NOVELSUncategorized

KWARATA 49

???? —— 49

       Gaba ɗaya na firgice na fita hayyacina kururuwar da nakeyi ta karaɗe kaf girman hotel in , hayagagata ya jawo hankalin mutane akayo wurina ana lafiya ? Duk wanda na gani sai inga fuskar mutumin nan gareshi wayyo Allahna na shiga 3 ???????? na lalace shikenan mutuwa zanyi na bani ׳ na ƙarasa maganar tare da faɗuwa ƙasa ina burgima.


      Baiwar Allah lafiya ? Meke damunki ? Shine tambayar da mutanen da suka zagaye ni sukemin amma maimakon naji maganarsu sai naji muryar mutumin cikin muryar tsoratarwa da firgitarwa yana cemin da hantarki da ƙodarki ko zuciyarki wanne kika bamu….

      Da sauri na dafe cikina na tallabo saitin zuciyata amma har yanzu wayata na riƙe ram a hannuna , cikin kuka nace wallahi bazan bayar ba , nawa ne ni ɗaya , cikina ne da zuciyata hantana da ƙoda Allahna ya bani ba wani ba , kuma ubangiji bazai baku damar rabani da ko ɗaya ba , wata irin gigitacciyar dariya akayi tare da cewa kina nufin kinci kuɗinmu a banza ? Tou wannan kuɗin ki sani jinin wasu ne da wasu sassa na jikin ɗan adam dole ki bayar da naki kema domin a bawa dodo ya bamu kuɗi zuciyarki zata shiga kwarya , bankwana da duniya sai wata rana….

       Gaggaɓewa akaci gaba dayi da dariya data gigitani a karo na biyu , addu’o’e naci gaba dayi da ƙarfi idan ina addu’a bana gama wata saina saketa na kamo wata , dai najin sautin muryar dariyar nayi sai sautin kuka har zuwa wannan lokacin ban daina addu’a ba , bayan wani lokaci kuma na dainajin sautin kukan gaba ɗaya…

      Da sauri na miƙe ko jikina ban tsaya kakkaɓewa ba nayi gaba , mutane suka bini da kallo yayin da wasu ke tunanin ko ina da taɓin kwalwa ne , da gudu na fita daga hotel in , ina na fita na samu napep sai gidan Mamy amma har yanzu hankali na baya jikina gaba ɗaya a ruɗe nake , napep na tsayawa na fita da gudu nayi cikin gidan Mamy , bata nan sai yara na samu nace musu ina Mamarsu ? Sukacemin yanzun nan ta fita tace idan kinzo ki kirata ,

      Jikina yana ƙyarma na fara laluben wayar Mamy babu ɓata lokaci ta ɗauka , gaisawa mukayi nace mata kina ta ina haka ne ? Sunan hotel in dana baro ta faɗamin tare da cewa wani sabon sauna ne na samu ki jirani na wankoshi cikin mintuna kaɗan zan dawo , kaina ya juya a gigice nace karki je , ki dawo hotel in nan akwai wani gahurtaccen matsafi daya bayyana karki shiga ɗaki ki dawo , Mamy tace wane ɗaki ? Nace ɗakin dana shiga wallahi matsafi ne karki shiga ki dawo akwai zama na musamman , Mamy tace tou lamba nawa ne ɗakin ,

       Da sauri na dafe kaina duniyar ta riƙa juyamin kamar nahau shillo mai wanawa , gafa lambar ɗakin ina gani a idona bana iya faɗa dan na iya lissafin lambobi tunda dasu nake sarving numbobin mutane a cikin wayata , ganin na kasa faɗa kawai nace ….

