???? —— 3 Saida na gama kallesu daya bayan daya sannan nayi murmushin takaici da gefen bakina, kallon inda gawar “yar madara take na kalla wani makoko yazo ya tsamin a makoshi wanda ko yawun zan hadiye sai naji kamar lumfashi na zai dauke. Dikko………………….! Saida na jinjina sunan a zuciyata da kuma bakina, sannan na kalli dandazon taron ahalin gidanmu, nu na su nayi da dan yatsa manuni, sannan na dafa daidai kirjina da
hannun haggu na , zanyi magana sai kuma maganar ta kasa fitowa dan bana iya magana a cikin yanayin bacin rai.. Wuri na samu na zauna ina ta sauke ajiyar zuciya, tsinuwa da zagi da Allah ya isa bansan iyakar adadin dozinan da suka saukemin ba, zagin ne dai kawai amma nasan bazan daku ba, Har yanzu babu wanda nayi ma magana kuma babu wanda na sake kallo, zama nayi na sauke kaina kasa, yayin da wasu suka gaji da tsayuwa suka durkusa wasu kuma suka bazama neman gida, dan su zasu nemo shi dan ko sun tsaya jiran Baba ko yazo bazaiyi wani abu ba, Bayan sun zauna ne sukaci gaba da tattauna maganar abinda Dikko yayi, ashe tun waccan ranar zagin da nayi masa ranar da zamu tafi makaranta tare da Babana bayan an bashi hakuri ashe baiyi hakuri ba. Da zai jira har na dawo daga makaranta ya takeni da mota ya wuce abinshi, tou bayan ya fito daga gidan da yake kiwon dokuna yaga Babana ya fito daga gidanmu, Shi Dikko mugune na gaskiya da gaskiya, duk duniya babu abinda ya raina yake kyankyami irin talaka, Dikko baya dariya haka kuma baya murmushi kullum fuskar nan tashi a hade take kamar hadarin tsakar dare, Bakya ganin dariyar shi kwata kwata, idan kuwa har Dikko yayi murmushi tou tabbas yaga cuta, idan kuma yayi dariya tou tabbas ku idan kuka ga abun sai kunyi kuka saboda tsabar tausayi.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());
Danshi sai yaga mugunta yake dariya….. Bayan Babana ya wuce, Dikko ya kalli gidan ya sake masa kallo babu abinda baya gani na gidan daga nan waje inda yake tsaye, Kallon rainin hankali yayi ma gidan tare da bata fuska ya juyar da kai ya kalli daya daga cikin wanda suka zo tare sannan ya kalli agogon hannushi yace waye shi…. Ya nuna Babana da gidanmu… Bai tsaya yin magana ba ya bazama cikin anguwa, a cikin kankanin lokaci yaje ya samowa Dikko duk wasu bayanai daya kamata akanmu da rayuwarmu, Jinjina kai Dikko yayi bayan yaji komai tare da cewa karta mutu, amma barsu na jikatasu zata gane Dikko ba sa’ar ubanta bane daga wannan rana tsoron Dikko zai shiga zuciyarta maza a nemo min mai gidan daya basu hayar gidan, dan gajeren tsoki yayi tare da cewa talaka banza a banza, za’a nuna mata su kudi jigo ne masu nuna ishashshen iko. Daga wannan rana zata gane mai kudi ba’ayi masa hawan kasa, Cikin anguwa ya sake komawa dan binciken mai gidan da muke haya, aka fada musu anguwar da yake zama, da kuma wurin da yake zama dan kasuwancin shi, Bayan sun gama daukar duk bayanin da suke bukata, sukayi tafiyarsu, ashe Dikko gidan da muke haya yaje ya siya, kuma mai gidan da muke haya yace wa Dikko Babana baya biyan kudin haya tuni yayi niyar tashinmu sai wata yayata take biyanshi kudin haya daga cikin kaddarar rayuwarta, Tun wannan ranar Dikko ya biya kudin gidanmu, bayan ya biya tafiya ta kamashi, saida yayi wata biyu baya nan, shine fa yana dawowa babu notice kawai yasa aka rushe gidan…… Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama jin duk bayanan su, yanzu ita Zainab zuwa takeyi anayin iskanci da ita kenan ? Amma ta bata wayanta, Yawwa an samo gida ku taso mu tafi, gaba daya sowar farin