NOVELSUncategorized

KWARATA 40

???? —— 40
             Miƙewa yayi bayan ya gama surutanshi ya fita babban palo maƙulin motarshi ya ɗauka ya fita , ina tsaye a jikin window ina kallonshi har ya shiga mota ya bar gidan da gudu bansan inda zaije ba , kuma ga dukkan alamu bazai kwana gidan ba , murmushi nayi tare dayin magana ƙasa² nace sauka lafiya.


     Yana fita na dawo na kwanta saman katifa naja bargo na lulluɓe na rufe idanuwana ina jinjina irin wulaƙancin da Dikko yayi mana shi mai kuɗi , “yar madara dabbace amma duk lokacin da naji an kira sunan mage ko na ganta sai magena ta faɗon min a rai da Dikko yabi ta kanta da mota bataji bata gani ba ,


      Wulaƙancin da yayi ma Babana a ranar daya wankemin ubanda yafi ko wane uba a wurina da ruwan taɓo , lokacin daya bugamin kanshi har na suma , uwa uba ƙarshen wulaƙanci daya keta min mutuntaka ta , idan ma har zuciyata ta bari ƙiyayyar Dikko ta goge a cikinta ban yafewa kaina , ɗaukar fansa ƙudirina ne kuma muradi nane ko ba daɗe ko ba jima saina kafawa Dikko tarihin da bazai taɓa gogowa a rayuwarshi ba , 

     Maganar cewa idan na kawo mishi na 20 zai rufe ƙofa dani nayi masa rata har abada nayi masa nisan da bazai iya kamoni ba , yanda Annabi ya gagari arna haka na gagareka Dikko sa’a ɗaya kawai nake nema fita daga hannunka amma da zaran na zare tou kwankin hararka sun soma…

      Dukan sitiyarin mota Dikko yayi a daidai wannan lokacin yace wallahi ƙarya kike , dan tunda ya fito daga gidan zuciyarshi tana faɗa mishi Sultana tana sanshi tabbas kuma akwai wannan soyayya domin yaga soyayyashi kwance a cikin idanuwanta !

       Da safe tunda nayi sallah asuba nayi wanka na shirya cikin kayan makaranta , jakata na ɗauka da sauran kuɗina da ban kashe ba nayo babban palo ,

      Na daɗe dan nafi ƙarfin awa ɗaya amma babu Dikko babu alamarshi kuma babu mota ko ɗaya a gidan , tun ina zama na marmari har na fara gajiya na kwanta saidai na kalli agogo nayi tsoki dan gani ma nake lokutan basa sauri , raina fa ya gama ɓaci sosai dan har nayi tunanin kila bayau zan koma ba ,

     Ƙarfe 9:46am ya shigo gidan , a kasalance ya fito daga cikin motar ya nufo palo , kallo 3 nayi mishi kafin ya iso na kauda kaina , kamar yayi kuka dan yanayin fuskarshi ya nuna rai a haɗe kamar hadarin tsakar dare ,

      Da sallama ya shigo palon bai ko kalli inda nake ba ya wuce ciki , na ansa sallamar na gaishe shi bai ansa ba ya wuce , murmushi nayi a zuciyata nace kila matarshi taci ƙaniyarshi , mugu kenan sai lahira a gane halinshi…

      Yayi fata² da awowi biyu sannan ya fito tunda ya fito ƙaramin palon ƙamshin turarunshi ya fara zagaye cikin gidan nan lungu da saƙo bana tunanin akwai inda ƙamshin bai kai ba , ƙamshin turare mai daɗi mai jefa mutum cikin wani irin baƙon yanayi mai wahalar mantawa ,

      Bayan kamar minti biyu ya iso cikin babban palo , wallahi dole tasa na juya dan yanda naji ƙamshi inga wace shiga yayi haka ? Dan nasan bazaiyi wannan ƙamshin a banza ba , yanayin ƙamshin nasan yanayin haɗuwar da zaiyi kuma ba’a magana , dan duk yanda zan musulta muku kyawun Dikko zakuga kamar shiri ne abun , gaskiya Dikko yana da kyau fiye da duk yanda mutum yake zato , tunda nake a rayuwa ban taɓa ganin wayayyen namiji ɗan gayu mai saurin shiga rai kamar Dikko ba , ko ta ina babu inda mutum ya isa ya kushe shi saidai wani halin daban dan ɗan adam 9 yake bai cika 10 ba , Dikko yana da aji yana da natsuwar da ko mace tayi natsuwarshi taci Allah buɗa , 

