NOVELSUncategorized

KWARATA 38

???? —— 38

        Ƙuramin idanuwa yayi yana kallona ta cikin madubin gaban mota , sai kuka nake ina fyace majina da gefen hijabina , tissue ya wurgomin bai juyo ba kuma bai kalleni ba yace zaki ma mutane shiru haka nan ko kuma dai…. ?


      Harararshi nayi cikin muryar kuka nace mara zuciya ko mutum baya harkar ka sai ka shiga nashi mutum ba dangin uwa ba na uba kawai ka shigomin rayuwa ,  kyakyawan murmushi yayi da gefen bakinshi amma baiyi magana ba , kallonshi Al ‘ Ameen yayi bakinshi ɗauke da magana , murmushi Dikko yayi tare da cewa manta da labarinta ka ƙaddara ma bama nan bare kayi tunanin munji abinda tace , makaranta dai zuwa babu fashi !

      Shiru sukayi su dukansu babu wanda ya sake magana , saidai shi Dikko yana kallona ta cikin madubi idan akayi sa’a muka haɗa ido sai yayi murmushi mai tattare da mugunta , matsawa nayi daga saitinshi dan ya daina kallona , ƙara gyara saitin madubin yayi yaci gaba da kallona , kwanciya nayi na lulluɓe da hijabi naci gaba da baccin dole…

      Har nayi bacci na farka bamu isa ba , kuma tafiya Al ‘ Ameen yake bata wasa ba dan shima kusan irin tuƙin Dikko yakeyi kamar basa san rayuwarsu , ganin har yanzu a hanya muke yasa na sake komawa na kwanta ina mai ci gaba da kuka , jin kukana yasa Dikko juyowa tare da cewa ke miƙomin kunun nan tunda baza kisha ba ,

     Cikin kuka nace ina sha , Al ‘ Ameen yasa ya faka a gefen titi da kanshi ya fita ya ɗauko ruwa a but sannan yazo ya buɗe inda nake ya bani ruwan , yana nufi in kuskure baki na , fita nayi na kuskure bakina na wanke fuskata na koma mota na zauna ,

Ɗan ƙaramin flaks ne na sulba mai kyau cike da kunun gyaɗa tun kafin in fara sha Al ‘ Ameen ya tada mota ya hau titi yadda ta kamata yaci gaba da gudu , cike da baƙin ciki nake shan kunun , yayi min daɗi sosai ɗan kaɗan na rage na miƙawa Dikko flarks in dan ya ajiye , ansa yayi ya shanye sauran dana rage, a raina kuma tunani nake Dikko ko ƙyamata bayayi yanda yake ɗan gayu mai aji har zansha abu in rage yasha saura na ,

      Har muka isa bakin get in makaranta babu wanda ya sake magana , a bakin get Al ‘ Ameen yayi parking , muna zaune a mota ga dukkan alamu akwai wanda ake jira , bamu wane daɗe ba , wata irin shareriyar mota tayi parking kusa da tamu , wani matashi ne ya fito daga motar yayo wurin motarmu , Al ‘ Ameen ya sauke gilashin kusa da Dikko , yana isowa Dikko ya miƙa mishi hannu suka kashe ,

     Sai kuma aka shiga gaisawa bayan sun gaisa yace ina An matan take ne ? Murmushi Dikko yayi yace gata can baya kuka takeyi , dariya matashin yayi tare da cewa tun daga katsina har bakori tana kuka ? Dikko yace ai bata da aikin yi , dariya matashin ya sakeyi tare da cewa sannu dai za’ayi mata , 

      Ba tare da Dikko ya juyo ba yace An mata dani dake waye ya kamata ayi ma sannu ? Banza nayi dashi ban bashi amsa ba , dariya yayi tare da cewa muje sauri nakeyi yayi maganar yana kallon agogon hannunshi , komawa matashin yayi cikin motarshi ya tada , mu mukayi gaba shi kuma yana bayanmu har muka isa bakin ofishin principal , a bakin ofishin mukayi fakin sannan muka fita gaba ɗayanmu muka nufi cikin office in…