ciki suka dauka tare da mikewa suna cewa a ina gidan yake ? Gidan Alhaji Sabo ne yace mu zauna dan yaji abinda ya faru damu kuma ya tausaya mana sosai, amma duk watan duniya yace zamu rika biyan dubu goma, Eh hakan yayi babu wani damuwa, ku tashi mu tafi, yeay yara da manya sukayi ta shewa muka tafi dukanmu yayin da wasu ke cewa dan uwar Dikko yazo ya anshi wannan idan ya isa. Haka muka koma gidan Alhaji Sabo dake makotan gidanmu da Dikko ya siya, bamu da komai haka muka shiga gidan, kowa daga ita sai kayan jikinta, Nidai har yanzu banyi magana ba, abun duniya duk ya dameni kuma babu wanda yabi ta kaina ko Inna bata sake shiga sabgata ba sunyi ayari wuri daya ana ta shawarar yanda za’ayi a samo kudin Alhaji a bashi dan ya basu daga yau zuwa jibi su kawo mishi kudin shi. Har safiya basu samu mafita ba, haka kuma Babana bai kwana gida ba, bansan yanda akayi ba suka shiga suka fita suka bawa Alhaji kudin hayarshi ba, Kwanan mu hudu a sabon gida Baba yazo gidan, bai tambayi yanda akayi muka dawo ba haka kuma baibi takan kowa ba zance ya akayi aka biya kudin haya ba, haka kuma baiyi ma kowa magana ba saini daya, Uwar masu gida lafiyar ki qalau kuwa ? Lafiya qalau Baba na amsa masa, yace kwana biyu bakije makaranta ba har kawarki ta tambayeni ko lafiya ? Nace mata lafiya qalau gaskiya, kinsan nima bana nan naje Abuja, Allah sarki na fada, tou miya hanaki zuwa makaranta ne ? Ya sake tambaya na, saida na tattara bakina sannan nace Baba ai an rusa gidan, komai namu kuma an tattarashi an kwashe anje an zubar, banda kayan makaranta da littafai, Wayyo Allah Mamana, taso muje waje muyi magana, mikewa nayi nabi bayanshi, yana gaba ina binshi har muka fita kofar gida, Wuri muka samu muka zauna, muna zama Babana yace in fada masa dame dame nake bukata ? Nace masa ko kayan sakawa dukanmu gidan bamu da, kowa kala daya yake dashi, amma makota sun dan tattara mana kaya, murmushi yayi tare da cewa wallahi Uwar masu gida bata saka kwancen kaya, na dawo garin nan jiya da kudi fiye da tunaninki Mamana, Tunda naji abinda ya faru tsakanin shadda da yadi da boyal saida na siya kusan kala arba’in, takalmi da agoguna da hulana duk babu abinda ban siya ba, kayan suna can na kai dinki, Tsare Babana nayi da ido, a zuciyata kuma ina ganin rashin adalci irin na Baba, amma Baba bakada imani iyalinka na nan suna neman abinda zasuci karma ayi maganar wurin zama amma kai har lokacin siyan kaya kake yi Baba……? Duk a zuciyata nake wannan tunanin. Mamana, ya kira suna na, kallonshi nayi ba tare dana ansa ba, tunanin me kikeyi ? Bayan gani a duniya ! Idan har ina nan a raye baki da matsala nayi miki alkawari zan kula dake zan kange miki duk wani bakin ciki da damuwa, idan dan maganar kayan makaranta ne da littafai zan siyo miki komai ma ki daina damuwa, zan miki duk abinda kike so dan kiyi farin ciki Mamana , wallahi da ina da iko ko kuda da sauro da ban barsu sunzo wurinki ba, haka nake alfahari da aihuwarki farar mace lantarkin ciki gida, da nasan zan haifeki wallahi da ban tara wannan yame yamen “ya “yan ba, A ranar da aka aifeki a ranar naci makudan kudade a wurin wasan caca , tun daga ranar na gane ke mai sa’a ce, wannan dalilin yasa nasa miki sunan mahaifiyata ya karasa maganar yana murmushi, sannan yaci gaba da cewa zuwanki yasa talauci ya guji rayuwata, shi yasa na tattara miki buri da yawa domin nasan kedin mai arziki ce. Yana fadar haka yace tashi muje, tashi nayi nabishi, yauma cikin wata zakanyar mota muka shiga, ta gaji da haduwa sai sanyin A C ke