      Ki dawo……….. Na faɗi ki dawo cikin wata irin murya hawaye suka gangaro daga cikin idona ina cewa nidai kawai ki dawo matan aure yake nema ko wane ɗaki bana so ki shiga ki dawo Auntyna bana san na rasa ki adaidai wannan lokacin ki dawo dan Allah na ƙarasa maganar ina durƙushewa ƙasa naci gaba da kuka , amma duk wannan maganar da nayi sam Mamy bata jini ta riƙa hello , hello idan kina jina kawai ki jirani , tana faɗin haka ta kashe wayarta ,

      Da gudu na fita daga cikin gidan , mai napep in daya kawoni shi nace ya maidani inda ya ɗaukoni dan dama ban sallameshi ba , nace kayi gudun bala’e ka kaimin motar nan maleji karka tsaya kuma karka kauce ina so kawai na buɗe idona na ganni a hotel in nan kamar kyaftawar ido ,

       Gudu mai napep yakeyi amma ce masa nake ya ƙara ina kiran wayar Mamy amma ba’a ɗauka , saidai na daki napep in nace wuta mai mota nace karka tsaya kaucewa ababen hawa muje kayi tuƙin nan kamar babu koma bisa titin nan saimu , gudu yake balbalawa na tashin hankali amma gani nake kamar baya tafiya , wayar Mamy kuwa saidai ta ƙari ringing inta ta tsinke amma ba’a ɗauka har muka isa hotel in ban daina kiran wayar Mamy ba kuma bata daina shiga ba haka kuma babu wanda ya ɗauka…

       A harabar hotel in naga dandazon mutane , da gudu na tunkari inda suke kamar wata mahaukaciya na riƙa ture mutane , hasahsena ya zama gaskiya domin Mamy ce yashe a ƙasa mutane sun zagayeta ga “yan sanda har sun rigani hallara a wurin , jini ne kawai ke ɗiga daga cikin idon Mamy kamar babu ƙwayar idonta dan baka gani hasken idon ko sai jini dake ɗiga ɗis ² , 

       A wurin mutane ke cewa yanzu wata ta fita itama tana ihu ita Allah yasa tana da sauran shan ruwa a gaba , goge hawaye nayi a zuciyata nace ba ni suke so ba matan aure , mutane sukaci gaba da cewe lallai akwai abinda yake faruwa , jiki a sanyaye na na isa gaban Mamy nace Aunty na ƙarasa maganar ina mai kamo hannuwanta , bata iya magana ma kwata² dan haka na rungumeta naci gaba da kuka ,  bayan “yan sanda sun gama bincikensu kuma basu samu wata sahihiyar sheda ba haka aka ɗauki Mamy da wayarta akayi asibiti da ita… Nima napep na koma nace masa mubi bayansu.

      Bayan mun isa asibiti “yan sanda suka danƙamu a hannun likitoci babu ɓata lokaci aka shiga duba Mamy , tashin farko dai likitocin sun tabbatar da babu idon Mamy kuma har yanzu jini bai gama fita ba , ni kuma hankalina yafi karkata akan wayarta dan haka naje wurin ɗan sanda nace ranka ya daɗe wayar zaka bani na kira Babanmu ,

     Kallona yayi sama da ƙasa sannan yace wace ce ke ? Nace ɗiyar mara lafiyarce ni , dan bana nan na dawo gida “yan uwana sukace Mama tace ta fita amma idan na dawo na kirata , bayan na dawo suka faɗamin na kirata mun fara magana da ita a waya daga baya kuma saita nunamin batajina , ka duba jerin kira kuma zaka gani dan daga baya nayi ta kiranta bata ɗauka ba ,

     Miƙomin wayar yayi domin wayar Mamy ba’a buɗeta sai an zana pattern yace buɗeta tou tunda kince ta Mamanki ce , lafiya lau na zana na buɗe wayar domin kullum a gabana take zanawa kuma baida wahala , bayan na buɗe ya duba yaga kiran da nayi mata kamar dai yadda nayi masa bayani , yana cikin dubawa kira ya shigo dan haka ya ɗauka , bayan gaisuwa naji yace muna genaral , yana faɗin haka ya kashe ya miƙomin wayar ,

     Babu wani daɗewa mijin Mamy ya iso asibitin , yasha kuka kamar ranshi zai fita duk iskancin da Mamy ke zubawa baya gani yana san matarshi , jikin gadon Mamy ya matsa cikin kuka yace Mamy Allah ya tsinemawa wanda yayi miki haka , Allah ya baki lafiya mata ta ubangiji yasa ki warke , 