    Bayan gaisuwa akaci gaba da abinda za,ayi duk wani abinda ya kamata ayi anyi , kuma Dikko yace wa principal ko hutu akayi idan bashi yazo ba kar wani ya ɗaukeni , ya ƙara da cewa ko wannan ya nuna Al ‘ Ameen yace koshi yazo a , a, niɗin dai , tace insha Allah , saboda Dikko ya ɗaukeni ƙarshen kidahuma JS 1 yasa aka ajiyeni , inajin aji ɗaya na ƙara fashe wa da kuka duk da dama kukan nakeyi tun safe har yanzu , 

      Bayan an gama aka ciro kayana daga bayan motar Dikko , a bayan motar abokinshi aka fiddomin katifa , bayan an gama sauke kaya Dikko ya bulale Prcp da kuɗi wanda Al ‘ Ameen ya miƙa mata su ,  tayi ta zabga godiya Dikko yace tasa min ido sosai a riƙa zaneni idan nayi abinda bai kamata ba , tace insha Allah !

      Ina tsugunne a gefe sai kuka nakeyi , bayan sun gama abinda suke Dikko ya kallo inda nake yace taso ki biyoni , jiki a lalace nabi bayan shi har cikin mota , dukanmu a baya muka zauna , da yanayin tausayi a fuskarshi yace idan kina san wani abu ki faɗawa principal zatamin waya kinji ko ? Nace to , karkiyi rashin ji kiyi karatu kuma ki zama mai haƙuri karki sake ki biyewa abokan banza kinji ko ? Saida na goge hawaye sannan nace tou ,

      Shiru yayi zuwa wani lokaci yace tou kalloni kiga , ba musu na ɗaga idona na kalleshi , murmushin shi mai burgewa yayi tare da cewa idan kuma kikayi , uhum ? Ya nuna idanuwanshi da hannunshi , bansan abinda hakan da yayi yake nufi ba , banyi magana ba ina kallonshi dai , yace to nan ? Ya nuna , girgiza kaina nayi alamar a , a tou zakiyi tunani na ko ? Da kai na bashi ansa Eh , tou idan dai kin tunoni kar kiyi kuka kinji An mata zan riƙa zuwa da wuri ina ganinki ai zaki ji daɗi idan kika ganni ko ? Nace Eh , 

      Bandir in “yan 1k ya bani guda biyu yana cewa karki yi damuwa sosai kiyi farin ciki kullum don Allah kar kiyi kuka da yawa inaji a jikina idan kina cikin damuwa kinji ko ? Jinjina kaina nayi alamar gamsuwa , godiya yayi tare da cewa tou kya iya tafiya , godiya nayi sannan na fita daga motar , ina fita Al ‘ Ameen ya shiga yaja suka tafi abokinshi yabi bayan su shima cikin motarshi…

      Aji Principal tasa aka rakani tare da cemin idan an tashi makaranta inzo da “yan ajinmu su tayani ɗaukar kayana , nace tou , kamar wata geliya haka nake ji na , na koma kamar wata sakara , haka na zauna ina bin “yan ajin da kallo , kowa sabgar gabanshi yakeyi babu wani da ya damu da wani ,

     Koda aka tashi ban nemi kowa ya tayani ɗaukar kaya ba na koma ofishin principal , tou Dikko dai ya nemomin mutunci na tunda yayi mata wanka da kuɗi mutane basa abu dan Allah sai dan hatimin nasara , da kanta ta samu yara suka tayani ɗaukar kayana har zuwa ɗakinmu…

      Bayan munje mun ajiye kayan na samu wuri na zauna ina kallon yanda kowa yake rayuwarshi domin ina so na fahimci yanda rayuwar makarantar take tafiya !

    Tunda Baba ya sulale ƙasa ya tsaya cak ya daina aiki , yana da rai amma dashi da matacce basu da banbanci ɗagowar da cikin shi keyi kawai zaka gani ka tabbatar da ranshi , wannnan abu yayi ƙololuwar ɗagawa kowa hankali dan haka aka kwashe shi akayi asibiti dashi…

     A ɓangaren Sadiyya kuma tanajin jiki sosai dan haka iyayenta suka buƙaci ta koma gida suyi jinyarta , amma daga inda Dikko yake ya murje idonshi tas yace idan dai shine yake aurenta a barta kar wanda ya tafar mishi da mata ko yace ya kasa kula da itane ? Dole suka haƙura suka barta ,