tashi ga kamshi mai dadin shaka, Babana fa dan gayu ne gashi da wayewa kuma yana da kalar burgewa amma babu halin kirki. A daren nan saida Babana ya tabbatar duk abinda zan bukata ya siyamin, sannan muka wuce wurin dinki, tela ya aunani Baba ya biya kudi muka dawo gida, Tunda muka dawo matarshi Mariya ta tada hankali ta fara zagina tare da aibatani, bata san Babana yana tare dani ba da batamin ba, yana shigowa cikin gida yace mata ta tafi ya saketa, maimakon Mariya tayi farin cikin sakin kawai sai ta kama kuka, dani Babana ke aure ya sakeni wallahi sai nayi farin ciki sosai na rabu da rayuwar wahala, Amma Mariya saita durkushe tana bashi hakuri, wallahi ko sauraren ta baiyi ba, anyi an gama domin Babana idan ya saki mace ya gama da ita har abadan duniya baya maimaita mace idan har ya riga ya rabu da ita, dan yace ko sitira sawa daya yake mata mace kadai yake ma maimaici a rayuwar shi, shi yasa idan har ya saki yake mantawa da babinta a rayuwarshi. Fita yayi yabar gidan, Mariya kuwa kuka takeyi kamar zata mutu, wallahi ta bani tausayi sosai dandai ba hurumi na bane dana bashi hakuri kuma tabbas nasan zai hakura amma ba ruwana tunda ba hurumi na bane, kuma nasan tsakanin gobe da jibi tabbas saiya karo aure……. Zaune muke lafiya a gidanmu, rayuwar dai tana nan kamar kullum kowa shi yake cida kanshi, gaba gaba dai yayuna sun fara harkar barikancin su har a cikin anguwa, saboda Baba baya tsawa tawa dan yaga dama ma ya kwana biyar ko sati baya gida, Bayan sakin Mariya da sati daya Baba ya auro wata “yar fiririyar yarinya wacce zata tsaya iyakar sa’ata, kankanuwar yarinya itama mai zubin karuwai, wankan tarwada ce kallo daya zakayi mata kasan ta gaji da fekewa da bari… Idan kayi mata magana saita wani yamutsa fuska sannan zata daga idonta dakel tayi maka magana, kai nidai sam tsarinta bai burgeni ba haka kuma bata wani shiga raina ba, dan bata da kunya ko ta misali, caccakakkar “yar iska ce , tasha iskanci ta koshi, amma anyaBaba auro yarinyar nan yayi kuwa ? Rayuwata nakeyi cikin farin ciki, bani da wata damuwa shi yasa bana gane abinda kowa yake ciki a gidanmu, idan na fito daga dakinmu sai dare nake komawa saboda Innata bata san gani na, dan kishiyoyi sun tisota a gaba da habaici saboda ni, Babana yana kula dani sosai baya barina shiga damuwa, ina zuwa makarantar boko da islamiya , amma boko gugar kaya kawai nake inje, islamiya kadai nake da fahimta. Tafiye nake a cikin nikaf ina, sauri kawai nake na isa gida saboda hadarin daya taso, sai wani irin iska akeyi mai hade da kasa, walkiya da cidar hadari duk sun karade sararin samani, tunda na biyo santar nan banci karo da kowa ba har na iso inda nake tunanin nan ne gidanmu, Kamar yanda nayi hasashe haka na yanki hanya domin shiga gida dan bana ganin gabana saboda kasar data shigar min ido, na daga kafata in taka sumintin kofar gidan naji wayam, kara mika kafata nayi dan a tunani na ban tako daidai ba, kamar yanda naji daga farko yanzu ma haka naji, Da sauri na bude idona dan inga lafiya ? Filin wurin kawai na gani kamar ba’a taba gini a wurin ba, salati nayi na sanar da ubangijina to ina “yan gidanmu suka tafi ? Makota na shiga na tambayi inda “yan gidanmu suke, aka cemin Alhaji Sabo ya canza mana gida kafin wata ya kare mu tashi, tambayar dalilin tashin da rusa gidan da akayi nayi amsar da aka bani itace, Dikko ne ya siyi gidan amma wannan karon anyi ma kowa uziri ya fita da kayanshi. Bance komai ba saidai na sake tambayarta ina gidan yake ? Kwatanci tamin gida na like da