      A wahalce Mamy tayi murmushi ta lalabo hannun mijinta tace kayi haƙuri mutuwa zanyi amma ina roƙonka daka yafemin , cikin kuka ya rungume Mamy yace Hajiya baza ki mutu ba wallahi baki mutuwa , Mamy tace naji amma kawai kace ka yafemin , cikin in’inna yace na , na na ya…. Ya fe miki , godiya tayi masa tare da cewa naji muryar Sultana tana ina ? Yace gata nan hajiya ya kamo hannuna ya haɗa da nata ,

    Umarni ta bashi cewa da Allah ya fita zatayi magana dani , cike da ladabi ya fice daga ɗakin , Sultana ta kira suna na , nace na’am tace dubamin babu kowa a kusa dani ? Babu Aunty na faɗa cikin girmamawa magana ta farayi bayan na tabbatar mata da babu kowa a wurin :•

      Sultana ta kira suna na , nace na’am Aunty , tace tou ki saurareni dakyau , nace inajinki Aunty , Mamy tace kinga whatsapp in nan da kike ganinta ? Wallahi ba ƙaramin haukata mata takeyi ba , shiru nayi ban sake magana ba naci gaba da sauraren Mamy .

      Aurena biyu a duniya , ina da shekara 39 akamin auren farko bayan nasha gwagwar mayar rayuwa , iyayena ba masu kuɗi bane suna dai da rufin asiri na ci da sha da sutura , mahaifina ba ɗan kasuwa bane kuma ba wani shahararen ɗan boko bane ba , yana aiki a ƙarƙashin kamfani wani attajiri , 

     Matan Babana biyu daga mahaifiyata sai abiyar zamanta , muna da yawa sosai mu “ya “yan babanmu , cikin hukuncin Allah matan gidanmu suna auren mazaje masu rufin asiri , duka matan gidanmu saida aka aurar dasu kaf har ƙanne na ni ban samu mijin aure ba ,

       Na tayar da hankalina sosai domin auren nake so ido rufe amma ban samu mai aurena ba , abin ya dameni sosai saina ma daina fita kwata ² kullum ina gida ko a familynmu daina shiga nayi domin na ganɗame sosai saina farajin kunyar shiga mutane ko baƙi akayi gidanmu sai in ɓoye ,

        Ina wannan ɓoye ²n ne Allah ya kawomin Bello a rayuwata , Bello abokin Yayana ne duk duniya baida aminin daya wuce Bello shima Bello baida aminin daya wuce Yayana , kowa yana san kowa kuma kowa baya ɓoyewa kowa sirrin junansu , sun yadda da juna fiye da tunaninki domin dai Bello zai iya tarawa da matar Yayana shima Yayana zai iya tarawa da matan Bello ,

      Tunda Allah yasa ya ƙyalla idonshi ya ganni ya liƙemin , nasan baƙin halin Bello sosai nasan illarshi kuma nasan miyagun halayyarshi dan haka koda ya furtamin kalmar so ban ansa ba nace bana sansa , shine ya faɗawa Yayana yana so na amma nace bana sansa , shine Yayan nawa yazo ya sameni yayi min kaca ² , nace ni bashi ne bana so ba halinshi ne bana so , kuma kaji tsoron Allah kai kanka baza ka iya bashi auren “yar uwarka da kuke ciki ɗaya , Yaya yace tou ko kinso ko kinƙi sai kin auri Bello idan baki aureshi don Allah ba zaki aureshi dan dole , saikin nemo Bello da kanki , yana faɗin haka yayi gaba abunshi ,

      Tun daga wannan ranar sukayi ta kusatsamin asiri na firgice na fita hayyaci na da kaina nake nemo Bello , idan na fita ban ganshi ba ko zankai gobe ban dawo gida ba saina ganshi hankalina zai kwanta ,

    A taƙaice dai Bello na aura aurena na farko , ranar da aka kawoni gidan Bello bayan mutane sun watse shima Bello ya shigo da abokanshi da suka rako ango ɗakin amarya kamar dai yadda akeyi ,

        Kowa fatan alkairi yaimin da addu’ar zaman lafiya , bayan an gama Bello ya bayyanar min da abokanshi kowa ya faɗamin sunanshi , saida yazo kan BINNA… ya dafashi cike da soyayya yace kinga wannan nace Eh yace Binna kenan Bello baya rayuwa saida Binna kamar yadda mutum bai rayuwa saida lumfashi , ina san Binna fiye da yadda nake san kowa a duniya , Binna nawa ne nima nashi ne , murmushi Binna yayi cike da izza amma baiyi magana ba , gaskiya Binna ya shiga zuciyata kuma duk duniya ban taɓa ganin wanda nake so a daidai wannan lokacin ba kamar Binna ,