      Amisty kuwa da Hafsa lingu da saƙo sun nemi Sultana basu samu ba , kuma wayarta ma idan sun kira a kashe take dan tuni Dikko ya ƙarya layin , kuma sunje wurin Alaji sun tambayeshi ko yana da labarin Sultana yace shima kanshi nemanta yakeyi , yaje gidansu ance an saceta wurin partyn birthday inta Babanta ma yana asibiti baida lafiya , bawan Allah Alaji shine ke kula da Baba duk wani aune ² da magunguna shine yake biya…

     Sati na ɗaya a makaranta banda damuwar komai kuma banda wani tunani daya dameni sai Babana da nakejin kewarshi kullum rana , bana tunanin Inna kwata² dan na tabbata itama duk inda take bana rayuwarta kuma bata tunani na amma nasan duk inda Babana yake yana can yanajin damuwa na rashina a kusa dashi !

     Har yanzu banyi abokiya ko ɗaya ba kuma bana shiga sabgar kowa tunda babu abinda na nema na rasa , ni ɗaya nake rayuwata idan kuma naje aji idan malami ya shigo zan samu natsuwa na tattara hankali na , rubutu ma ni nakeyin abuna da ɗaiɗaya nake ɗauko ko wane harafi , bana surutu a aji dan ba’a magana da hausa idan kuma mutum yayi za,aci shi tara ne ,

      Tun ranar da nazo ban sake zuwa wurin principal ba , kuma ta aiko a kirani banje ba , harkar gabana kawai nakeyi dan gaskiya naji ciwo da Dikko yasa aka ajiyeni JS 1 kuma naci ɗamara saina nuna mishi ni ba jahila ba ce ba ,

      Dikko kuwa tunda ya ajiye Sultana a makaranta yaci gaba huɗɗoɗin gabanshi , baiyi waya yaji ya Sultana ba kuma baizo makaranta ba da sunan ziyara , duk juma’a yana katsina yana komawa monday tunda safe yana ta zirga² a hanya saboda rashin lafiyar matarshi amma ko so ɗaya bai biyo wurin Sultana ba ,

      Haka dai rayuwa ta taci gaba da tafiya a makaranta , mutane suna ta shigowa rayuwata amma banda lokacin kowa ina so in tsula iskancina amma ba yanzu ba saina san abinda nakeyi , saboda ko magana nayi ma mutum sai kawai inji suna wani min turanci banza shi yasa na fita sabgar kowa nake tawa sabgar..

    Wallahi kwata² banajin daɗin zaman makarantar nan a daddafe dai muka fara jarabawa dan hutu za’ayi mana kuma har yanzu Dikko bai zo ba bai aiko ba , kuma kuɗin daya bani har yanzu akwai su kayan provision ina ma akwai sosai dan gaskiya ba ƙananan kuɗaɗe ya kashe ba dan dai kawai inyi farin ciki !

    Tunda naga hutu ya fara gabatowa nake neman “yan katsina dan in turasu gidanmu su faɗawa Babana ina FGC nasan zaizo idan muka dawo hutu , na samu “yan katsina amma duk wanda na faɗa masa anguwarmu sai yace bai sani ba dan abinda na lura duk “ya “yan masu kuɗi ne irin wanda basa zuwa yawo kamar yanda mu “ya “yan talakawa keyi…

     Dole na haƙura gashi ban riƙe number kowa ba dana riƙe tabbas dana samu aron waya na kira nace a faɗawa Babana yazo ya tafi dani , tou ban riƙe ba banda yanda zanyi inba haƙuri ba dan ban samu yanda nake so ba , duk ɗalibai suna farin cikin hutu kowa yana cike dajin daɗi zaije yaga iyayenshi saɓanin ni da bazan samu ganin Babana ba ,

       Anyi jarabawa an gama kuma an bada report ga ko wane ɗalibi nima an bani na saka a jakata na adana abuna , 

     Ranar hutu kowa yana cikin farin ciki ko wane ɗalibi ya samu “yanci kamar sakakken tsuntsu kowa na wali sakamakon ni da principal ta tsare a ofishinta , motoci kuwa sai ɗaukar dalibai sukeyi suna tafiya abin dai gwanin burgewa ina ta kallon ikon Allah har ɗalibai suka ƙare kaf dan principal tacemin tun satin hutu ta faɗawa Yayana za’ayi hutu , kuma jiya ta kirashi tace mishi yau ake hutu yace zaizo insha Allah ! Saida kowa ya watse babu sauran ɓishi²n ɗaliba ko ɗaya saini ina jiran zuwan shi ,

