikko ɗansu tunda dai ɗanshi ya zama ɗan iska, Binta kuwa ta kifa kanta ƙasa tace ita duk duniya babu wanda ya isa ya kashe mata aure,

      Ganin za’a kashe mata aure dole yasa ta saɓe abunta ta dawo wurin mijinta , koda Dikko ya dawo gida ya sameta yaji daɗin dawowanta yace tayi haƙuri abubuwa ne sunka sha mishi kai da yawa da yawa shi yasa baizo ba , tace ba komai da yake itama bata da matsala.

      Can ƙauye kuwa da aka tabbatar da Binta ta koma wurin Dikko iyayenta sunsha zagi da tirr da Allah wadai da halin ɗiyarsu, basu da yadda zasuyi tunda suma basu san Binta zata koma wurin Dikko ba dan batayi shawara dasu ba ta tafi.

      Tun lokacin da Binta ta dawo wani abu bai shiga tsakaninta da Dikko ba , ita kanta wahalar gani yake mata dan yanzu kasuwancin nashi ya fara ketarawa , kuma babu damar taje ta faɗa gida dan tun abun baya damunta yanzu harya fara damunta.

     Yau kam ta hana idonta bacci ko Dikko zai kai safiya bai dawo ba zata jirashi kuma yau za’ayita ta ƙare , koda Dikko ya dawo gida daɗin bakin yayi ma Binta kuma ta haƙura amma kam a daren nan sunɗan caskaɗe dan tunda ta dawo wannan shine haɗuwarsu na farko,

    Tou haka kwanciyar auren ta koma duk lokacin da Dikko ya kwanta da binta wani rantsetstsen rabo zai fita , adadin yawan “ya “yansu adadin yanda Dikko ya kwanta da ita , yanzu tayi yara bakwai ,

Kuma rabonshi da gida tunda ya maida Binta aihuwar Babana bai sake zuwa ba har Binta tayi “ya “ya bakwai , saida itace kaɗai take zuwa, mahaifin Dikko kuwa yayi danasanin kai Dikko birni ,

     Haka rayuwar taci gaba da tafiya saida malam ya rasu Dikko yaje ƙaunye ta’aziyya, mahaifiyarshi kuma tayi kuka da tir da rayuwar birni, da yake shegen wayau ne dashi lallashinta yayi saida ya kwantar mata da hankalinta sannan yace tunda bata da komai a ƙauye zai tafi da ita birni !

      Haka kuwa akayi bayan addu’an bakwai suka tattaro suka dawo tare da kakar babana, zaman kakarsu dady ta gano Dikko bata mace yake ba , ta jinjina wa Binta da wannan haƙuri, ita dai batace komai ba tana dai kallon ikon Allah..

      Ummar wato Dadyna, yana gama secondry sch Dikko ya korashi ƙasar waje karatu dan bayasan ganin yara kusa dashi, tafiyar Ummar babu daɗewa kaka Dikko ya tsirawa kanshi aure rana guda aka kawo mishi mata biyu shi mai kuɗi, idan an haɗa da binta sun zama 3 kenan.

Nan fa haihuwar gasa ta tashi mata sunga kuɗi duk shekara sai an direwa Dikko “ya “ya amma banda Binta dan ita tana mamakin ma yaushe Dikko yake kwanciya dasu sakamakon ita ? Ko kuwa dandai su shine ya auro su da kanshi Oho,

       Tunda Dady ya tafi karatu Kaka Dikko ya hanashi dawowa , da yaga mai zai matsa mishi saiya dawo ya tusheshi da kasuwa can yace ya nemi kuɗi ya manta da rayuwar nigeria shima haka babanshi yayi mishi.

       Duk da Ummar yana ɗan farko saida Binta tayi magana a maido mata ɗanta karya halaka cikin duniya , Dikko yace bazai maido ba, shi ya akayi bai ɓace ba da babanshi ya kawoshi birni, dole Binta ta haƙura ta dainawa Dikko maganar Ummar , itama kakar Dady tayi harta gaji Dikko bai dawo da Ummar ba,

        Kwanci tashi asarar mai rai , abubuwa da dama sun faru a ciki kuwa hada rasuwar Kakar Dady , Dady kuma yayi shekaru kusan 15 yana ƙasashen yahudawa, tun yana marmarin gida shima harya goge ya janye zance gida a rayuwarshi.

       Shi kuwa Dikko yanzu hankalinshi ya tashi saboda mata sun tara tulin ɗiya sai meeting ɗin kasheshi sukeyi su kwashi dukiya , wannan dalili yasa ya cire Binta a gidan ya sake mata mazauni ita kaɗai daga ita sai “ya “yanta dan ya lura itace kaɗai take masa san tsakani da Allah.