    Sun ɗan daɗe dai suna fira amma har akayi firar aka tashi Binna bai saka baki ba har suka gama suka tafi , bayan Bello ya dawo daga rakiyar su yacemin na tsani Binna na nuna miki shi domin ki ganshi , hawaye ya cika a idon Bello yace tsinan Allah kawai ranar da zan zama ango Binna ya ɗauke budurci ya gudu , saboda kawai nayi ma yarinyar gidan da suka ɗaukoshi a bakin titi suna taimaka mishi , 

     Nayi alƙawari saina ƙafa babban tarihi a zuciyar Binna saina tagayyara mishi rayuwa saina zama silar rushewar kaf ahalinsa wanda suka gabata da wanda basu zo ba , saina jefa ƙiyayya mara gogewa tsakaninshi da “yan uwanshi da suke uba ɗaya , nayi alƙawari kuma babu gudu babu ja da baya ko duniya zatashi saina cika muradina ,

      Wani irin nishin wahala Mamy tayi har yanzu jinin bai daina ɗiga ba , a wahalce taci gaba da cewa….

     Bayan Bello ya gama alkaba’inshi ya hawo gado babu wata sallar godiya ga Allah babu wani abunda ya shigo min dashi irin wanda ango yake zuwa ma amarya dashi a daren farkonsu , haka ya hayeni yaita sassaƙa kamar mai faskare ya samu babban bedi , haka kuma babu wata addu’ar tarawa da iyali , 

    Sam banajin daɗin zaman aure da Bello dan na fahimta mugun atsabibi ne , babu sallah bare salati haka kuma bai yadda da ƙaddara ba komai dai malamin tsibbu , ina haƙuri dai ina zama amma sam bana sansa dauriya ce kawai , 

     Tun daga ranar da aka kawoni ina amarya ban sake ganin Binna ba saida yazo faɗama Bello an haifeki , 

     Duk ƙudirin da Bello yayi akan Sultana da burin mahaifinta akanshi ta faɗawa Sultana , tace wannan shine silar abinda ya rabani da Bello domin na nuna ban yadda ba ya aiwatar da ƙudirinshi akan Binna ba domin gaskiya ina sansa kuma bazan bari a cutar masa da rayuwa ba ,abun yayi ma Bello ciwo dan shine ya sakeni ,

      Bayan mun rabu nayi ² Binna ya aureni yaƙiya ina sansa kuma ina sha’awarshi dan haka nayi masa tayin kaina kuma Allah ya taimakeni ya ansa , da sauri na runtse idanuwana , Mamy bata gani na dan haka taci gaba da cewa kullum ni nake isko Binna ko ya nunamin baida buƙata sai nayi yadda za’ayi ya kwanta dani danni kaɗai nasan yadda nakeji idan ina kwance dashi ,

    Har na shekara 2 ina zawarci Binna fa ya kame akan bazai aureni ba , dole na haƙura na samu miji nayi aure , tunda nayi aure na daina zuwa wurin Binna , ina zaune da mijina lafiya babu abinda na nema na rasa , saidai zaman kaɗaici yana damuna , wannan dalili yasa na saya babbar waya na fara chating..

      Banda friends sosai a whatsapp dan haka dana duba naga wanda ke online saina dameshi da surutu , idan nayi magana sai mutum ya ɗauki tsawon lokaci bai bani ansa ba , na gaji dai nacema wata ƙawata wai sai inyi magana kuyi kamar baku gani ba , dariya tayi sannan tacemin haba hajiyata yaushe rabon duniya da ayyaraye , ni bana cht da mutum prvt ina can group inmu na mata masu duniya , wayayyin mata masu aji masu faɗa a gidan aurensu aji ina ƙaruwa ina zan tsaya saurarenki.