     Baida yawan dariya haka kuma bai cika murmushi ba , idan kuma yaji mugunta ya fara dariya kai kanka sai abun ya burge ka domin dariya tana mishi kyau , haka kuma murmushi ke ƙara ƙawata kawunshi , kuma yanayin ɗaure fuska ma dai yana mishi kyau gaskiya !

      Idona na sauka kan idonshi gabana ya yanke ya faɗi , yasha ƙananan kaya abunshi yayi kyau cikar zatinsa da ƙwarjinsa ya ƙara fitowa sosai , bai kalleni ba ya yayi kamar ma bana nan saida yazo dai² inda nake zaune yace muje ,

     Ajiyar zuciya na sauke na ɗauka jakata nabi bayanshi dan shi tuni ya fice daga palon , lokacin dana fito harya shiga mota , ina buɗe murfin motar zan shiga baya zaune naga shine zauna , fuska a haɗe kamar an aiko mishi da sauƙon mutuwa , 

     Kawai dai naji babu daɗi yanayin yanda yake ta haɗe rai duk na kama kaina haka nan naji duk na takura , jakata na fara sakawa sannan na shiga na rufe na kalli wani gefe daban ba na driver ba kuma bana Dikko ba , yau an sako Al ‘ Ameen wani mai girman kan bala’e ne , kamar jira yake na rufe ƙofa ya bige mota kamar zai tashi sama ,

       Saida muka fara biyawa Alheri clinic acan matar Dikko take shi kaɗai ya fita yaje ya dubota bai wani daɗe ba ya dawo yana gaba wata kyakkyawar budurwa tana biyoshi baya har suka iso wurin mota ,

      Buɗe motar yayi ya ɗauki wayoyinshi daya bari lokacin da zaije wurin Sadiya , gaba ya koma ya zauna ita kuma ta shigo baya , kallona tayi ƙasa da sama sannan tayi tsoki tare da faɗin wata kalma da turanci amma ko miye tanayin maganar da zafi ne ,

      Ɗaga kaina nayi na kalli cikin madubi inda Dikko yake kallona , sam yau idonshi hankalin shi da tunaninshi baya wuri na , da gudu driver ya sauko daga inda aka tanada dan ajiye motoci ya ibi hanya yaci gaba da falfala gudu babu ji babu gani ,

       Saida mukayi tafiya sosai sannan ta sake faɗar irin kalmar data faɗa daga farko tana hararata , shiru nayi banyi magana ba , bayan wani lokaci tace au na manta ashe da daƙiƙiya nake magana jahila karuwar banza karuwar wofi , wani irin ɓacin rai na haɗeye dakel lumfashina ya fara yawo tsakanin duniya da lahira , taci gaba da cewa karya wacce iyayenki suka kasa baki tarbiya balbaɗaɗɗiya dake ɗiyar ɗan caca ,

       Murmushi nayi mai cin zuciya amma banyi magana ba dan na fahimci tana da sauran magana , ci gaba tayi da cewa ni sweetheart baya ɓoyemin komai ni nace yayimin rainonki zuwa ranar da za’a ɗaura mana aure zaki dawo gidana kuma gidan mijina da zama a nan zan fara baki azabar tausayin da yasa kika shigo rayuwata Sadiya ma da tamin hawan ƙawara ya kikaga lamarinta ya ƙare ? Zata tafi duniyar mutuwa babu jimawa ,

      Murmushi nayi tare da gyara zamana na kalleta sosai sannan nace idan kin isa ki sake maimaita abinda kika faɗa daga farko ! Nace jahila , nace ni ba jahila bace dan abinda na sani ko uwarki bata sanshi ba , ina da ilimin addini sittin ce a kaina sakara izihinki nawa ke ?  Tayi shiru nace tou kinga ɗan caca tun nan ya nuna tarbiyarshi tafi irin wacce babanki ya baki ,