gidan da aka rushe nan muka koma, ban sake cewa uffan ba na nufi gidan. Daki daya ne tak a gidan saboda haka kowa yana zaune cikin barandar dake tsakar gidan, sallama nayi amma babu wanda ya ansa min sallamar har Innarmu, nima ban sake sallamar ba na samu wuri na zauna tare da jan bakina na kameshi, Dukanmu a tsakar gida muka kwana yayin da wasu suka kwana a zaure, babban gida ne sosai amma daki daya ne ya gina shima ajiye ajiye yake a cikinsa, gari na wayewa na shirya na tafi makarantar boko, Baba bayanan sun tafi gasar caca, dan bai fadawa kowa sunan garin daya tafi ba, ni kadai yayiwa bankwana. A makaranta Amisty ta lura ina cikin damuwa, dan haka ta tambayeni abinda ya dameni, ban fada mata ba, saidai nace mata da Allah waye Dikko a garin nan ? Hmm su Amisty idon duniya saida tayi masa wani irin kirari sannan tace miya hadaki dashi ne ? Nace mata kawai dai labarinsa nakeji shi yasa nake san sanin koshi din waye. Abinda Amisty tacemin shine, yanda kike takama Babanki yana masifar sanki da kaunarki dan dole wannan misalin da kanki zanyi shi idan ba haka nayi miki ba tou fa lallai nasan baza ki gane ba, Dikko d’a daya tak a wurin mahaifin shi, yana da yayu mata sosai saboda suna da yawa gidansu suma, amma basu kai gidanku yawa ba, abinda yasa kuwa aka tara yawa a gidansu saboda san haihuwar d’a namiji da basu samu ba, Akan Dikko ya samu namiji daga shi kuma har zuwa yau din nan ba’a sake haihuwar namiji ba, Dikko gaskiya yana da kirki kuma shi ba dan iska bane amma gaskiya baya san raini, Yana da alkairi sosai amma shi baya dariya haka kuma baya murmushi, ni bayan wannan bansan komai ba haka dai kawai naji ana fada a gari, Gyara zama nayi tare da tambayarta shi kuma waye ubanshi ? Murmushi Amisty tayi sannan tace da Allah karki dauki ne wake da shinkafa mana, Dikkon ne a katsina baki san waye ubanshi ba ? Wallahi ban sani ba, na bata amsa, tashi tayi ta barni a wurin dan ita a tunanin na sani jan zance ne. Har muka tashi makaranta Amisty bata fadamin ko waye uban Dikko ba, ni kuma ana tashi makaranta ban tsaya komai ba na nufi gida tunda nasan Babana baya nan, Tunda napep ta ijiyeni, na hango kofar gidanmu daddabe da mutane, Dikko yana zaune a saman gaban mota ya kwantar da bayanshi saman gilas din motar kafarshi daya saman daya, ya tallabo kanshi da hannayen shi, kamar kullum yauma cingom yake ci, kananan kayane jikinshi ya dode da gilashi mai saukin duhu. “Yan gidanmu sun daddabe shi suna bashi hakuri amma ko inda suke bai kalla ba bare su sa a ransu zaiyi magana, sai waso mana kaya akeyi daga cikin gida, yayin da “yan zaginshi ke cewa ai tunda har kuka tabo mai gida a garin nan sai kun rasa gidan zama, wannan dinma ya siyeshi idan kunyi zuciya ku gina naku talakawan banza kuna jayayya da masu katsinar gaba daya, Inda jakar islamiyata take naje na duka na dauka, na koma gefe nayi tsayuwata tunda ko nayi magana babu wanda zaimin magana kowa haushi nake bashi, Wani dattijo ne shima makoci ne , yace ni inje in bawa Dikko hakuri duk saboda abinda nayi masa yake ta wannan saye sayen gidanje, dan gajeren murmushi nayi tare da cewa Baba kenan aini wancan dan iska nafi karfinshi wallahi baikai matsayin da zan kalleshi ba bare har na bawa banza hakuri, idan kuma har ka tilasta naje to lallai ina zuwa zan jawo dan iska ya fado kasa, Lallashi na dattijon nan ya farayi akan lallai sai naje na bawa Dikko hakuri, a lokacin har an gama fito da komai namu an fara rushe gidan.
(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());