NOVELSUncategorized

KWARATA 28

???? —— 28

        Kallo Alhaji ya bini dashi mai nuni da yama rasa abinda zaicemin , murmushi nayi tare da cewa da Allah kar kaga kamar cin fuska ne ko wani abu ko zaka taimakamin naga hoton matar ka ?


      Me yasa kike son ganin hoton matana ko zakije ki haɗamu da ita ne ? Ya ƙarasa maganar cikin sigar barkwanci , murmusawa nayi tare da cewa haba Alaji yadda da arne shi yake sa aci yankashi , kuma daɗin aure kesa mata tace miji Baba… Ganin hoton iyalinka bashi ne yake nuni zan faɗa ba , nasan gidanka komai da komai naka na sani hoto kawai zan gani sai nayi gaba abuna…


(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9704, ‘t’: ‘160 by 600’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


      Amma kafin na tafi don Allah me yaja ra’ayinka ka afkowa matan bariki bayan ka baro naka matar gida ? Ɗaure fuska yayi tare da cewa me yasa kike so kimin haka wai ? Dani dake da ku dukanku taimakekeniyar juna mukeyi manta da lamarin matana da kuma abinda yasa na faɗo barikinku mu fuskanci abinda ke gabanmu !

       Miƙomin wayar yayi da hoton zuƙeƙiyar matarshi wacce ta gaji da haɗuwa duk inda ake neman mace takai kuma duk inda ya nuna matanshi abun kallawa ce , gaba ɗaya tafi su Amisty komai na morewa amma bata kai diddigen Sultana ba , danni a tara mace dubu baza’a iya samo ɗaya kamarni ba ,

       Caf na faɗa tare da kallon Alhaji sannan nace wannan kyakkyawa ya akayi ka baro kyau siga da nagarta ka faɗowa kwarin mata ? Me matan bariki suka fi matar ka ? Me yasa ka kashe sunna kake ƙoƙorin ɗabbaƙa zunubi ? Me yasa kabaro inuwa ka dawo rana ? Ya akayi kabar rahama ka dawo azaba ? Me matan bariki sukafi matar ka don Allah ? Me ya ɗaukar maka hankali da macen bariki har ka baro taka kazo wurinmu……. ?

      Kallo Alhaji ya bini dashi na kece abun tausayi mai ƙaramar shekaru dake kina ɗaukar kayan daya fi ƙarfinki , kamar nasan abinda ke zuciyarshi nace manta dani ka fuskanci taka rayuwar , nasan matsayin zina , illolinta matsalolinta wahalhalunta tashin hankalin dake cikinta da kuma bala’en dake tare da ita , san zuciya da ɗaukar huɗubar shaiɗan ya mantar dani , domin yawan kusantar saɓo yana hana ganin girman zunubi , kasan surar da Allah ya sauke akanmu mu mazinata , ina matsalar take tsakanin kai da matar ka ne ?

       Gyara zama Alhaji yayi sannan yace :• me yasa matan bariki suka fi iya jan hankalin namiji ? Ba tare dana kalleshi ba nace shaiɗan ne yake ƙawata maka su domin yasan zina hanyace da take kai mutum ga halaka , zina tana zubar da mutinci tana rage ma mutum daraja a wurin ubangiji sannan mutuncin shi zai ragu a wurin al’umma kuma zina tana rage ƙwarjini fuska ,

       Har yanzu baka bani amsar tambaya na ba , miya ja ra’ayinka shiga harkar bariki wai ? Alaji yace matan bariki kullum a shirye suke basa taɓa gajiyawa da ansar buƙatarka duk lokacin daka zo musu zasu anshe ka cikin farin ciki ba tare da gajiyawa ba , zaka kwanta da mace babu wari a jikinta babu ƙarni ko zarni bare kuma hayaniyar “ya “ya , yayin da zaka kwanta da matarka lokacin zata fara cewa batayi ma yara shimfiɗa ba , kana mata magana tana wani fiffizge kai tun kana sha’awar abun har yazo ya fita akanka ,

      Kallon Alaji nayi sosai sannan nace , filawar bisa hanya tasha banban data cikin gida , mace kamar filawa take idan ta samu wuri mai kyau kuma akayi mata ban ruwa yanda ya kamata idan dai tasha ruwa ta ƙoshi duk wanda ya gani sai ta bashi sha’awa , lokacin da filawa ta rasa ruwa zata bushe ta soye duk wadda ya kalleta baya sha’awar ƙara kallonta , to haka mace take , matan bariki wayau suke muku kuna basu kuɗi suna gyara jikinsu a cikin kuɗin da kuka basu a ciki suke siyan abunda zasu ja muku hankali dashi , matarku ta sunna tana can viseline in da zata shafa wahala yake mata , taya zata gyara bare har ta baka sha’awa ? Idan baza ka damu ba zanyi magana da matarka idan Allah ya kaimu idan har tabi shawarata tabbas zaku samu rabauta , kai kuma zan koya maka yadda akewa mace ban ruwa ….