       Tou wannan dalili ne yasashi ya ɓanɓako dady daga ƙasar waje shi kuma zuwa wannan lokaci baya san dawowa nigeria dan shima ya riga ya kafa kanshi a can yayi kuɗi wanda saida suka tadawa Dikko hankali duk neman duniyarshi, yace Ummar da nasan zakayi kuɗi duniya da na zauna na mori rayuwata ban ba kaina wahala wurin tara abun duniya ba,

       Dikko dai bai ɓoyewa Ummar komai ba ya sanar dashi cewa mata zaku kasheshi su gaji duk dukiyar daya sha wahala wurin tarawa , dan haka abinda Dikko yayi shine , duk abinda ya mallaka tsakanin gidaje filaye motoci filazozoji Dikko ya kasasu 10 ya bawa Ummar kashi 9 sannan yayi rabon gado da kashi ɗayan daya rage,

       Duk wacce ta samu kuɗin nan ruɗewa tayi dan wannan kuɗi da Dikko ya bada gado wa duk “ya “yanshi iyakar almubazzarancin mace rayuwar duniya dai ba ƙiyama ba ya isheka, ganin kuɗaɗe a hannunsu kuma sun tabbata babu saura yasa kowa ta tsige aurenta ta kama gabanta…

      Aure Dikko ya nemowa Dady ɗiyar wani aminishi suma attajirai ne na gaske , babu wani ɓata lokaci suka anshi tayin Dikko bikin bai wani ibi lokuta ba aka daura mishi aure da matarshi Maryam , mai irin sunan Sultana…

      Dady bai daɗe da aure ba , Kaka Dikko da Kaka Binta sukayi gobara gaba ɗaya gidan babu wanda ya fita , duk wanda suke uwa ɗaya da dadynmu wuta ta cinyesu sun mutu har lahira, Dady yayi kuka na tashin hankali duk mai imani saida ya tausawa Dady,

      Rayuwar dai haka taci gaba da tafiya , kakana na wurin uwa shine ya cusawa dady ra’ayin siyasa kuma Allah yasa ya shiga siyasar da sa’a domin ya riƙe manya manyan muƙamai dan siyasa tayi dashi kuma tana cikin yi dashi daga baya kuma ya tsaya takarar gwamna kuma Allah ya bashi yaci , 

         Matan dadyna 2 a yanzu suka rage masa dan shima ya ɗan ɗana aure aure dan samun namiji amma Allah bai bashi ba , harya haƙura ya fidda rai Allah yasa ya sameni daga tsakiya dan mata sune samana kuma suke ƙasa na a cikinsu na rayu dasu nake gogayya banda aboki sai mata shi yasa ni ban ɗauki mace komai ba dan duk wani feleƙe da iyayi na mata babu abinda za’a layancemin , zancen cin cingom da duk wasu ɗabi’u na mata duk a wurin “yan uwana na koya, amma bana ɗabi’u irin na “yan daudu kuma bana magana irin na mata…

        Ina da ilimin addini domin nima sittin ce cikin kaina nasan hadissai sosai duk ƙaunar da ake nunamin da sangarta baisa na zama sakarai ba nasan abinda nake , tunda nake dadyna da mom ina basu taɓa dukana ba babu mai dakamin tsawa kuma babu wanda yakemin kallon banza tunda nake ban taɓajin kalmar zagi akaina ba saida Allah yasa an mata ta shigo rayuwata, itace mutum ta farko data fara zagina a rayuwa.

      Nima haka tunda nake ban taɓa neman mata ba kuma bana sabgar su akan ta ne na nuna mazantaka na, ni ba sakaran namiji bane ƙaddara ce kawai kuma bansan abinda hakan yake nufi ba , 

      Gashi ta shigomin rayuwa banda isashshen lokacin da zanyi maganinta dan nima babana ya ƙusani cikin siyasa, ya fiddo ne akan wata kujera ta abokinshi daya rasu kuma inaji a jikina nine dan ban taɓa nema na rasa ba tun ina ƙarami duk abinda naso a rayuwata bai taɓa wuceni ba , dan bana san siyasa a rayuwata amma dole sai nayi ta.

      Mu fitaccin mutane ne muna da cikken asali bama da wani tambari na ɓatanci haka kuma bamu da sata bamu da maita , mu ba ɓoyayyin mutane bane sananni ne kuma fittaci tun zamanin iyaye da kakanni, haka nima sananne ne kowa ya sanni kasancewar ɗa ɗaya tal namiji a wurin mahaifina , shi yasa ban ɓoyu ba domin dady ya ɗaukeni kamar abokinshi baya ɓoyemin komai duk wani samunshi a tafin hannuna yake , ragamar komai a hannuna yake , dan zaka tara matashi kamarni wanda akeji dasu ko sukeji da kuɗi wallahi ka tara matashi talatin maiji da kuɗi da motoci basu Dikko ɗaya duk yawansu wallahi.

       Daga yau wallahi nayi rantsuwa idan har Sultana ta sake shigowa rayuwata saina keta mata mutunci wanda yafi wanda nayi mata a baya…..


       Taff wannan shine ƙudirin Dikko , ita kuma bara muji nata .

Hafsa kuwa tunda Dikko ya zageta fess take kuka, 


          Ni kuma bacci ɗaya nayi na farka ina tunanin yadda zan hudowa lamarin Hafsa…….

Previous page 1 2

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button