    Koda na tambayeta me ake koyawa a group in sai tacemin bara tayi adding ina gani ya kori ji ,  nace tou , bayan tayi adding ina ta gabatar dani tare da tura hotona , kowa dai yaimin fatan alkairi , a hankali dai nake rayuwa da “yan group in ina fuskantar su ,

       Basu da aiki sai turo style na ɗinki , idan sabuwar atamfa ta fito sai an turota , wasu takalman yayi masu zafi suma a turo jukkuna gyaluluwa “yan kunne tsarƙa , bawai na siyarwa bane ba , a , a sune dai na zamani su matan idan suka gani zasuje kasuwa su siya ,

       Mace kuwa idan tayi lafiyayen girki saita gama tsara abunta kaf a tebirin cin abinci sai ta ɗauko hoto ta turo a group , idan wanka kikayi kika kai ƙarshen adaka zakiyi hoto ki turo matan group in suna zugaki ,

     Shin da Allah mace ta dafa lafiyayyen abinci komai yaji banda bala’e kina kallon yadda naman kaji ke wali ga lemuna masu kyau da tsada an jera ki faɗamin ke kinyi ɗan wake da miyar ƙuli ko kinyi zazafen tuwo kin ɗauka ki tura ?

     Mace ta share ƙaton fili ga filawowi ta ɗauko hoto tasha kafirarriyar shadda ko wani ƙaton leshi ko super ke kuma mijinki baida halin ɗinka miki super atamfa rober yake da halin ɗinka miki kuma ita gareki shin kin ɗauka hoto ki tura a group in mata masu duniya ?

    Banda ko sisi amma ina da style na ɗinkuna a wayata yafi dubu , duk wata jikkar da ake yayi ko atamfa sabuwar fitowa tana cikin wayata , banda sisi mijina baya dashi na manta da hatta yatsun hannuna ba ɗaya suke ba , duk lokacin da wata ta ɗauko hoton palonta ta turo sai ince ya zanyi na maida nawa haka ? 

     Kafin wani lokaci na fara tadawa mijina hankali cewa duk mazan duniya suna kishin matansu suna musu sutura sun wadatasu da komai amma duk lokacin da nayi maka magana sai kacemin kai babu ,

      Idan yayimin nasiha ya bani haƙuri sai kuma in haƙura , kullum dai abu ci gaba yakeyi dan haka na fita daga group in , amma kash ina fita admin in ta biyoni prvt tacemin taga nayi left lafiya ? Ban ɓoye mata komai ba nace gaskiya ina ganin kayane hankalina yana tashi zuciyata tana min wasi² kuma mijina baida kuɗi shi yasa na fita , dan na lura idan aka turo kayan yayi duk wacce ta sawo idan ta ɗinka hoto takeyi ta turo kowa ya gani ,

Tacemin bara in kiraki nace tou , babu ɓata lokaci ta kirani bayan mun gaisa tacemin duk wanda na gani a group in nan matan aure ne , kuma yadda nake tunanin mijina ma baida hali yafi na wasu a cikin group in , kinsan yanzu ana zamanin rayuwar “yanci kina da aurenki amma kina da abokinki a waje , wanda zai ɗauke miki duk wata hidima taki ,

      “Yanci shine babban mutunci da zaran kin rasashi taki ta ƙare , cikin mintuna biyar kacal abokinki zaiyi ya miki abinda mijinki da kike aure bazai miki irinshi ba , yanzu an daina duhun kawai rayuwar ƙyaunci ta gushe , ki riƙe babbar waya kici mai kyau kisha mai kyau ki ɗaura mai kyau ki gyara muhallinki babu wanda yaji kuma babu wanda ya gani ,

     Nace tou idan kuma mijina yace ina na samu kuɗin da nake wannan hidimar fa ? Tace dama ai kafin ki shiga zaki rufe banza a tulun ƙasa zaki riƙa juya rayuwarshi kamar remote sai yadda kikace dashi babu shi babu magana kuma idan “yan uwanshi sukayi mishi magana tou fa ko uwarshi ce zai iya rabuwa da ita akanki , nace tou abokinki me ake bashi yake bada kuɗi haka kuma a ina zan samu abokin , tace abinda zaki bashi yana nan jikinki samun shi kuma nine zan haɗaki dashi , nace tou zanyi shawara ,