     Da kika cemin karuwa tabbas ni karuwa ce bazaki shaida hakan ba saina kasa tallata a bakin titi uban naki idan ya gani zai kwasa , ni da kika gani kamar ɗan silif nake ko mutum baici ba saina burgeshi idan kuma harya taɓa kwanon zai taɓo cikin idan baici ba saiya lashe hannu , tabbas zan nuna miki kaidina da kuma illar kirana da karuwa da kikayi , 

     Matsalarki da Sadiya ba tawa bace amma tabbas sai ubanki ya taɓa nan da nan ya kuma maida miyanshi , na faɗi maganar tare da nuna mata wuraren da idonta ke iya gani sannan nace dake da Dikko duk nafi ƙarfinku kuma kinyi ganganci shigowa rayuwata abun harina ya koma biyu daga yanzun nan zanci gaba da hararki kuma in hari Dikko , mari takaimin , nima na rama daga nan muma cakume da kokowa daga zaune ,

      Da sauri Dikko ya juyo yace miye haka kuma ? Cikin ɓacin rai nace ban sani ba baƙin munafiki dakai , zaro ido yayi yace ai bake nake tambaya ba , cike da masifa nace nima ai bakai nake ba ansa ba , Ashiru yi parking inji Dikko , da sauri ya gurji gefen titi ƙayyyyy yayi parking har lokacin bamu daina bige² ba ,

      Ni Dikko ya fara fiddowa tunda ni nake saitin daya buɗe murfin motar yana fizgoni ya mareni yace nine munafikin An mata ? Kafin ya sauke hannunshi nima na zabgaga mishi mari nace kaine mana munafiki dama akwai wani bayan kai ?

       Da sauri Ashiru ya kauda kanshi , murmushi Dikko yayi yace An mata ni kika mara ? Nace waye kai ? Dikkon banza Dikko wofi , fitowa tayi daga cikin motar ta kamani da kokowa duk da banda ƙarfi na firgice sosai dan na tsani inji an aibata Babana , kokowa mukaci gaba dayi Dikko ya riƙeni na sake fizgewa mukaci gaba da faɗa , ya ƙara riƙeni sosai hannun damarshi ya riƙo min ƙuguna dashi hannun haggunshi kuma ya ɗagomin fuskata kowa yana kallon kwayar idon kowa ,
 K       Cikin maganarshi maisa natsuwa yace An mata yau kuma Dikkon ne na banza da wofi ? Ni An mata ? Kinmin adalci kenan ? A gaban mutanen dake ganin girmana zaki tozarni ? Mi yasa bakimin jiya ba ? Me yayi zafi haka haba An matana…. Ya ƙarasa maganar kamar zaiyi kuka , cikin kuka nace cewa fa tayi Babana ɗan caca kuma kaine kace mata ni karuwa ce kuma karya fa ???? jahila fa ????daƙiƙiya balbaɗaɗɗiya fa wai Babana bai bani tarbiya ba irin wannan shedar zakuyi ma Baba ?

       Tsareni yayi da idanuwanshi masu ɗaukar hankali sannan yace tou kiyi haƙuri , rufe idanuwana nayi nace inyi haƙuri a aibata min Babana ? Dikko ya ƙara cewa kiyi haƙuri , buɗe idanuwa na nayi tare da cewa wallahi Babana bai kasa bani tarbiyya ba kuma kai zaka sheda haka wata rana sakeni , sakina yayi baiyi kaddama ba mota na koma na ɗauko jakata nazo gabanshi na zazzageta nace ga jakar ka nan ga sauran kuɗinka nan idan naje gida zan bada cikonka a kawo maka ,

       Ina faɗin haka nayi gaba , Dikko yace ina zaki je ? Juyowa nayi cike da ɓacin rai nace zanje gidan ubanda ya hafeni ne , nasan darajar ɗan caca kuma nasan mutuncinshi , kallon inda budurwar take nayi nace sunana MARYAM ALIYU MUHAMMAD BINNA { Sultana } ki fara kuka tun daga yanzu domin kwanakin baƙin cikinki sun soma daga yau , mafita ɗaya kawai shine ki mutu ki huta amma tabbas bazan goge kuɗina akanki ba wallahi ×³ , zaki iya danna wannan hoton na kasa don samun kyaututuka.

1 2Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button