        Shiru Alaji yayi zuwa wani lokaci yace babu damuwa kije na yaddar miki , godiya nayi masa sannan na miƙe ɗauko kujerar sukayi suka biyoni da ita yayin dana tsaya wurin wata motar…

     Ajiye min kujera akayi na zauna , motar a buɗe take dan haka na ɗora ƙafata ta haggu a saitin mazauni driver tare da cewa malam barka da dare ! Allah ya taimaki uwar ɗakinmu ya haƙuri damu ? Alhamdulillah na faɗa tare da cewa ya iyali ? Kamar jira yake yace tana can shegiyar saida nayi mata jakin duka na fito , kallon agogon hannuna nayi ba tare dana kalleshi ba nace me tayi maka ne ? Ta rainani idan na shigo da leda takemin sannu da zuwa idan banzo da itaba ko daga ɗaki bata fitowa , yau na yanka rago dake duk sati nake yankawa , mahaifiyata tazo nace a ibar mata shine tayi mata rashin kunya ni banji daɗin abunba shi yasa nayi mata duka na baro gida , 

Kallonshi nayi sannan nace to me kazo kayi nan ? Dariya yayi irin ta sakarkari sannan yace nazo a ban natsuwa , jinjina kai nayi sannan nace tou yau babu maganar bariki kaje gida ka lallashi matarka muna zuwa gidan idan Allah ya kaimu , ina faɗin haka na miƙe nayi gaba , ɗauko kujerar sukayi suka biyoni domin cikin gida na nufa…

      Hayani mazan suka farayi tare da cewa ya zanyi musu haka ne ? Ai haka ma babu adalci , a zuciyata nace wannan matsalarku ne ba nawa ba ,

      Ina shiga gida na shige ɗakina , Amisty ta rufomin baya , itace ta kulle ɗakin domin dare yayi kowa a gajiye yake babu abinda yake buƙata sai bacci , kayan jikina na cire na ɗaura zanin bacci , Amisty kuwa da kayanta tayi kwanciyarta ,

      Tunda na kwanta fuskar Dikko kezomin a idanuwana , ya ƙara kyau abu ga farar fata ga hutu ga gayu gemunshi yasha gyara sai kyalli yakeyi , an gyara ƙasimbar ta kwanta sosai dake farine sai abun ya bada wani irin sirrintaccen burgewa , shi ba wani tsoho ba amma dole sai ya zama tsoho me yasa yakeyin haka ne ? Dan yaga gemun yana mishi kyau gaskiya fa yayi mishi kyau shi yasa yake ɗaukar hankalin mata , gemu da ƙasimba make up in maza kenan…

       Ajiyar zuciya na sauke tare da gyara kwanciyata , damuwa nakeji sosai ina ta ƙoƙarin molaƙe rayuwata ashe shi Dikko yana can yana ƙoƙarin gyara tashi , zaiyi aure ya barni ina cikin karuwanci , ina ganin zan masa rata ashe shine zaimin rata , ya zama shugaban al’umma ta wani gefen ni kuma na zama shugabar rusa rayuwar farin cikin wasu da tawa rayuwar ? Hawaye ya cikamin ido bayan sun gangaro na maida numfashi dakel sannan naci gaba da zancen zuci ! Me yasa na zaɓi na zama karuwa ? Me yasa banyi ƙoƙarin zama ta gari ba ? Mai makon na zama waraka ga al’umma sai na zama cuta a garesu…

    Kukan zuci naci gaba dayi irin mai kartar zuciyar nan wanda kesa mutum yaji kamar zai mutu shi naci gaba da yi numfashi na naji yana ƙoƙarin fita daga jikina dolena na tashi zaune da sauri naci gaba da fita dan ceto tawa rayuwar….

       Zaune yake ya hakince irin zaman nan da yakeyi na ya raina mutane , ɗage yake kallon kowa yayin da bakinshi ke motsawa a hankali cikin kwarewa da goguwar iya cin cingom , Al ‘ Ameen ya kalla sannan ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunshi yace wai mema zance mata idan tazo ? Murmushi Al ‘ Ameen yayi tare da shafa kanshi yace tuba nake ranka ya daɗe , dan tunda akayiwa Dikko kyautar Sadiyya bai taɓa zuwa ba sai yau , baya ko waya da ita yauma Dadynshi ne ya matsa mishi shi yasa yazo !