        Dikko baizo ɗaukata ba sai bayan azahar bayan ya iso ya kira principal ya sanar da ita zuwanshi , dan dama lokaci ² tana kiranshi ya kawo ina tana mishi sannu da hanya , tare muka fito da ita har wurin mota muna tare da ita , bayan mun isa  suka shiga gaisawa da Dikko tare dajanshi da fira dan kilbibi an fara magana da hausa sai a wani jefo turanci dan munafirci , gajiya nayi da tsayuwa na buɗe mota na shiga na zauna ,

      Yauma ya tunbiza mata kuɗi masu yawa , gaskiya Dikko yana da kyauta sosai zaiyi wuya ka ganshi bai baka ba , ya ganka yanzu ya baka anjima ma idan kuka sake haɗuwa saiya ƙara maka , godiya tayi sosai tare da mana addu’ar sauka lafiya ta wuce…,

      Saida Al ‘ Ameen ya fara tafiya Dikko ya juyo dukanshi yana kallona , bayan wani lokaci yace An mata kin rame me ya sameki ne ? Gyara baki na nayi tare da cewa ina yini , na gaishe shi dan kauda waccan maganar , murmushi yayi tare da cewa lafiya qalau , gaishe da Al ‘ Ameen nayi shima ya ansa , 

         Cike da tausayi Dikko yace kodai baki san wannan makarantar ne ? Dama saida nace bazan kawoki boarding ba kowa yace min wai in kaiki makarantar kwana , a raina nace wato saida kayi shawara kenan , kallon Al ‘ Ameen yayi tare da cewa ji yarinyar nan ta rame ni gaskiya banji daɗin haka ba wallahi ya ƙarasa maganar yana mai dawo da kallonshi wurina yace An mata ko bakicin abinci ? Murmushi nayi nace ina ci , to baki da kuɗi ? Nace ina da , to meke damunki ? Ko baki lafiya ne ? Yayi maganar tare da nunamin in matso kusa dashi ,

     Matsawa nayi kamar yanda yake so , ƙasa² yayi da murya yace meke damunki ne ? Ba komai nace , tsoki yayi tare cema Al ‘ Ameen ya tsaya zai dawo kusa dani , parking Al ‘ Ameen in yayi Dikko ya fito ya dawo baya kusa dani , ansar jakata yayi bayan ya rufe ƙofa yana cewa matso kusa dani , juyar da kaina nayi ina cewa nidai ka gyaleni a dai² lokacin da motar taci gaba da tafiya ,

Buɗe jakar yayi yana cewa ni wallahi naga duk kin koma “yar ƙarama Allah dai yasa ba masonyo min ke akayi ba , shiru nayi kamar banji ba , kalloni yayi da kallo maisa natsuwa , magana yayi cikin riƙe haruffa yace umm ya nunamin nayi shiru da kanshi , murmushi nayi shima murmushin yayi yace tou kice wani abu mana ,

     Sake maimaita maganar yayi , girgiza kai nayi cewa nice , yace ai banji kin fara kuka ba yau naji kinyi shiru , a daidai lokacin daya fara duba littafai na , haka yayi ta cirosu ɗaya baya ɗaya yana dubawa har yazo kan report ina , warwareshi yayi ya duba , gaba ɗaya annurin fuskarshi ya ɗauke ya ƙurawa report in ido , cikin muryar ɓacin rai yace tsaya , tsayawa Al ‘ Ameen yayi Dikko yace fita ki koma gaba ki zauna , da sauri na fita na koma gaba na zauna , ina ta mazurai kamar nayi wa sarki ƙarya duk yanda akayi a cikin waccan takarda yaga ɓacin rai…

      Shiru yayi tun daga nan ba saike magana ba har muka iso katsina , ko waya aka kirashi baya ɗauka , lokacin da muka iso har an fara sallah magrib , Al ‘ Ameen na tsayawa na fita da sauri zan wuce cike Dikko yace ke zo nan , da sauri na dawo shi kuma Al ‘ Ameen fita yayi ya ɗauki buta ya zagaya can bayan gida dan yayi alwallah ,