       Sati ɗaya ina neman mafita kuma kullum saita kirani ta ƙara bani shawara , ƙarshe dai na haƙura nima na antaya a duniyar kwaratanci , social media tana da amfani tana gyara amma illolin sunfi gyaratanta yawa kusan irin mutanen da kuke huɗɗa dasu , tari tayi sosai cikin yanayin wahaltuwa tace ki riƙe wayata a hannunki akwai wata ƙawata dana haɗa da Bello akwai wasu maganganu da nayi da ita akanki kuma na haɗasu domin ina so duk wani shiri nasa ya lalace ƙarshenshi tazo , naso na kafa rayuwa mai inganci a gareki amma lokaci ya ƙuremin , cikin kakari tace kuma Baban Hafsa da Baban Amisty da Binna …… Daga nan lumfashin Mamy ɗauke ,

      Shikenan Mamy tata , ta ƙare ina da tulin tambayoyi da zan mata amma ta tafi inda bazan sake ganinta har abadan duniya , me mutumin yayi mata ? Ya akayi aka ƙwaƙwale idonta ? Ina ƙawarta data haɗu da ita a sanadin whatsapp ? Ya akayi Babana bai aureta ba ? Cikin abokan Bello waye Yayan Mamy a ciki ? Ina iyayenta suke ? Wayyoni Allahna na shiga 3na , tou wai meye take san faɗamin data kira sunan Babana dasu iyayensu Amisty ? Wai ya rayuwata take tafiya a taltala ? Wani irin juyi kaina yayi na saki wani irin gahurtaccen ihu tare da faɗuwa ƙasa somammiya ,

     Ihun Sultana yasa mijin Mamy ya shigo da gudu , da taimakon likitoci aka samu aka farfaɗo da Sultana daga duniyar sumar data tafi , a lokacin dana farko har an fita da gawar Mamy waje an sakata a mota , 

KUYI KILIK ANAN

(function loadPageAds() { return afriPageAds({ ‘pid’: 8612, ‘uid’: 9740, ‘t’: ‘300 by 250’, ‘url’: ‘https://2gnblog.blogspot.com/’ }); }());


      Mijin Mamy ya bani wayoyi duka domin duk firar da mukayi da Mamy yaji komai , yace min kije gida sai Allah ya kaimu gobe za’ayi jana’izar Hajiya , mai napep in da kika zo dashi na sallameshi kije kar a nemeni ,

     Yana faɗin haka yayi gaba , kamar wata doluwa haka na riƙa tafiya irinta sakarkari har na fito waje , napep na samu na faɗa masa inda zai kaini , har na iso gida kuka nakeyi haka na sauka daga napep in nayi cikin gida abuna , shima Babana ya sallameshi ya tafi ,

        Wanka na farayi har na fito kuka nakeyi , zuwa wannan lokacin kuma labarin mutuwar Mamy ya fara zagawa a cikin gari , har su Amisty sunji labari kowa so yake yaji dalilin da yasa aka ƙwaƙwalewa Mamy idanuwa , bayan na fito wanka ina zaune a gefen katifa na kunno recording in da nayo bana gane komai amma fa ga murya nan lafiya zaw kanajin komai , aje wayar nayi na fita nayo alwalla ina dawowa na saka kayana ban shafa mai ba , hijabi na saka nayi sallah la’asar da ban samu yi ba ina gamawa na maida magrib bayan na sallame na ɗauki alkur’ani naci gaba da karantawa dan har yanzu bana cikin natsuwata ga tsoron da naji daga farko ga kuma mutuwar Mamy da aka zare ranta a gaban idona ….

          Tsaye yake gaban madubi yasha ƙananan kaya cikakken namiji kenan tsawonshi ma kanshi abun burgewa ne , sanye yake cikin farar riga da bakin wando rufaffen takalmi baƙi yasha stocking da bakin belt ƙamshin turare mai daɗi da dasa farinci mai jefa mutum yanayi marar gogewa a rayuwa sai tashi yake , murmushi yayi yayin daya fara sharce gemunshi yana cewa , sa’a da kanta take kwankwasa mana ƙofa ga duk nasarar namiji mace ce jigonshi , cingom yasaka a bakinshi saida ya ɗan tattauna yace gani nan zuwa gareki An matana……

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button