      Dan ko hotunansu dake yawo a social media haɗawa akayi bashine da ita suka jera suka ɗauka ba , Dikko baiyi magana wa Al ‘ Ameen ba Sadiyya ta shigo cikin palon , gaisheta Al ‘ Ameen yayi sannan ya fita…

      Cikin karairaya da kwarewa da bariki tayo inda Dikko yake zaune , ɗan taɓe baki yayi a zuciyarshi yace bari inga rashin kunyarki , bai gama tunani ba ta zauna tare da ɗora kanta a saman kafaɗarshi tana mai sauki ajiyar zuciya cikin yanayin mai nuni da tana cikin shauƙi, daga waje har ciki Dikko baiji wani shock ba , dan haka yace sauke kanki mace bata hawana , na miki uziri nayau idan kika sake zaki samu matsala….

    A shagwaɓe tace haba diye { dear } … Yanayinka sch ne amma ya kake abu kamar class ? Banza Dikko yayi baice komai ba , jinyayi shiru yasa tace ya hanya da mutane ne ko ? Nan ma bai bata ansa ba , zagba surutu taci gaba dayi tare da cewa idan sukayi aure zata mishi soyayya , ba komai kake ta wani jan allo dana fara rubutuna zaka sauke , hauka dai tayi ta zuba mishi tare da son ƙara kwanciya jikin Dikko amma abun ya mata girma ,

       Bayan ta gaji da surutun tayi shiru , can kuma taci gaba , kasha drinks mana , ta ci gaba da lissafo duk abinda aka kawoma mashi , har ta gaji ta sake ɗaukewa , ganin Dikko bazaiyi magana ba yasa ta fashe da kuka cikin kuka take cewa haba Yaya wai me yasa baka so na ne ? Ina ta magana amma kamin shiru ka mayar dani kamar wata mahaukaciya ! Nifa “yar uwarkace ka soni dan Allah kodan zumunchin dake tsakaninmu….

      Kallonta yayi sannan yace ya isa , kije ki kwanta a gajiye nake muyi magana anjima , goge hawayenta tayi tare da cewa ai ko na kiraka ma baka ɗauka , karki damu zan ɗauka insha Allah , murmushi tayi tare da miƙewa cikin farin ciki , shima murmushin yayi zuciyarshi tace dama An matane a wannan yanayi , wata “yar jakace a gefenshi ya nuna mata yace ɗauka…

       Ɗauka tayi babu ko godiya ta fice a palon , wayarshi ya ɗauka ya nuno hoton Sultana , ya ɗauki tsawon lokaci yana kallonshi bayan wani lokaci yayi magana a bayyane cewa kuka kikayi , ina gane yanayin farin ciki da damuwa idan na kalli hotonki , duk yanayin da naji na shiga tou kin shiga yanayin meke damunki ne ….?

      Banda ajiyar zuciya babu abinda nake saukewa har yanzu zaune nake ban kwanta , ɗan ɓata rai Dikko yayi a daidai wannan lokacin ya kalli hoton Sultana sannan yace ki daina damuwa ki zama mai farin ciki a ko wane lokaci , taɓa screen in wayarshi yayi tare da cewa kiyi bacci cikin aminci da salama ….

     Ajiyar zuciya na sauke tare da komawa na kwanta , ban daɗe da kwanciya ba bacci ya ɗaukeni , …..

      Koda Dikko ya koma masauki wanka ya farayi duk saida ya gama abinda yakeyi sannan ya cire wayarshi daga airplane mode , kamar wani munafiki wai ba’a kunna waya sai dare sosai zai duba saƙon da aka turo masa , a lokacin zai shiga yanar gizo , a lokacin zai ansa waya idan aka korashi itama sai wacce yakeji zai iya ɗauka , da zaran kuma ya gama abinda yake zai sake rufewa sai kuma wani daren , wayarshi ɗaya kuma da ake samunshi ba kowa yake da number ba , daga gidansu saida wanda shine yaga dama ya bashi , dan dayaji an kirashi da wayar to yasan kirane mai mahimfaci ,

          Wani vidio ya buɗe da abokinshi ya turo mishi , kafin vidion ya buɗe ya fara karanta rubutun ƙasan vidio da akayi , 

     Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un , Allah yayiwa Fatima rasuwa sakamakon fyaɗe da akayi mata , abun babu kyan gani kuma ko su waye da gayya sukayi mata sun wulaƙanta yarinya bataji bata gani ba , sannan suka ɗauki vidio a waya suka bada wayar a cikin envilop aka kaiwa Babana har Office dan lokacin kwananta ɗaya da yini ba’a ganta ba , gawar kuma suka zo suka jefar a ƙofar gida…

       La’ilaha illa anta sub’hanaka inne kuntu minaz zalimeen Dikko ya furta a lokacin daya gama karanta saƙon ya fara kallon vidion , ƙattin maza ne sunkai su biyar amma duk sun rufe fuskarsu da maX , ihu Fatin keyi amma babu abinda ya damesu kowa burinshi ya biya tashi buƙatar , wani irin motsi Dikko yaji kwalwarshi tayi kanshi ya yamitsa da sauri ya ajiye wayar tare da dafe kanshi da dukan hannuwanshi biyu abinda yakeji da game da Sultana ya dawo mishi sabo….

      Lahaula wala kquwwata illa billahil ‘ aliyyil azeem , Dikko yake ta maimaitawa ya ƙurawa kafet ido kamar Sultana ce a wurin , saida natsuwa tazo mishi yaci gaba da zancen zuci lallai ya cuci rayuwar Sultana shima bashi da banbanci da mutane biyar ɗin nan domin magungunan daya sha sun bashi wani irin ƙarfi wanda ko allura hauka akayi ma doki iyakar abinda zaiyi kenan dan nuna shi mai ƙarfi ne , hawaye ya cikawa Dikko ido tausayin Sultana ya ƙara kamashi lallai ya cuci yarinyar nan !

Yau wane irin baƙin ciki iyayen Fatima suka shiga ? Wane irin ɗaci sukeji idan sukaga wannan hoto ? Ya Abbakar zaiji yayin daya ga wannan hoton akan ƙanwarshi ? Da nine ya zanji idan haka ta kasance akan ahalina ? Kwantar da kanshi yayi a saman hannun kujara ya rufe idanuwanshi duk yanda akayi akwai abinda Baban Abbakar yayi suka ɗauka fansa dan yanayinsu ya nuna a lokacin da suke aikatawa kamar biyan bashi ne sukeyi , Allah na tuba ka gafartamin ka sakawa An mata soyayya ta mai girma a zuciyarta , sona ya hanata bacci da tunanin kowa a duniya saini , ta daina jin maganar kowa sai tawa , ka saka mata san kasancewa dani inuwa ɗaya kasa mata firgici idan ta yini ko ta kwana bata ganni ba , ka ɓadda mata tunanin kowa da komai na duniya saini , ka saka mata san jin muryata ka goge mata kuɗirin fansa akaina , nayi alƙawari zan zamar mata natsuwa zan zama uwa da uba data rasa masu kishinta bazan barta tayi kuka ba haka kuma zanyi ƙoƙarin sakata farin ciki , duk wanda ya ɓata mata ko yasa taji damuwa nine zan tsaya harsai naga tayi farin ciki , Allah ka gafar tamin ka goge damuwata a zuciyar an mata ta zama soyayya mai ban al’ajabi ga kowa , 

      Buɗe idanuwanshi yayi tare da goge hawayenshi , sannan ya ɗauki wayar ya goge vidio ba tare daya gama gani ba , wayar Abbakar ya fara kira dan jajanta mishi kafin yaje mishi ta’aziyya , Sadiyya koda ta kira Dikko text ya tura mata idan ya gama zai kira , koda ya gama abinda yake ba wulaƙanci ba da gaske ya manta da labarin kiran Sadiyya , da tunanin An mata yayi bacci….

      Da safe wanka nayi na shirya cikin riga da zani na atamfa , hijabi na saka sannan nacewa Amisty zanje in dawo ! Ina zakije tunda safe haka ? Ta tambayeni ! Takalmi na saka tare da ce mata zanga wani a bakin hanya , addu’ar a dawo lafiya tamin ni kuma na fice daga ɗakin…

A ƙofar gida na anshi makullin mota na dana sa aka ɗaukomin , ɗan daba ɗaya na dawo dan ya rakani gidan Alaji koda an samu ɓacin rana , abinda yasa ban tafi dasu Amisty ba saboda kar ya zama naje gyara kuma gyaran ya zama ɓarna…..

     Tafiya mai nisa mukayi zuwa gidan Alaji , a ƙofar gida nayi parking sannan na fara kiran wayarshi dan dama banzo ba saida izininshi………

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button