      Buɗe murfin motar yayi ya fiddo ƙafar ɗaya ɗayar kuma tana ciki , tsareni yayi da idanuwa dan haka na sauke kaina ƙasa shiru yayi na wasu mintuna sannan ya ɗago report in yace dan kin ɗaukeni sakarai ni zaki kawo ma wannan abun ? Shiru nayi banyi magana ba , tsawa ya daka min yace baki ji ina miki magana ne ? Cikin rawar murya nace yi haƙuri , fitowa yayi daga cikin motar da sauri nayi baya , shima takowa yayi ya matso kusa dani , da sauri na sake ja baya , ya sake biyoni , yana sake matsowa na ƙara ja baya , idan na sake matsowa kika matsa wallahi saina zaneki , tsayawa nayi jikina ya fara kyarma ina kallonshi , 

     Cike da ɓacin rai yace wannan iskanci zaki kawomin ? Girgiza kaina nayi ba tare da nayi magana ba , cikin tsawa yace shin kinyi rantsuwar magana ne ina miki magana kina girgizamin kai , da sauri nace a , a , jinjina kai yayi tare da tillomin report in yace ɗaukarshi ki shiga gani nan zuwa zaki faɗamin iskanci da kikeyi makaranta har kika ɗaukomin na 20 , na ƙarshe ke jakar da baki kishin kanki ya ƙarasa maganar tare da nannaɗe hannun rigarshi dan Al ‘ Ameen ya kawo mishi ruwa zaiyi alwallah…

       Duƙawa nayi na ɗauki report in zan shiga ciki yace kije ki fiddo min jakar banzarki daga mota , da sauri naje na ɗauko jakar na wuce ciki a lokacin shi kuma har ya gama alwalla ya biyo bayana yana ci gaba da faɗa ,

        Ɗakin da yake shiga ya wuce ni kuma na shige ɗakin da nake zama , yana nan kamar dai da babu wani ci gaba a cikin ɗakin , alwallah nayo nayi sallah ina roƙon Allah ya bani mafita Babana kaɗai nake ciwon san gani ,

      Har nayi sallah isha’e Dikko bai fito ba , su kuma uwayen ƙwa² har sun cika gidan sun fara gardamar kwallo , gajiya nayi na kwanta a inda nayi sallah gaskiya rashin ahali masu mutunci bai ba , duk wanda ya rasa iyaye masu daraja ya zama sai a hankali , ita kuma Inna ko wane irin ahalin suka raine ta ? Soyayya tana rufewa mata ido dasan duniya har su kasa gane aibun namiji , irin wannan rayuwar bata dace dani ba , da na fito daga zuri’a masu mutunci da duk haka bata faru dani ba ,

            Inayin rayuwa irin ta dabbobi kuma ni ba dabbar ba , mahaifi ya haifi zuri’a wai ya barsu da cida kansu wannan ba komai bane sai rashin tsoron Allah , caca neman mata shaye² shine wanda na samu a matsayin ubana , rayuwata tazo a garari zata ƙare a raɓe² , na ɓarar da mutuncin da yasa har wani namiji yake da damar shigowa rayuwata ya ɗaukoni daga cikin ahalina ya maidoni cikin rayuwarshi , wannan wace irin rayuwace na samu kaina a cikin ta… ?

        Dariyar Dikko na jiyo sai kyalkyatawa yakeyi duk yadda akayi waccan dariyar wallahi mugunta yaji , palon yayi shiru sai salati akeyi ƙasa² amma Dikko sai dariya yakeyi yana ƙarawa , maganar Al ‘ Ameen naji yana cewa mai gida tou ya za,ayi , miƙewa Dikkon yayi yana dariyar mugunta yayo ɗakin da nake kwance ,

     Cikin dariya yace ya miƙo hannunshi yana cewa An mata taso mu tafi , da sauri na taso kallona yayi yace wai duk me kikeyi baki cire kaya ba , ba tare dana kalleshi ba nace ba komai , tou zo mu tafi kina zuwa ? Ya tambayeni , girgiza kai nayi alamar a , a dan Dikko baida saiti abinda na fahimta idan dai yana cikin mugunta zaiso yayi ta zalinci yana dariyar cuta ,

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button